Ƴan Najeriya 4 da suka shiga jerin attajiran Afirka na 2026

Asalin hoton, Others
Ƴan Najeriya huɗu sun samu shiga jerin attajiran Afirka 23 na 2026, kamar yadda mujallar Forbes mai nazarin alƙaluman tattalin arziki ta bayyana.
Cikin rahotonta na shekara-shekara mujallar ta ce arzikin attajiran nahiyar Afirka ya yi matuƙar bunƙasa da kashi 21cikin 100 idan aka kwatanta da 2025, inda a yanzu jerin hamshaƙan attajiran nahiyar ke juya jarin dala biliyan 126.7 tsakaninsu.
Ƙasar Afirka ta Kudu ce kan gaba a yawan attajiran da suka shiga jerin, inda take da guda bakwai, yayin da Masar ke biye mata da attajirai biyar a jerin, daga nan sai Najeriya mai huɗu, amma ƴanƙasarta ne gaba-gaba a jerin.
Mujallar ta ce jarin attajiran nahiyar ya yi matuƙar haɓaka, musamman daga bunƙasar kasuwanni da farfaɗowar darajar kuɗi a wasu ƙasashen nahiyar, lamarin da ya haifar musu da riba mai matuƙar gwaɓi.
A cikin wannan maƙala mun duba ƴan Najeriya huɗu da suka shiga cikin jerin.
Aliko Dangote $28.5bn

Asalin hoton, AFP
Shugaban rukunin kamfanonin Dangoten ya ci gaba da riƙe matsayinsa na mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka.
Mujallar ta ce Dangote na da yawan jarin da ya kai dala biliyan 28.5.
A cewar mujallar ta Forbes a shekara mai ƙarewa arzikin attajirin - ɗan asalin jihar Kano da ke arewacin Najeriya - ya ƙaru da kusan dala biliyan 4.6.
Forbes ta alaƙanta ƙaruwar arzikin attajirin da bunƙasar hannayen jarin kamfaninsa na sumunti wanda ya ƙaru matuƙa.
Rahoton na Mujallar Forbes ya ce kamfanin simintin na Dangote ya ninka ribarsa a 2025, inda ya samu ribar naira tiriliyan ɗaya.
Mamallakin katafariyar matatar man fetur mafi girma a Afirkan a baya-bayan nan ya ƙulla yarjejeniyar dala miliyan 400 da wani kamfanin China domin ƙara yawan da matatar ke tacewa nan da 2029.
Abdulsamad Isyaka Rabiu $11.2bn

Asalin hoton, BUA group
Mujallar Forbes ta ce shugaban rukunin kamfanonin na BUA ne ya fi kowane attajiri samun riba mafi yawa a Afirka.
A cewar Forbes ƙididdigar jarin attajirin ta ƙaru da kashi 120 cikin 100.
A yanzu ƙarfin jarin attajirin, wanda shi ma ɗan Kano ne a arewacin Najeriyar ya kai dala biliyan 11.2, daga dala biliyan 6.2 da yake a shekarar da ta gabata.
A yanzu Abdulsamad Isyaka Rabiu ne mutum na uku mafi arziki a nahiyar Afirka, daga matsayi na 6 da yake kai a shekarar da ta gabata.
Mujallar Forbes ta ce kamfanin sumunti na BUA ne kan gaba cikin abubuwan da suka ƙara wa attajirin riba da ƙarfin jari.
Mike Adenuga – $6.5bn

Asalin hoton, others
Shugaban rukunin kamfanonin sadarwa na Globacom, Mike Adenuga ne mutum na uku cikin attajiran Najeriya da suka shiga jerin attajiran na Afirka.
Mujallar Forbes ta ce a yanzu attajirin shi ne mutum na shida cikin jerin attajiran Afirka, wanda ƙarfin jarinsa ya kai dala biliyan 6.5.
Mista Adenuga shi ne shugaban kamfanin mai na Conoil, wanda ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa fannonin sadarwa da harkokin bankuna da cinikayyar mai da iskar gas.
Mike Adenuga ɗan asalin jihar Ogun ne da ke yankin kusu maso yammacin Najeriya.
Femi Otedola – $1.3bn

Asalin hoton, Others
Ɗan Najeriya cikin na huɗun da ya samu shiga jerin attajiran Afirka shi ne Femi Otedola.
Shugaban kamfanin samar da makamashi na Geregu Power Plc, shi ne mutum na 22 cikin jerin attajiran nahiyar Afirka 23 da mujallar Forbes ta wallafa.
A cewar mujallar ƙarfin jarin attajirin ya kai dala biliyan 1.3, kodayake mujallar ta ce attajirin ya yi asarar dala miliyan 200 saboda sayar da mafi yawan hannayen jarin kamfaninsa na samar da makamashi.
Femi Otedola ɗan asalin jihar Legas ne da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.










