Me ya sa ake bayar da shawarar samar da dokar yin wa'azi a Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

Majalisar Ƙoli ta kan harkokin Shari'ar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin shugabanta mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ta nemi da a samar da dokokin da za su tantance masu wa'azi.

Wannan dai na zuwa kwanaki kaɗan al'ummar Musulmi su fara gudanar da azumin watan Ramadan.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu malamai ke amfani da mumbarinsu na wa'azi da kafofin sadarwa na zamani wajen yi wa junansu raddi, musamman akan wasu batutuwa da suka shafi addini.

Malamai da shugabannin addinin Musulunci a Najeriya, sun ce lokaci ya yi da za a samar da dokoki da suka shafi yadda ake gudanar da wa'azi a faɗin ƙasar.

Abin da NSCIA ke son a yi

Sakatare Janar na Jama'atu Nasrul Islam, Farfesa Khalid Aliyu ya shaida wa BBC cewa lokaci ya yi da dole ne a saka dokokin ƙayyade wa'azi da tafsiri a Najeriya.

"Ka da a mayar da munbarin tafsiri na habaici da zage-zage da ɓatanaci da ɗauko fannonin ilimi masu girma waɗanda ya kamata a karantar da su a zaure a gaban malamai sannan kowane malami ya yi bayani gwargwadon ilimin da Allah ya bashi.

Ƙoƙarin yadda za a rage damuwar kafafen sada zumunta wurin barazanar haɗin kai tsakanin malamai da masu wa'azi, inda jama'a ke kawai yin wa'azi saboda an kafa masa kamera." In ji Farfesa Khalid.

Shi ma Sakatare na Malam Nafi'u Baba-Ahmed "wajibi ne gwamnati ta fito ta yi dokokin da za su tsara yanayin da za a yi wa'azi da tafsiri domin muna ganin yadda wasu mutanen da ke kiran kansu da malamai na fitowa su yi maganganu akan jahilci da sunan wa'azi."

Mene ne ra'ayin malamai?

Da alama su kansu malaman da ake son yi wa wannan linzami na maraba da batun samar da dakokin wa'azin.

Sheikh Muhammad Bn Othman, malamin addinin Musulunci a birnin Kano, ya bayyana goyon bayansa dangane da samar da dokar.

"Indai kuwa aka ce akwai doka ta kyautata wa'azi musamman ma a watan Ramadan to wallahi muna maraba. In zai yiwu a kafa doka wajen tabbatar da cewa mai son yin tafsir yana san tafsir ɗin? Ya san Arabiyya?.

Saboda haka muna goyon bayan a yi wa Alƙur'ani gata. Ya kamata ka da mu mayar da mumbari wurin yin raddi. Muna kira ga mai alfarma Sarkin Musulmi da a tabbatar da wannan doka ka da ya zama an yi taro an fashe babu wani a ƙasa." In ji Sheikh Bn Othman.

Me tsarin mulkin Najeriya ya ce kan dokar wa'azi?

Domin jin tanadin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi dangane da dokar wa'azi, BBC ta tuntuɓi Barista Sulaiman Magashi, wani lauya mai zaman kansa a birnin Kano.

"Abu ne mai yiwuwa kuma mai fa'ida a ɗauki matakin tsara yadda ya kamata a gudanar da wa'azi domin shi ma fanni ne na wata sana'a wadda shari'ar addinin Musulunci da tsarin ƙasar suka amince a kyautata su."

Tsarin mulkin Najeriya ƙarƙashin sashe na huɗu na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da ƴancin gudanar da addinin da mutum yake so ciki kuma har da wa'azi wato kira ga addinin da yaɗa shi.

To sai dai kuma wannan ba yana nufin a yi wa'azin ta-ci-barkatai ba ko kuma yadda zai saɓa da tsarin zamantakewar jama'a kamar cin mutumcin wani ko kuma tayar da tarzoma. Saboda haka akwai buƙatar a yi dokokin kyautata wa'azi abu ne da ya dace a yanzu haka." In ji barista Sulaiman Magashi.

To sai dai barista Sulaiman Magashi ya ce akwai buƙatar shigar da waɗanda abun ya shafa cikin al'amarin.

"Ya kamata a lokacin yin dokokin da kuma zaratar da su a shigar da malaman da al'amarin ya shafa ciki domin samun cikakkiyar fa'idar aiwatar da tsarin ba tare da wata matsala ba." In barista Magashi, lauya mai zaman kansa a Kano.