Daga Gaddafi zuwa Khamenei: Me Putin ya ce bayan faɗuwar abokansa?

Asalin hoton, DMITRY AZAROV/SPUTNIK/AFP via Getty Images
- Marubuci, ساندرو گویندادزه
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بخش مانیتورینگ بیبیسی
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani abu ya faru da aka yi tunanin Shugaban Rasha, Vladimir Putin zai yi amma, sai dai kuima bai yi ta ba.
A ranar 28 ga watan Fabrairu, aka kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a wasu hare-haren Amurka da Isra'ila.
Kwana guda bayan haka Shugaba Putin ya bayyana kisan nasa a matsayin aikin ''ta'addanci'' kuma ''babban saɓa wa dokokin duniya da mutunta ɗan'adam''.
To amma bai ambaci sunan wanda ya aikata laifin.
Cikin sakon ta'aziyyar da ya aike wa Shugaban Iran, Masoud Pezzekian ya kauce wa kama sunan Amurka da Isra'ila.
A watan Janairun 2025 ne Iran da Rasha suka ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro, to amma ba ta wajabta wa Moscow bai wa Iran tallafin soji ba.
A watan Yunin 2025, lokacin da Amurka ta kai harin bom cibiyoyin nukiliyar Iran, Mista Putin ya bayyana matakin da ''cikakken takalar faɗa ga Iran'', wanda ''babu dalilin aikata shi,'' amma a nan ma ya guje wa ambaton sunan Amurka.
A baya da aka tambaye shi, abin da zai yi idan Amurka da Isra'ila suka kashe Ali Khamenei, Putin ya ce ''bana son yin magana game da wannan batu.''
Sashen bibiya na BBC ya yi nazarin saƙonnin da fadar gwamnatin Rasha da kafofin yaɗa labaran suka suka fitar domin yin nazarin kalaman Putin bayan faɗuwar wasu ƙawayen Rasha biyar tsakanin 2011 zuwa 2026.
Yayin da a baya, Vladimir Putin ke ambaton sunayen waɗanda suka aikata laifi, a baya-bayan nan baui fiye ambaton suna, koma yakan yi shiru a wasu batutuwan.
Gaddafi da Yanukovych: Kakkausan martani
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar Libya, Muammar Gaddafi a watan Oktoban 2011, Mr. Putin ya yi magana mai yawa.
Ya yi magana kan ''jiragen Amurka marasa matuƙa'' da suka kai hari kan tawagar motocin Gaddafi sannan ya yi magana kan ''dakarun ƙasashen waje da ya ce bai kamata su shiga Libya ba''.
Ya bayyana kisan Gaddafi a matsayin kakkaɓe shi ''ba tare da bincike ko shari'a ba'', sannan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani.
Haka ma Mista Putin ya yi magana sosai bayan kawar da Viktor Yanukovych daga shugabancin ƙasar Ukraine a watan Fabrairun 2014.
A wani taron manema labarai ranar 4 ga watan Maris ɗin 2014, ya bayyana sunayen ministocin ƙasashen waje na Poland da Jamus da Faransa a matsayin waɗanda suka cimma yarjejniya tsakanin gwamnati da ƴan hamayya.
Ya kuma bayyana ƙarara cewa ya taimaka wa Mista Yanukovych tserewa zuwa yanzun Crimea.
Shekarun da suka biyo bayan nan, Mista Putin ya sha zargin Amurka da shirya abin da ya kira ''juyin mulki'' a Ukraine da kuma yaudarar Rasha.
Assad: Ɗaukar mataki ba tare da furta komai ba
A lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Basha al-Assad a Siriya farkon Disamban 2024, Rasha ce ta ɗauke shi zuwa Moscow tare da ba shi mafaka, amma a jawabin da Putin ya yi kan batun, bai yi alla wadai ba, bai kuma ambaci sunayen masu laifi ba.
Kusan mako biyu bayan komawar Bashar al-Assad zuwa Rasha, Vladimir Putin ya shaida wa manema lanbarai cewa bai gana da tsohon shugaban na Siriya ba tun bayan zuwansa ƙasar.
Ya kuma ce ''abin da ke faruwa a Siriya ba ya nuna cin nasara a kan Rasha''.
Wata 13 bayana nan, Putin ya taya sabon shugaban riƙon ƙwaryar Siriya, Ahmed al-Sharaa, murnar mayar da ƙasar turbarta.
Maduro: ba um, ba um-um
A watan Janairun 2026, a lokacin da sojojin Amurka suka kama shugaban Venezueal, Nicolas Maduro tare da kai shi Amurka, Mista Putin bai ce komai ba.
A maimakon haka mataimakin shugaban majalisar tsaron ƙasar, Dmitry Medvedev da jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia da kakakin ma'aikatar wajen ƙasar, Maria Zakharova, ne suka yi Allah wadai da matakin.
Amma babu wata sanarwa a hukumance daga fadar Kremlin.
Khamenei: Allah wadai, babu sunan masu kisan
Saɓanin kama Nicolas Maduro, kisan Ali Khamenei ya samu martani daga fadar Kremlin, amma Putin ya kauce wa ambaton sunan masu kisan.
Wannan ya nuna abin da Alexander Baunov, babban jami'i a Cibiyar Carnegie Berlin, ya bayyana da tsarin "harsunan siyasar'' Rasha: Ma'aikatar Harkokin Waje na da alhakin aika maganganun nuna ƙyama ga Amurka, yayin da Fadar Kremlin ke bin wata hanya ta daban game da Donald Trump.
Baunov ya kuma ce kalaman da Vladimir Putin ya yi kan Ali Khamenei sun ma fi rauni fiye da kalaman da ya yi a baya kan kashe Qassem Soleimani, tsohon kwamandan dakarun Quds na IRGC, a wani harin da Amurka ta kai a shekarar 2020.
"Sun je suka kashe wani Janar na Iran, gaba daya hankalinsu ya tashi," kamar yadda ya bayyana a lokacin.
A lokacin Putin ya gaza ambaton sunan Donald Trump.
Ekaterina Kotrikadze, wata ɗarjaridar ƙasar da ke zaman gudun hijira a ƙasar waje, ya ce Vladimir Putin na cikin mawuyacin lokaci.
ya ci gaba da cewa ba zai iya fitowa fili ya soki Amurka ba kamar yadda yake yi a baya, to amma shirun da yake yi tamkar gazawa ce a gare shi.
"Ɗaya bayan ɗaya manyan abokansa na faɗuwa, wanda babban koma-baya ne gare shi. To amma ba zai iya mayar da martani ba, saboda har yanzu Rasha na son ƙulla alaƙar kasuwanci da Shugaba Trump,'' kamar yadda ya bayyana.
Wani masanin harkokin siyasar ƙasar, Alexander Morozov, ya ce yaƙin Iran ya fallasa tsohon yayin salon yaƙin Putin da kuma jefa fadar Kremlin cikin tsaka mai wuya.
''Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Mista Putin shiru da bakinsa shi ne yana ganin matakan da Trump ke ɗaukar tamkar barazana ce a gare shi.
A 2011, wani ɗanmajalisar dattawan Amurka, John McCain ya ce Vladimir Putin zai fuskanci ''irin makomar Gaddafi.'' Amma sai Putin ya mayar masa da martani da tuhumar lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
Sai dai Amurka ba su taɓa yin irin waɗannan kalaman ba. Amma martanin Putin ya sauya daga zargi kai-tsaye zuwa matakin da yake kai yanzu na daina ambatar sunan kowa.










