'Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 600 a Lebanon'

Asalin hoton, STR/EPA-EFE/REX/Shutterstock
Isra'ila ta ce ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Iran da Lebanon. Ta ce an kai hare-haren ne kan ababen more rayuwa a fadin Iran, da kuma wuraren da kungiyar Hizbullah ta ke a Beirut babban birnin Lebanon.
Wakiliyar BBC ta ce rundunar sojin Isra'ila ta ce wasu hare-harenta na baya-bayan nan, ta kai su ne kan dakarun Iran da ke shirin harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa, zuwa yanzu sun kashe kusan mutum dari shida tun bayan fara yakin.
Cikin daren jiya Talata, sojojin Amurka sun ce sun lalata wasu jiragen ruwan Iran goma sha shida da ke sanya nakiyoyin karkashin ruwa a mashigar Hormuz, bayan da shugaba Trump ya gargadi Tehran kan sanya nakiyoyin.














