Liverpool na son Diaby, Pochettino zai koma Real Madrid

Moussa Diaby,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Moussa Diaby,
Lokacin karatu: Minti 2

Juventus tana sha'awar sayen dan wasan baya na Tottenham da Ingila Djed Spence, mai shekaru 25, a lokacin bazara. (Gazzetta dello Sport)

Liverpool na tunanin sayen dan wasan gefe na Al-Ittihad da Faransa Moussa Diaby, mai shekaru 26, yayin da ake sa ran tsohon dan wasan na Aston Villa zai bar kungiyarsa ta Saudi Pro League a wannan bazarar. (Teamtalk)

Real Madrid na tunanin daukar tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino don maye gurbin Alvaro Arbeloa a Bernabeu a kakar wasa mai zuwa. (ESPN)

Manchester United ba za ta yi gaggawar nada kocin dindindin ba duk da kocin rikon kwarya Michael Carrick na ci gaba da nuna bajinta. (The Athletic)

Dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister, mai shekaru 27, ba ya shirin tattaunawa da Liverpool kan sabuwar yarjejeniya a wannan bazarar (Mundo Deportivo)

Napoli na son tsawaita kwantaragin ɗan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay har zuwa 2030 a ƙoƙarin hana duk wata kungiya daukar dan wasan mai shekaru 29. (Il Mattino)

Da wuya Manchester City ta amince da wata yarjejeniya wadda za ta sa ɗan wasan tsakiya na Amurka mai hazaka mai shekaru 16 Cavan Sullivan ya koma ƙungiyar MLS ta Philadelphia Union a kakar wasa mai zuwa. (The I)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Tottenham Ryan Mason ne ake sa ran zai maye gurbin Igor Tudor a matsayin kocin riƙon ƙwarya a Spurs. (Football Insider)