Manyan sojojin Najeriya biyar da Boko Haram ta hallaka

..

Asalin hoton, BBC Collage

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Talata ne rahotonni suka fara ɓulla cewa mayaƙan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (Iswap) ta kashe Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kisan nasa ya tayar da muhawara game da yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap ke kashe manyan jami'an sojin Najeriya, duk da cewa ba shi ne na farko da ya mutu a filin daga ba.

Bayanai sun nuna cewa Janar Uba ne babban jami'i na biyu mafi girman muƙami da 'yanbindigar suka kashe tun shekarar 2021.

Iswap ta bayar da sanarwar kisansa a shafinta na Telegram, inda ta ce mayaƙanta sun kama shi ranar 15 ga watan Nuwamba bayan harin kwanton-ɓauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kusa da garin Wajiroko da ke jihar ta Borno.

Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe sojojinta biyu da dakarun sa-kai biyu. Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga iyalan Janar Uba da sauran dakaru.

Wannan maƙala ta duba manyan jami'an sojan Najeriya da aka kashe yayin yaƙi da Boko Haram tun daga 2018.

Birgediya Janar Uba

..

Asalin hoton, Presidency

Birgediya Janar M Uba shi ne kwamandan birged na 25 na rundunar sojin Najeriya.

Uba, ya zamo jami'in sojin Najeriya mafi girman muƙami da ƙungiyar ta kashe tun daga shekarar 2021.

Borno na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi, inda Boko Haram da sauran ƙungiyoyi ke iko da wasu yankuna.

A tsakiyar watan Janairu ma wasu mayaƙan Boko Haram ko na Iswap sun kai wa wasu manoma da masunta hari a garin Dumba na jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Akasarin mazauna ƙananan hukumomin Gudumbari, da Marte, da Abadam na zaune ne ƙarƙashin ikon 'yanbindigar kusan tsawon shekara shida.

Birgediya Janar Dzarma Zirkusu

Tun bayan fara yaƙin Boko Haram a 2009, Birgediya Janar Dzarma Zirkusu ne jami'in sojan Najeriya mafi girman muƙami da ya fara rasa ransa a 2021.

Janar ya mutu ne tare da wasu dakaru uku lokacin da shi ma mayaƙan Iswap, wadda ta ɓalle daga Boko Haram, suka yi musu kwanton ɓauna a garin Askira Uba a watan Nuwamban 2021.

Janar ɗin ɗan asalin jihar Adamawa ya zama kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade a garin Chibok a watan Janairun shekarar.

Sanarwar da rundunar sojan Najeriya ta fitar a lokacin ta ce ta yi nasarar kashe 'yanbindigar da dama da kuma ƙwace makamai masu yawa yayin da suka kare harin da aka kai musu.

Kanal Dahiru Chiroma Bako

..

Asalin hoton, Others

A watan Satmban 2020 ne kuma mayaƙan Boko Haram suka yi wa Kanal Dahiru Chiroma Bako kwanton ɓauna a wajen garin Wajiroko kuma ya rasu bayan raunukan da ya ji a harin.

Rahotonni sun ce an yi masa tiyata a asibitin 7 Division Military Hospital kafin rasuwarsa.

Shi ne kwamandan ƙaramar rundunar 25 Taskforce Operation Lafiya Dole a Damboa.

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya bayyana Kanal Bako a matsayin "jajirtaccen soja wanda ba a taɓa cin garin Damboa da yaƙi ba a ƙarƙashin jagorancinsa".

Kanal Muhammad Abu Ali

Kanal Muhammad Abu Ali

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto, Kanal Abu Ali kenan lokacin da ake ƙara masa girma

An kashe Kanal Muhammad Abu Ali a watan Nuwamban 2016 shekara ɗaya da ƙara masa girma daga manjo zuwa laftanal kanal.

Kanal Ali ya zarta ɗaruruwan sojoji abokan aikinsa ne sakamakon jajircewa da ya nuna a fagen yaƙi da Boko Haram yayin da yake jagorantar rundunar 272 Task Force mai kula da tankokin yaƙi.

Rundunarsa ce ta gwabza ɗaya daga cikin yaƙi mafi tsanani da Boko Haram a watan Fabrairun 2015, wanda ya kai ga ƙwato garin Baga daga hannun 'yan ƙungiyar.

Labarin rasuwarsa ya zama batun da ya fi kowanne jan hankalin ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya a lokacin.

Ya rasu ne lokacin da 'yanbindigar Boko Haram suka far wa Bataliyar 119 ta sojojin Najeriya Mallam Fatori da ke jihar Borno.

"Yana wajen tankarsa riƙe da rediyonsa. Amma saboda cikin duhu ne babu wanda ya ga 'yanta'addan da suka harbe shi," kamar yadda wani asibitin sojoji ya shaida wa jaridar TheCable a lokacin.

Kanal Ibrahim Sakaba

..

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Kanal Ibrahim Sakaba

Wani jajirtaccen sojan da Najeriya ta yi asara shi ne Laftanal Kanal Ibrahim Sakaba a watan Nuwamban 2018.

Kanal Sakaba ya mutu yayin harin da 'yanbindiga suka kai kan wani sansanin sojoji arewacin Borno, inda suka kashe gomman dakarun Najeriya.

Kafin rasuwarsa, shi ne shugaban ƙaramar rundunar 157 Task Force da ke Metele.

Wata sanara da rundunar sojan Najeriya ta fitar a watan Agustan 2021 ta musanta iƙirarin da matar sojan ta yi cewa 'yan'uwansa sojoji ne suka kashe shi saboda ya ƙi bayar da hadin kai a aikata cin hanci da rashawa.