Bashi ya yi wa Najeriya katutu - Masana

Tinubu

Asalin hoton, presidency

Bayanan hoto, Shugaba Bola Tinubu

Yayin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da ciwo bashi domin gudanar da ayyukan ta, masana sun ce lamarin tarko ne ga makomar tattalin arzikin ƙasar.

Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun bayyana damuwa kan yawan bashin, wanda su ka ce ya kamata a ɗauki mataki a kai.

Matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na ci gaba da ciwo bashi domin gudanar da aiki na ƙara haifar da shakku a tsakanin masana tattalin arziki da sauran masu ruwa da tsaki.

Yanzu haka dai, bashin da ke kan ƙasar ya zarce dala tiriliyan 87, kamar yadda ofishin kula da bashin Najeriyar ya ya sanar.

Wannan dai kididdiga ce ta zangon ƙarshe na wannan shekara, kuma hakan na nuna cewa an samu ƙarin fiye da kashi 75 na jimillar bashin ƙasar a ƙarshen watan Maris ɗin bana.

Wannan ya sa kwararru a fannin tattalin arziki irin su Dr Isma’il Anchau na kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Kaduna ke ganin cewa an kai maƙura.

"Wannan karon an ware kudin biyan bashi sama da naira tiriliyon 7, yayin da ɓangaren manyan ayyuka aka ware sama da tiriliyon takwas, wato dai banbancin kaɗan ne tsakaninsu, idan aka cire abin da ake bin bashi kashi 40, to zai zama yana rage bunƙasar tattalin arziƙi da kashi biyu, kuma Najeriya ta doshi shiga wannan matakin," in ji Dr Isma'il Ancahu.

Shin me ne ne Mafita?

.

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, Takardun kudin Nijeriya

Masanin tattalin arziki ya ce idan aka shiga irin halin da Najeriya ta tsinci kanta a fannin tattalin arziki, to kamata ya yi gwamnati ta waiwayi cikin gida don neman mafita, a madadin ƙara ciwo bashin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Isma'il Anchau ya ce "Yanayin yadda ake kashe kuɗaɗe wajen tafiyar da gwamnati, misali albashin da ake ba ƴan majalisar ƙasar masu adadi fiye da 300 da duk kuɗaɗen da ake basu za a iya ragewa, sai kuma a duba yadda ake tafiyar da gwamnati da duk wasu kuɗaɗe da ake kashewa, kamar fitar da mtane ƙasar waje domin samun horaswa da wasun su basu cancanta ba da sauran wasu abubuwa duk idan aka rage za a iya samun sauƙi.

Masanin tattalin arziƙin naganin inda gwamnati za ta mayar da hankali wajen shawo kan matsalar danyen mai za a ƙara samun kudaden shigar gwmanati.

"Sannan kuma tallafin da aka cire ya kamata yana bada gudumuwa wajen ƙaruwar kuɗaɗen shiga an Najeriya, sai dai babu alamar hakan, " In ji Dr Isma'il.

Ba dai wannan ne karon farko da ƙungiyoyi da ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki ke bayar da shawara kan illar cin bashin, da ma hanyoyin bunƙasa tattalin arziki ba, amma Dr Isma’il Anchau ya ce an baro gini tun ranar zane.

" Wasu masana tattalin arziki da dama na bin mas'habar jari hujja, inda suke nuna cewa ciwo bashi kuma a duƙi matakan yi wa tattalin arzƙi kwasƙwarima kamar irin su, cire tallafi da sayr da kadarorin gwamnati da ƙara haraji da bar wa kasuwa ta yi halin ta, sai dai ba lallai wadannan matakan su yi wa Najeriya aiki ba, saboda ya kamata kowace ƙasa ta duba yanayin tattalin arziƙinta a duk wani mataki da za ta ɗauka," cewar Dr Isma'il

Yayin da masana ke bayyana rashin amincewar su da salon ciwo bashin na gwamnatin Najeriya, gwamnati a nata ɓangaren ta jajirce cewa shi ne mafita a halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki yanzu