Da gaske ne an cire Igbo daga littafin tarihin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Chiamaka Enendu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
- Lokacin karatu: Minti 6
Dawo da koyar da darasin tarihi a tsarin koyarwar Najeriya, bayan shafe shekaru 16 ba a koyar da shi ya janyo cece kuce daga masu amfani da kafafen sada zumunta bayan zargin cewa an cire ɗaya daga cikin manyan ƙabilun ƙasar daga littafin koyar da tarihin.
A watan da ya gabata, Umelo Victor wanda ke sharhi kan harkoki siyasa da zamantakewa a kafafen sada zumunta ya wallafa wani bidiyo, inda a ciki ya ke sukar wani littafin da ya ce ɗansa na amfani da shi a makaranta mai suna Living History littafi na 1. Ya yi zargin cewa ba a sanya ƙabilar Igbo a cikin littafin ba kuma hakan zai iya janyo barazanar shafe ƙabilar Igbo daga tarihin Najeriya.
Mutane fiye da 300,000 suka kalli bidiyon kuma wasu fiye da 2,000 suka yaɗa shi a shafukansu. Bidiyon ya kuma ɗauki hankali a TikTok. Vivian Ifeoma , wadda ta yi ice wajen wallafa bidiyon al'ummar Igbo da al'adunsu tana cikin waɗanda suka yi sharhi kan batun. Bidiyon ta ya ja hankali dubban mutane, inda aka riƙa tafka muhawara game da zargin rashin sanya harshen Igbo a cikin littafin.
Mr Victor ya shaidawa BBC cewa yana ƙorafi ne a kan littafin da ke hannun ɗansa. Amma littafi na biyu an sanya ƙabliar Igbo a ciki kuma BBC ta gano cewa a haka aka fitar da jaddawalin koyarwa na Najeria.
Kamfanin da ya wallafa littafin ya ce duk abin da ya wallafa abubuwa ne da ke cikin tsarin koyarwa na ƙasa.
Mr Victor ya jajirce kan matsayarsa, amma ya ce har yanzu bai kai ga ganin sauran littafan da aka wallafa bayan wanda ya gani ba.
Al'amarin da ya fara a matsayin ƙorafi daga mutum ɗaya, ya rikiɗe zuwa babban zance a game da wakilcin ƙabilun Najeriya a ajin karatu, da matakan amincewa da littafan da ake amfani da su wajen koyarwa a ƙasar da kuma sarƙaƙƙiyar da ke cikin tsarin koyar da darasin tarihi a makarantu.

Mene ne a cikin wannan littafi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A hukumance, Najeriya ta amince da harsuna ko ƙabilu uku: Hausa da Yaruba da kuma Igbo. Kuma baki ɗaya ƙabilun uku idan aka tara yawan jama'ar su ya kai kashi 70cikin 100 na jama'ar ƙasar. Akwai kuma wasu ƙarin ɗaruruwan ƙabilu a Najeriya bayan waɗannan uku.
Masu suka sun yi amanna cewa littafin bai kunshi tarihin ƙabilar Igbo ba.
Amma kamfanin Accessible Publishers wanda ya wallaa littafin ya kare aikin nasa yana mai cewa a litattafi na farko an yi bayanin tarihin Najeriya ne kafin samuwar ƙabilar Igbo, kuma a littafi na biyu an bayar labarin ƙabilar Igbo, da yadda ta haɓɓaka da kuma al'adun ta.
Ya ƙara da cewa a shirye yake ya yi aikin haɗin gwiwa da maruta daga al'ummar Igbo domin ƙara inganta littafan.
Mafi yawan tattaunawar da aka yi game da litafin a kafafen sada zumunta ta mayar da hankali ne a kan littafi na farko wanda taƙaitaccen bayanin gabatarwar da aka yi masa ke nuna cewa littafi ne da zai share fage ga ɗalubai domin sanin muhimmancin haɗin kai a Najeriya.
BBC ta sayi littafin na farko da na biyu da kuma na uku.
Yayin da littafi na farko ya lissafa Igbo a cikin manyan ƙabilun Najeriya a shafi na 15, akwai kuma shafuka aƙalla uku zuwa tara da aka ware ana bayani kan kowanne daga sauran ƙabilun, inda aka zayyana mafarin su da ala'adunsu da salon mulkinsu da kuma harkokin tattalin arzikin da suka gada.

Asalin hoton, Getty Images
Amma a ɓangare guda, an yi bayanin ƙabilar Igbo ne a ƙarƙashin sashin da aka yi bayani kan lokacin baya kafin samuwar tarihin Najeriya kuma a cikin wannan sashi an bayanin ƙabilar ne a cikin tarihin al'adun Nok da Ife da Benin da kuma Igbo Ukwu.
Cibiyar nazari kan ilimi a Najeriya NERDC ta tsara cewa a koyar da littafi na farko ga ɗaluban matakin sakandare aji ɗaya watau JSS1, kuma a mayar da hankali wajen sanar da ɗaluban ma'anar tarihi da hanyoyin samun bayanai kan tarihi da mahumman wuraren tarihin al'ummar Najeriya kafin zuwan turawan mulkin mallaka da kuma manyan al'ummomin wancan lokacin kamar masarautun Hausa-Fulani da masarautar Oyo da ta Benin da dai sauran su.
A littafi na biyu kuma na ƴan ajin JSS2, an fadada tarihin zuwa al'ummomin da basu da masarautu a farko tarihin yammacin Afirika da suka haɗa da ƙabilar Igbo da Idma da iv da dai sauran su.
A wannan littafi an yi bayani sosai a kan ƙabilar Igbo, daga mafari zuwa al'adu da tsarin siyasa da tattalin arziki da kuma salon mulkinsu.
Ƙila saboda da haka ne aka fi samun bayani kan ƙabilar Igbo a cikin littafi na biyu.
Farfesan tarihi a jami'ar Ibadan, Olutayo Adesina ya ce bai yi mamaki ba kan zargin rashin bayani game da ƙabilar Igbo da aka tayar.
"A ƙasar da jama'a ke zaune da juna cikin zargi da rashin yarda, mutane na saurin ɗaukar duk nau'in rashin daidaito a matsayin abin da aka tsara yi da gangan,'' In ji Farfesa Adesina.
Ya ƙara da cewa babban abin tambaya a nan shi ne "ko an bai wa kowacce ƙabila dama yadda ya kamata cikin adalci,"
Frank Omoba, wani malamin tarihi a makarantar sakandare a Abuja ya ce yana kyautata zaton akwai dalilin da ya sa aka tsara littafan a yadda suke.
Ya ce "Tsarin ƙabila mai masarauta da jagororinta fitattu ya fi sauƙin a koyar da ɗalubai masu ƙarancin shekaru kuma su fahimta cikin gaggawa,''
Ya ƙara da cewa lokacin da ɗaluban suka shiga aji na biyu a ƙaramnar sakandare, za su iya koyon tarihi da al'adun sauran ƙabilu masu wahalar fahimta.
Wa ke karanta littafin?
Ma'aikatar ilimi ta tarayya a Najeriya ta ce ba a kai ga amincewa da littafin domin koyar da shi a makarantu ba, kuma ba a miƙa shi ga cibiyar bincike kan ilimi ba domin nazari. Amma ta yaya aka samu ana koyar da shi a makarantu kamar yadda masu amfanoi da kafafen sada zumunta suka yi zargi?
Mr Victor ya shaidawa BBC cewa ana koyar da ɗansa littafin ne a wata makaranta mai zaman kanta da ke garin Fatakwal, kuma ɗan nasa yana a ajin ƙaramar sakandare na ɗaya ne.
Ya jajirce cewa dole liytattafin ya samu amincewa shiyasa ake amfani da shi a makarantar.
Makarantar da Mr Victor ya yi bayani ta tabbatarwa BBC cewa littafin na cikin tsarinta na koiyarwa.
Makarantar ta ce ma'aikatar ilimi na tura mata jerin littafan da za ta yi amfani da su wajen koyarwa, amma ita kuma tana ƙarawa da nata waɗanda babu su a jerin da aka aike mata, kuma kafin yin hakan tana nazari sosai kan littafan da ya dace ta yi amfani da su.
Ta ƙara da cewa kawo yanzu ba ta samu wani ƙorafi daga iyaye ba, game da rashin gamsuwa da amfani da take yi da wannan littafi.
A Najeriya ma'aikatar ilimi ce ke tantance littafan da za a yi amfani da su wajen koyarwa a makarantu sannan ta tura makarantun domin fara aiki da su. t what qualifies as an "approved" textbook.
Adekunle, wani mai sayar da littafai Yaba da ke jihar agos a ce daga shekarar 2025 zua yanzu ya sayar da wannan littafi fiye da 6000, ga ɗaiɗaikun jama'a da kuma makarantun da ba na gwamnati ba.

Asalin hoton, Getty Images
Tarihin darasin tarihi
An canza jaddawalin tsarin koyarwa a Najeriya sau da yawa, tun bayan samun ƴancin kai.
A ƙarƙashin tsarin da aka ɓullo da shi a farkon 1980, an cire darasin tarihi daga ƙaramar sakandare kuma aka maye gurbin shi da social studies. Amma an ci gaba da koyar da tarihi a matakin babbar sakandare.
A 2009 aka cire darasin tarihi a tsarin koyarwa a matakin firamare da kuma sakandare, inda aka cusa shi a cikin social studies.
Wannan mataki ya sha suka sosai a lokacin.
An kuma yi maraba da matakin dawo da koyar da darasin tarihi a firamaare da kuma ƙaramar sakandare.












