Ko hamayya ta kama hanyar ƙarewa a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, Social Medai handles
Komawar gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, bayan ficewarsa daga PDP ya fara dasa ayar tambaya kan makomar hamayya a siyasar Najeriya.
Hamayya na ɗaya daga cikin ginshiƙan dimokraɗiyya, inda a lokuta da dama ƴan hamayyar kan riƙa sukar gwamnati kan wasu manufofin da ake ganin sun saɓa wa muradun ƴan ƙasa.
Shigar Gwamna Dauda jam'iyyar APC na zuwa ne mako guda bayan takwaransa na Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya koma jam'iyyar mai mulki.
A halin yanzu jam'iyyar APC mai mulki na da gwamnoni 31 cikin jihohin ƙasar 36.
Sauran gwamnonin hamayyar biyar da suka rage wa jam'iyyun hamayya biyu na PDP ne yayin da AP da AFGA da LP ke da ɗaiɗai.
Daga cikin jihohin arewacin Najeriya 19 jihar Bauchi ce kawai, wadda ba APC ke mulkinta ba.
Kuma tuni jam'iyyar ta samu gagarumin rinjaye a majalisun dokokin ƙasar biyu.
Wannane ya sa wasu ƴan ƙasar suka fara tunanin hamayya ta kama hanyar ƙarewa a shiyasar Najeriya.
Mene ne amfanin hamayya a siyasa?
Dr. Ibrahim Baba Shatambaya malami a tsangayar nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya hamayya babban ginshiƙi ne a harkokin dimokraɗiyya.
''Ka iya cewa hamayya ita ce gishirin dimokraɗiyya, domin shi ne babban abin da ya bambanta tsarin dimokraɗiyya da sauran tsare-tsaren mulki'', in ji shi.
Masanin kimiyyar siyasar ya ce muhimmancin hamayya a tsarion dimokraɗiyya ba zai misaltu ba.
''Domin shi ke bai wa jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen huka damar bibiyar ayyukan gwamnati da nufin kare muradun ƙasa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ce tsari ne da ya bayar da damar bin diddigin gwamnati domin ganin cewa ba ta yi zalunci ko bijiro da wasu al'umaura da za su cutar da ƴan ƙasa ba.
Me ya sa ƴansiyasa ke komawa APC

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mafi yawan gwamnonin da suka koma APC kan bayar da dalilai na rikicin jam'iyyunsu, musamman na PDP.
PDP ta faɗa rikici tun bayana zaɓen 2023, matsalar da ta ƙi ƙarewa tsawon shekara uku.
Sai Dr. Shamtambaya ya ce akwai dalilai da dama da ke sanya wasu ƴansiyasa ciki har da gwamnoni ke komawa jam'iyyar APC mai mulki.
''Na farko shi ne tarin rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyun wanda hakan na barazana ga makomar ƴansiyasar, musamman kan batun takara'', in ji shi.
Ya ce saboda rikice-rikicen da suka dabaibaye jam'iyyun ƴansisar na fargabar asarar takararsu a tsoffin jam'iyyun nasu, saboda jam'iyyun nasu sun fara rasa martabarsu a idanun al'umma.
Malamin jami'ar ya ce wani dalilin kuma shi ne zargin da ake yi cewa jam'iyya mai mulki na yi musu tayin takara kai-tsaye, musamman gwamnoni idan suka koma cikinta.
''Haka kuma akwai batun fifita kai, maimakon mafitar jam'iyyar gaba ɗaya, galibi waɗanda suke komawa APC za ka tarar buƙatunsu ne a gaba, maimakon fifita muradun jam'iyyarsu'', in ji shi.
Sannan kuma Dr Shatambaya ya ce wani dalilin shi ne samun manyan ayyuka da talklafin gwamnatin tarayya a jihohinsu.
''Galibi wasu kan koma jam'iyyar ne domin samo wa jihohinsu manyan ayyukan gwamnatin tarayya da samun manyan muƙamai a gwamnatin tarayya'', in ji shi.
Ina makomar hamayya a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Wasu ƴan ƙasar da dama na nuna fargabarsu game da makomar hamayya a ƙasar, idan aka tafi a wannan yanayi.
Sai dai Dr. Shatambaya ya ce baya tunanin hakan ƙarewar adawa a Najeriya.
''Ai ba yanzu muka saba ganin haka a siyasar Najeriya ba, a baya an taɓa yin lkokacin da PPD ta yi irin wannan ganiyar, take da mafi rinjayen gwamnoni take da rinjaye a majalisun dokokin ƙasar, amma adawar ba ta ƙare ba'', in ji shi.
Ya ce ba a taɓa siyasa babu hamayya ba.
Malamin jami'ar ya ce Hausawa na cewa idan ganga ta fiya zaki fashewa za ta yi.
''Don haka sannu a hankali ita ma APC abin da ya samu PDP zai zo mata, in ba ta yi a hankali ba, domin kuwa akwai matsalolin da za su kunno kai cikinta, wanda maganinsu sai Allah''.
''Idan aka zo batun takara, wasu suka samu, wasu suka rasa, daga nan matsala za ta fara ɓullowa a jam'iyyar', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce ba zai matuƙar wuya a ce duka ƴan siyasar Najeriya su koma jam'iyyar hamayya.
Ko ADC ka iya maye gurbin PDP a hammaya?
Tun bayan da wasu manyan ƴansiyasar ƙasar suka sanar da ƙulla ƙawance a jam'iyyar ADC domin ƙalubalnatar jam'iyyar APC a 2027, jam'iyyar ke ci gaba da samun tagomashi.
Ko a makon da ya gabata ma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya yanki katin jam'iyyar, lamarin da ke alamta shigarsa ADC a hukumance.
Amma Dr Shatambaya ya ce abin da kamar wuya, domin a cewarsa ita kanta ADC cike take da waɗanda ya kira ƴankasuwar buƙata da kuma ''barazanar APC'', kamar yadda ya bayyana.
''Ita kanta jam'iyyar ADC an ƙi barin mambobinta su zauna lafiya, tun bayan sanar da ita a matsayin jam'iyyar da ƴan hamayya za su yi hamayya, aka riƙa farautar mambobinsu ta hanyar zarginsu da aikaya laifuka da kama su da kuma tsare su'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa jam'iyyar ADC cike da take da manyan ƴansiyasa masu muradin tsayawa takarar shugaban ƙasa.
''Duk mutanen da suka baro jam'iyyunsu, suka shigo ADC, sun shiga ne da buri ɗaya, wato tsayawa takarar shugaban ƙasa, kuma dai ka san takarar nan mutum ɗaya ne zai samu'', in ji shi.
Don haka ne ya ce matsawar ADC ba ta iya magance wannan ba tun yanzu, to da wahala ta iya riƙe kambin babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar.












