Ƙasashen Afirka 7 da aka fi biyan ma'aikata albashi mai gwaɓi

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wani sabon rahoto da LiveGDP ya fitar ya gano manyan bambance-bambance a matakan albashi tsakanin ƙasashen Afirka, inda Djibouti ta kasance a kan gaba da mafi girman matsakaicin albashin wata da ma'aikaci ke samu bayan cire haraji da sauran kuɗaɗen da doka ta tanada.

A cewar rahoton, matakan albashi suna bambanta ne saboda wasu dalilai daban-daban, ciki har da matakin ci gaban tattalin arziki da ƙwarewar ma'aikaci a aikinsa, datasirin wasu ɓangarori alal misali sassas da suka shafi na man fetur da ma'adinai da yawon buɗe ido da na ɓangaren kuɗi, da kuma buƙatun ƙungiyar ƙwadago.

Sauran abubuwan da ke shafar kuɗin shigar ma'aikata sun haɗa da yawan haraji da hauhawar farashi da darajar kuɗin ƙasa da yanayin samar da ayyukan yi a kowace ƙasa.

A cikin rahoton da aka fitar, Kenya ta kasance ta 10 cikin ƙasashen Afirka 54 wajen matsakaicin albashin wata bayan cire kuɗaɗen da suka danganci haraji da sauran su.

Bayanai sun nuna cewa ma'aikaci a Kenya yana samun matsakaicin shilingi 44,553 (dala 344) a wata bayan cire kuɗaɗe, matakin da ya sanya ƙasar a matsayi na 132 a duniya.

"Kenya tana da matsakaicin albashin wata na dala 344 bayan cire kuɗaɗe kuma tana matsayi na 10 a Afirka," in ji rahoton.

A yankin Gabashin Afirka, Kenya ta fi maƙwabtanta da suka haɗa da Tanzaniya da Uganda da Rwanda, amma ta kasance a bayan Djibouti, wadda ta jagoranci ba Gabashin Afirka kaɗai ba har ma da nahiyar baki ɗaya da matsakaicin albashin dala 2,836 a wata.

Sai dai LiveGDP ya yi gargadin cewa ba za a iya amfani da bayanan albashi kaɗai wajen auna yanayin rayuwa ko ikon sayen kayayyaki da sauran wasu abubuwa na daban ba, saboda farashin gidaje da abinci da sufuri da kiwon lafiya da ilimi da kuma hauhawar farashi sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.

Ga jerin ƙasashen Afirka bakwai da ke da mafi yawan albashi mafi gwaɓi.

1. Djibouti

Djibouti ce ke kan gaba a Afirka wajen matsakaicin albashi a wata da ma'aikaci ke samu bayan cire haraji, wanda ya kai kusan KSh 367,311 (dala 2,836).

Ƙasar tana bakin ƙofar Bahar Maliya da Tekun Aden, kusa da ɗaya daga cikin hanyoyin safarar jiragen ruwa mafi yawan cunkoso a duniya. Hakan ya sanya ta zama muhimmiyar cibiyar safarar kaya da ayyukan tashoshin jiragen ruwa.

Matsayinta na dabaru a kan hanyoyin kasuwanci na Bahar Maliya da kuma kasancewar sansanonin sojojin ƙasashen duniya a cikinta sun taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikinta.

2. Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ta kasance ta biyu da matsakaicin albashi na KSh 164,486 daidai da dala 1,270.

A matsayinta na ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu tattalin arziki a nahiyar, ƙasar ta bunƙasa fannonin hakar ma'adinai da na kuɗi da masana'antu da sauran muhimman ayukka.

3. Tsibirin Seychelles

Tsibirin Seychelles yanki ne da ya biyo baya da matsakaicin albashi na KSh 102,318 daidai da dala 790.

Tattalin Seychelles ya fi dogara ne kan yawon buɗe ido da kamun kifi da da sauran ɓangarorin da suka shafi hada-hadar kuɗi, yayin da ƙarancin yawan jama'a ke taimakawa wajen samar da albashi mai tsoka da kuɗin shiga ga kowane mutum.

4. Mauritius

Mauritius na daga cikin ƙasashen Afirka da ke da mafi yawan albashi saboda tattalin arzikinta ya bambanta, wanda ya haɗa da yawon buɗe ido da hada-hadar kuɗi da ƙre-ƙere da kuma tarin kamfanonin yin da masana'antar masaku. Haka kuma, ƙasar ta shahara da kyakkyawan yanayin kasuwanci.

5. Gabon

Gabon na amfana da yawan man fetur da sauran albarkatun ƙasa da take da su.

Duk da ƙarancin yawan jama'arta, kuɗaɗen shiga daga ɓangaren man fetur sun sanya ta cikin ƙasashen da ke da albashi mafi gwaɓi a nahiyar ta Afirka.

6. Botswana

Botswana ta yi suna wajen samun kwanciyar hankali a fagen siyasa da kuma kyakkyawan tsarin tafiyar da kuɗaɗen shiga da take samu saboda arzikin ma'idinin lu'u-lu'u.

Bangaren ma'adinai ya kasance gimshiƙi mai muhimmanci wajen taimaka wa ƙasar ta ci gaba da samun albashi mai tsoka idan aka kwatanta da ƙasashe da dama na Afirka.

7. Namibia

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Namibia ta shiga jerin ƙasashe bakwai da ke da mafi yawan albashi. Tattalin arzikinta ya dogara ne kan haƙar ma'adinai da kamun kifi da yawon buɗe ido, yayin da ƙarancin yawan jama'a da kuma ƙaƙƙarfan tsarin tattalin arziki ke taka rawa wajen samar da albashi mai gwaɓi.

A cewar bayanan ƙididdiga, Kenya ta kasance ta 10 a Afirka, inda matsakaicin albashin wata ya kai KSh 44,553 kwatankwacin dala 344, bayan cire haraji. Hakan ya sanya ta kasance a gaban ƙasashen Gabashin Afirka da dama, ciki har da Tanzania da Uganda da kuma Rwanda.

Sudan ta Kudu ce ta samu mafi ƙarancin matsakaicin albashi, wanda ya kai shilingi 9,066 daidai da dala 70, sai Burundi da shilingi 9,713 daidai da dala 75 da Saliyo wadda ke da shilingi 10,361 wato dala 80, sai Gambia da shilingi 11,008 (dala 85), sannan Malawi da Sudan masu shilingi 11,656 (dala 90) kowannensu.

Sai dai LiveGDP ya yi gargaɗin cewa ba za a iya amfani da bayanan albashi kaɗai wajen auna rashin talauci a rayuwa kai tsaye ba.

Farashin gidaje da na abinci da sufuri da kiwon lafiya da ilimi, dahauhawar farashi da hawa da saukar darajar kuɗin ƙasa sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.