Manyan basuka shida da Bola Tinubu ya ci bayan hawa mulki

Asalin hoton, STATE HOUSE
A ranar Alhamis ɗin nan ne Majalisar dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na karɓo bashin dala biliyan 2.347 daga kasuwannin hada-haɗar kuɗi ta duniya domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan takardun lamuni na Eurobonds da ke ƙarewa.
Tinubu ya bayyana cewa bashin zai kasance bisa tanade-tanaden dokar kula da bashi ta 2003, wadda ke buƙatar amincewar majalisa kafin ɗaukar sabon bashi ko sake biyan tsoffin bashi.
Wannan ne karo bakwai da gwamnatin Tinubu ke cin bashi a tsawon shekaru biyu da rabi.
A ƙarshen watan Yuli ne Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da ƙudurin shugaban ƙasar Bola Tinubu na cin bashin kuɗi sama da dala biliyan 21 domin cike giɓin kasafin kudin shekara ta 2025.
Gwamnatin Najeriyar ta ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen samar da ayyukan ci gaba da kiwon lafiya da ilimi da tsaro da kuma samar da muhalli. Za a ware dala biliyan uku domin farfadowa da kuma gyara titin jirgin ƙasa na gabashin ƙasar.
Ga jerin manyan basuka shida da aka amince wa Bola Tinubu karɓowa daga farkon kama mulkinsa:
22 ga watan Yuli 2025
Majalisar Dattijai ta amince da buƙatar gwamnatin tarayya ta karɓar bashi dala biliyan 21 daga waje, domin amfani da shi a shekarar kuɗi ta 2025 zuwa 2026.
6 ga watan Mayu 2025
Gwamnatin tarayya ta amince da karɓar bashi dala miliyan 652 daga Bankin Exim na China domin gina titi daga tashar ruwa ta Lekki zuwa matatar man fetur.
21 ga watan Nuwamba 2024
Majalisar Dattijai ta goyi bayan buƙatar karɓo bashi dala biliyan 2.21 daga waje domin cike giɓin kasafin kuɗin 2024.
13 ga watan Yuni 2024
Najeriya ta karɓi bashin dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya domin daidata tattalin arziƙi da tallafa wa talakawa.
1 ga watan Mayu 2024
Majalisar Dattijan Najeriya ta amince wa gwamnatin tarayya ta karɓi bashin dala miliyan 500 domin samar da mitar wutar lantarki, wanda ke cikin shirin karɓar bashi dala biliyan 7.94 daga waje tsakanin shekara ta 2022 zuwa 2024.
30 ga watan Disamba 2023
Majalisar Dattijai ta goyi bayan karbar bashin dala biliyan 7.4 da yuro miliyan 100 a matsayin wani ɓangare na shirin karɓar bashi dala biliyan 7.94 tsakanin shekara ta 2022 zuwa 2024.
Ya zuwa ƙarshen watan Maris na wannan shekara ta 2025, bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 149.39, inda aka samu ƙarin naira tiriliyan 27.72, wato kashi 22.8 cikin ɗari idan aka kwatanta da bashin da ake bin ƙasar a watan Disamban 2024, in ji ofishin lura da basuka na ƙasar.
Ƙaruwar da ake samu na kuɗin bashin da ake bin ƙasar na faruwa ne sanadiyyar ƙarin ciwo sabbin basuka da kuma raguwar darajar naira wajen sauke nauyin bashi da ke kan ƙasar.











