Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya

Asalin hoton, @jidesanwoolu

Bikin gabatar da kasafin kudin a Najeriya da shugaban kasar ya yi ga majalisar dokoki ya bar baya da kura, inda wasu `yan majalisar ke zargin cewa shugaban kasar ya yaudare su inda suka ce ya mika musu kundin kudurin kasafin kudin 2024 na bogi.

A ranar Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.

Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.

Sai dai ƴan majalisar sun ce "babu komai a cikin wani dan akwatin da shugaban kasar ya rusuna ya ajiye a gaban zauren majalisar."

Hon Yusuf Shitu Galambi, dan majalisar wakilan Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ko shakka babu shugaban kasa ya karanta musu jawabinsa na kasafin kudi, amma maganar kundi na kasafin kudin ba su ganshi ba.

Ya ce, " Shugaban kasa ya karanta mana lissafe lissafen kudin, to amma a jiye gundarin yadda kasafin yake na kowacce ma'aikata kamar yadda aka saba yi ba a kawo shi ba."

Dan majalisar ya ce," Mun duba kundin da ya ajiye amma ba mu ga komai a cikinsa ba."

Hon Yusuf Shitu Galambi, ya ce a tarihin majalisar wakilai ta tarayya ba a taba irin abin da aka yi ba a wannan karon, kuma kundin tsarin mulki ba haka ya ce a yi ba.

Ya ce,"Mu kanmu 'yan majalisar wannan abu ya daure mana kai, saboda abu ne wanda ba a taba gani ba sannan ba a taba zata ba ko a mafarki."

"Muna ganin wannan abu kamar yaudara ce, tun da dai idan ba a shirya ba don me za a zo ace mana amma na gama komai, ai sai a nemi karin lokacin har zuwa lokacin da za a gama ai ba gaggawa a ciki."

Dan majalisar ya ce, tun da yanzu dai kundin kasafin kudin babu komai a ciki, dole su dan yi jinkiri har zuwa lokacin da shugaban kasa zai kawo bayanai na dalla-dalla a kan kasafin kudin.

'Babu yaudara'

Sai dai a ɓangare guda wasu ƴan majalisar ta wakilai sun ce babu yaudara a cikin gabatar da kundin kasafin kudin da shugaba Bola Tinubu ya yi wa majalisar.

Hon Sada Soli Jibia, wanda ɗan majalisar wakilan ne wanda ya ce bisa al'ada sai majalisa ta bi waɗansu matakai kafin raba kwafen kasafin kudin ta yadda kowane dan majalisa zai ga abin da suka kunsa.

Sai dai Sada Soli ya ce ya zuwa ranar Juma'a ba su ga kundin kasafin kuɗin ba kasancewar a cewar sa "Zuwa yanzu ana bugawa a maɗaba'ar da ake buga takardu ta majalisa."

Ya ƙara da cewa a ranar Asabar kwamiti kan kasafin kuɗi zai gana da shugabannin kwamitocin majalisar, kafin daga baya a bai wa kowane ɗan majalisa nasa kwafen na kasafin kuɗin.