Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon kocin Super Eagles Onigbinde

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa iyalai da abokan hulɗar fitaccen jami’in harkar ƙwallon ƙafa kuma tsohon kocin tawagar ƙwallon kafar Najeriya, Adegboye Onigbinde, wanda ya rasu yana da shekara 88.
Shugaban ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya NFF da hukumar wasanni ta ƙasa tare da abokan aikinsa da magoya bayan ƙwallon ƙafa, yana mai tuna gudummawar da marigayin ya bayar a matsayin kocin Super Eagles na farko a shekarar 1982.
Saƙon ta’aziyyar shugaban ƙasar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata.
Shugaba Tinubu ya yaba da gudummawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa tun daga matakin ƙananan yara, da kuma ƙarfafa tsarin tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Ya kuma tuna da rawar da marigayin ya taka lokacin da ya jagoranci tawafar ƙwallon ƙafar Najeriya zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa ta Afrika a shekarar 1984..
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwarsa a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin ‘yan uwansa, Bolade Adesuyi, ya fitar.
Iyalan sun ƙara da cewa za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa a gaba.






