Arsenal da Man U da Chelsea na rububin Manzambi, Barca ta fara fitar da rai da Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na sha'awar siyan dan wasan tsakiya na Jamus Julian Brandt, mai shekaru 29, lokacin da kwantiraginsa na Borussia Dortmund zai kare a wannan bazarar. (Metro)
Manchester United, da Arsenal da Chelsea duk suna sha'awar dan wasan tsakiya na Freiburg mai shekaru 20 Johan Manzambi na Switzerland. (Teamtalk)
Ko da yake Arsenal ta janye sha'awarta ga dan wasan tsakiya na Italiya mai shekaru 25 na Newcastle Sandro Tonali. (Chronicle)
Da wuya Tonali ya koma Seria A, bayan da Newcastle ta sanya farashinsa a kan fam miliyan 77 (Yuro 90) ga dan wasan, idan har Juventus tana son daukarsa, amma har yanzu Manchester United da Manchester City ma mima sja'awarsu. (Matteo Moretto)
Juventus ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva game da komawa kungiyar idan kwantiragin dan wasan mai shekaru 31 ya kare, amma tana fuskantar gasa daga kungiyoyi ciki har da Galatasaray da Inter Miami. (Gazzetta dello Sport)
Brighton tana da kwarin gwiwar doke Chelsea wajen sayen dan wasan gefe na Cologne Said el Mala, mai shekaru 19 a lokacin bazara, wanda ya ja hankalin kungiyoyi a Bundesliga. (Football Insider)
Chelsea ba ta son sayar da dan wasan gaba Liam Delap a wannan bazarar duk da cewa dan wasan na Ingila shekaru 23 ya zura kwallo daya kacal a gasar Premier a kakar wasan nan sakamakon daurin da ya samu. (Mirror)
Liverpool ta ci gaba da neman dan wasan baya a wannan bazarar kuma dan wasan Jamus na Eintracht Frankfurt Nnamdi Collins ne ake sa ran zai koma, inda Arsenal ma ke sa ido kan dan wasan mai shekaru 22. (Mirror)
Barcelona na neman madadin Marcus Rashford idan ba za su iya cimma yarjejeniya ba don sayan dan wasan gaban Ingilam mai shekaru 28 daga Manchester United ya zama na dindindin ba. (Marca)
Crystal Palace ce ke kan gaba wajen neman dan wasan gefe na Millwall Femi Azeez (Teamtalk)
Tottenham, Crystal Palace da Manchester United duk suna sha'awar kocin Bournemouth Andoni Iraola. Kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa. (i paper)












