Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 12/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 12/01/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Diginza, Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Gwamnatin Somalia ta yanke hulɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    Gwamnatin Somaliya ta sanar da yanke hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da soke duk wasu yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin ƙasashen biyu.

    Wata sanarwa da aka fitar bayan taron majalisar ministocin ƙasar ta ce an soke duk wasu yarjejeniyoyin da aka rattabawa hannu da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da suka haɗa da tasoshin jiragen ruwa da haɗin gwiwar tsaro.

    Matakin ya shafi duk shirye-shiryen da suka shafi tashoshin jiragen ruwa a Berbera, Bosaaso, da Kismayo, da kuma yarjejeniyoyin da aka yi da hukumomin tarayya, da hukumomin da ke da alaƙa da su, da kuma gwamnatocin yankuna.

    Daga cikin yarjejeniyoyin da abin ya shafa har da yarjejeniyar tashar jiragen ruwa ta Berbera, wadda a ƙarƙashinta gwamnatin Somaliland ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar gudanarwa a shekarar 2016 da kamfanin DP World.

    Gwamnatin Somaliya dai ta daɗe tana adawa da yarjejeniyar, tana mai cewa an ƙulla yarjejeniyar ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba.

    Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin kare ƴancin Somaliya da haɗin kan yankunan ƙasar, da kuma tsarin mulkinta.

  2. MSF ta yi gargaɗi kan shirin mayar da ƴan gudun hijiran Burundi daga Tanzania

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF) wadda aka fi sani da Doctors Without Borders, ta yi gargaɗin cewa shirin mayar da ƴan gudun hijirar Burundi sama da 50,000 daga sansanonin da ke yammacin Tanzaniya na iya haifar da matsalar jin ƙai.

    A watan Disambar 2025, gwamnatin Tanzaniya ta ba da sanarwar soke matsayin ƴan gudun hijira kan ƴan Burundi da kuma rufe sansanonin ƴan gudun hijira a ƙasar kafin watan Yunin 2026.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, MSF ta ce dole ne tsarin mayar da mutanen ya ba da fifiko kan tsaro, lafiya da mutunci, tana mai gargaɗin cewa wannan shiri na iya jefa rayuka cikin haɗari.

    MSF, wadda ke ba da agajin kiwon lafiya a sansanin ƴan gudun hijira na Nduta tun 2015, ta ce yawancin ƴan gudun hijirar suna fama da rashin lafiya kuma suna fuskantar haɗari mai tsanani idan aka dawo da su.

    Hukumomin Tanzaniya da Burundi ba su mayar da martani kan gargaɗin na MSF ba.

  3. Ayatollah ya gargadi ƴan siyasar Amurka kan zanga-zangar Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran addini na Iran Ali Khamenei ya jinjinawa gangamin da aka yi na goyon bayan gwamnati, inda ya ce ya zo ne a matsayin gargadi ga ƴan siyasar Amurka da su kawo ƙarshen abin da ya kira yaudarar da suke yi wa duniya.

    Ayatollah ya ce yau rana ce ta tarihi inda aka daƙile shirin maƙiyan Iran.

    Ya bayyana zanga zangar a matsayin gargadi ga Amurka, da waɗanda ya ƙira sojojin hayar Amurka.

    A halin da ake ciki kuma, rahotanni na cewa adadin masu zanga zangar ƙin jinin gwamnatin da jami'an tsaro suka kashe na ci gaba da ƙaruwa.

    Wata ƙungiyar ƙare hakkin biladama ta Iran da ke Norway, ta ce a yanzu ta tabbatar da aƙalla mutum ɗari shida da hamsin da lamarin aka kashe.

    Sai dai ta yi gargaɗin cewa wasu sun yi ƙiyasin mutum fiye da dubu shida sun mutu.

    Hukumomi a Iran ɗin sun sake yi wa shugaba Trump gargaɗin kar ya aiwatar da matakin da ya ce zai ɗauka, tare kuma da cewa a shirye suke a tattauna.

  4. Mawaƙan Najeriya sun taka rawar gani a bikin karrama mawaƙan Afrika

    Burna Boy

    Asalin hoton, Getty Images

    Mawaƙan Najeriya sun samu nasarori da dama a bikin karrama mawaka na All Africa Music Awards (Afrima), wanda aka kammala a Legas a daren Lahadi.

    Shahararren mawaƙin Najeriya Burna Boy ya yi nasarar lashe kyautar Album na Shekara da sabon aikinsa mai suna 'No Sign of Weakness.'

    Ya kuma lashe kyautar waƙar haɗin gwiwa mafi ƙayatarwa da wakar da ya yi da mawaki mai tasowa Shallipopi, wanda shi kuma lashe kyautar waƙar da ta fi tashe a shekarar da waƙarsa mai suna 'Laho' wadda ta yi tashe a shafukan sada zumunta.

    Wasu fitattunƴan Najeriya da suka yi nasara sun haɗa da Yemi Alade, wacce ta lashe Kyautar Sauti a Fim, da wakar ta mai suna 'You Are' daga fim ɗin Iyanu, da kuma gogaggen mawaƙin Hip Hop, Phyno, wanda ya lashe lambar mawaƙin da ya fi tashe a ɓangaren African Hip-Hop.

    Bikin wanda aka ɗauki tsawon mako guda ana gudanar da shi, ya samu halarcin ƙwararrun masana kaɗe-kaɗe daban-daban da cikin nahiyar Afirka da kuma na ƙasashen waje a matsayin alkalai.

  5. Mu na samun haɗin kai daga gwamnatin riƙon Venezuela - White House

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Fadar White House ta ce mahukuntan Venezuela da shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar Delcy Rodriquez suna ba da haɗin kai sosai ga Amurka.

    Sakatariyar yaɗa labarai, Karoline Leavitt, ta shaidawa manema labarai cewa, Venezuela ta amince da gagarumar yarjejeniyar makamashi kuma ta nuna aniyar sakin fursunonin siyasa.

    Tun da farko gwamnatin Venezuela ta ce ta saki fursunoni 116 da aka tsare bisa umarnin hamɓararren shugaban ƙasar Nicolas Maduro.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙi sun musanta wannan adadin, inda su ka ce yawan waɗanda aka sako bai kai haka ba.

    Fiye da fursunonin siyasa 800 ake tunanin suna garƙame a gidajen yarin Venezuela.

  6. Real Madrid ta naɗa Álvaro Arbeloa domin maye gurbin Alonso

    Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Real Madrid ta sanar da naɗa tsohon ɗan'wasanta Álvaro Arbeloa a matsayin sabon kocinta domin maye gurbin Xavi Alonso.

    Álvaro Arbeloa tsohon ɗanwasan ƙasar Spain ne da Real Madrid, inda ya kasance yana buga baya.

    Kafin naɗa shi wannan matsayin, shi ne mai horas da matasan ƴanwasan ƙungiyar.

  7. Ba zan sauka ba duk da binciken da nake fuskanta - Shugaban babban bankin Amurka

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban babban bankin Amurka, Jerome Powell ya kafe cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba, duk da binciken shi da ma'aikatar shari'ar kasar ke yi kan aikata laifuka.

    Ya ce barazanar da ake yi masa kan bahasin da ya bai wa majalisar dokoki kan aikin gyara wani gini, wani shiri ne kawai na matsawa babban bankin Amurka lamba kan rage kuɗin ruwa.

    Ya ce zai ci gaba da yin aikin da majalisar dattajan ƙasar ta amince masa ya yi.

    Wakilin BBC ya ce a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta NBC a jiya Lahadi, mista Trump ya ce ba shi da masaniya kan binciken da ake yi. Sai dai a cewar sa Mista Powell din ba ya aiki yadda ya kamata.

  8. Xavi Alonso ya ajiye aikin horas da ƙungiyar Real Madrid

    Xavi

    Asalin hoton, BBC Sport

    Xavi Alonso ya ajiye aikinsa na horas da ƴan'wasan ƙungiyar Real Madrid kwana ɗaya bayan Barca ta doke ta a gasar Spanish Super Cup.

    Tuni ƙungiyar ta maye gurbinsa da tsohon ɗanwasanta Alvaro Arbeloa.

    A wata sanarwa da ƙungiyar a kafofin sadarwa, ta ce sun amince su rabu da Alonso ne ta hanyar fahimtar juna domin a rabu lafiya.

    "Za mu ci gaba da girmama Xavi Alonso a Real Madrid kuma yana da daraja da wuri na musamman," kamar yadda ta wallafa.

    Madrid ta ƙara da cewa tana godiya da gudunmuwar da ya bayar wajen horas da ƴan'wasanta, "sannan muna masa fatan alheri a gaba."

    Alonso ya lashe wasa 24 ciki wasa 34 da ya jagoranci ƙungiyar a cikin wata takwas da ya yi.

  9. Magoya bayan Kwankwaso sun ƙi halartar taron Gwamna Abba

    ...

    Asalin hoton, BBC Collage

    A daidai lokacin da raɗe-raɗen sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ke ci gaba da ɗaukar hankali a Kano, an sake ganin wata sabuwar ɓarakar da ke nuna akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamnan da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

    A ƙarshen mako, wasu manyan magoya bayan Kwankwaso sun ƙaurace wa taron yaye ɗaliban da suka koyi sana’o’in hannu, wanda gwamna Abba ya jagoranta a fadar gwamnatin jihar.

    Rashin ganin fuskokin wasu fitattun ‘yan Kwankwasiyya a taron ya ƙara dasa alamar tambaya kan alaƙar da ke tsakaninsu.

    Wannan dai shi ne karo na farko da aka ga gwamnan a bainar jama’a bayan shafe fiye da mako guda ba tare da fitowa fili ba.

    Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai Hashim Sulaiman Dungurawa, wanda makusancin Kwankwaso ne. Sai dai a wurin taron, Abdullahi Zubairu Abiya ne ya halarta a matsayin sabon shugaban jam’iyyar NNPP a jihar.

    Akwai kuma wasu waɗanda ake gani makusantan Kwankwaso ne da suke tare da Kwankwaso da ba su halarci taron ba.

    Daga cikinsu akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr Yusuf Kofar Mata; da Kwamishinan Tsaro na Kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya, tare da Shugaban Ma’aikata, Abdullahi Musa.

  10. Ko APC da Tinubu za su iya hana tsige Fubara?

    Rivers

    A daidai lokacin da siyasar jihar Rivers ke ƙara ɗaukar zafi, musamman kan sake yunƙurin majalisar jihar ta tsige Gwamna Sim Fubara, masu sharhi kan harkokin siyasa sun fara muhawara kan abubuwan da za su iya faruwa.

    A ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026 ne dai majalisar jihar Rivers ta sake bijiro da batun yunƙurin tsige gwamna jihar, bayan musayar yawu da takun-saƙa da aka lura akwai a tsakaninsu.

    Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya gabatar da takardar neman majalisar ta fara yunƙurin tsige gwamnan, bisa zarginsa da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.

  11. Venezuela ta saki fursunonin siyasa 116 da aka kama ƙarƙashin Moduro

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Venezuela ta ce ta saki fursunoni 116 waɗanda aka kama a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Nicolas Maduro wanda aka tsige.

    Hukumomin ƙasar sun ce waɗanda aka saka ɗin an tauye musu ƴancinsu saboda sun yi wa zaman lafiyar ƙasar zagon ƙasa.

    Tun da farko ƙungiyoyin kare hakkin biladama sun tabbatar da sakin fursunoni arbain da ɗaya.

    Gwamnatin ta ce za ta saki adadi mai yawa na fursunonin, bayan da shugaba Trump ya sanar da cewa za a rufe sanannen gidan yarin nan na El Helicoide da ke Caraacas.

    Iyalan ɗaruruwan fursunonin siyasar sun taru a wajen sanannen gidan yarin da ke Caracas, suna sa ran a sako ƴan uwansu.

    Ƴan adawa sun ce fiye da fursunonin siyasa 800 ne ke gidan yarin.

  12. 'An shawo kan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun shawo kan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka shafe kwanaki ana yi a ƙasar.

    A yau Litinin ne magoya bayan gwamnati suka bazama kan tituna, lamarin da ya sha bamban da abin da ya faru kwanaki uku da suka gabata.

    Kafafen yaɗa labarai na gwamnati na ƙoƙarin nuna cewa al’amura sun koma daidai, sai dai katse hanyoyin sadarwa da aka yi ya sa ba a iya tantance sahihancin bayanai.

    Rahotanni dai na nuna cewa fiye da mutum dubu ɗaya ne ake zargin sun rasa rayukansu yayin da ake ƙoƙarin kawo ƙarshen zanga-zangar.

    Ma’aikatan lafiya sun bayyana cewa asibitoci sun cika da mutanen da suka jikkata sakamakon harbin jami’an tsaro.

    A halin da ake ciki, Shugaban Amurka Donald Trump dai ya yi barazanar ɗaukar matakin soji domin kare masu zanga-zangar, yana mai cewa shugabannin Iran na neman a shiga tattaunawa, duk da cewa ya ce yana iya kai hari kafin a kai ga hakan.

  13. Ƴanbindiga sun kai hari kan masana’antu a Mali

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Yammacin Mali na cewa mayaƙa masu iƙirarin jihadi sun kai hari kan wasu masana’antu da dama a tare da ƙona su.

    An zargi iƙirarin jihadi mai alaƙa da al-Qaeda da hannu a lamarin, wanda ke nuna ƙarin yawan hare-hare kan manyan wuraren tattalin arziki a yankin.

    Aƙalla mutum huɗu ne aka sace yayin hare-haren, kamar yadda rahotannin yankin suka bayyana.

    An kai hare-haren ne kan masana’antu guda uku masu sarrafa siminti da sauran kayayakin gine-gine, ranar Lahadi a yankin Kayes.

    Rahotanni daga yankin sun ce masu harin sun isa yankin a kan babura ɗauke da manyan makamai, kuma an ƙiyasta cewa sun kai tsakanin mutum 150 zuwa 200.

    Yankin Kayes ya sha fama da irin waɗannan hare-hare a ‘yan watannin baya.

    A watan Yuli, an zargi masu iƙirarin jihadi da kai hari kan masana’antu a wannan yanki, inda suka sace ma’aikata da dama, ciki har da wasu ‘yan Indiya.

  14. Majalisar jihar Rivers ta zargi wasu da yunƙurin hana tsige Fubara

    ...

    Asalin hoton, Rivers state Government House Media

    Majalisar Dokokin jihar Rivers ta yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na ƙoƙarin yin amfani da kotu wajen neman toshe ƙofar tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

    A cewar majalisar, yunkurin neman umarni daga babbar kotun jihar da ke wajen birnin Fatakwal na nuni da ƙoƙarin dakatar da yunƙurin tsige shi.

    Shugabannin majalisar sun jaddada cewa tsarin tsige gwamnan yana tafiya ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba za su bari wani matsin lamba ko tsoma bakin waje ya hana su sauke nauyin da doka ta ɗora musu ba.

    Sun kuma ce duk wanda ke da ƙorafi ya bi hanyoyin doka da oda, yayin da suke tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da bin doka wajen gudanar da dukkan matakan da suka shafi batun tsige gwamnan.

    'Yan majalisar na neman tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa kan zargin rashin ɗa'a da nuna reni ga majalisar da umarnin kotun koli.

  15. Somaliya da Masar za su hana amincewa da Somaliland

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Somaliya da Masar sun amince su hana Somaliland samun amincewa a matakin ƙasa da ƙasa, bayan Isra’ila ta bayyana a watan Disambar 2025 cewa ta amince da ita a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yancin kai.

    Wannan yarjejeniya ta biyo bayan tattaunawar da ministocin harkokin wajen Somaliya da Masar, Abdisalam Abdi Ali da Badr Abdelatty, suka yi a taron ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmai (OIC) da aka gudanar a Jeddah ranar 10 ga Janairu.

    Ministocin biyu sun yi watsi da matakin Isra’ila, suna mai cewa matakin na ƙalubalantar iyakokin Somaliya da duniya ta amince da su.

    Kungiyar OIC, wadda ta ƙunshi ƙasashe 57 masu rinjayen Musulmi, ta gudanar da taron ne domin tattauna matakin Isra’ila da yiwuwar ɗaukar matsaya tare.

    Somaliland ta ayyana namen ƴancin kai daga Somaliya tun 1991, kuma Isra’ila ce ƙasa ta farko kuma kaɗai daga cikin mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da ta amince da ita a hukumance a watan Disambar da ya gabata.

  16. Sojoji sun ceto fasinjojin da aka yi yunƙurin sacewa kan hanyarsu zuwa Kamaru

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta na 13 Brigade sun samu nasarar ceto fasinjoji 18, ciki har da jarirai 2, daga wani jirgin ruwa da ‘yan fashin ruwa suka kama a ranar 11 ga Janairu, 2026.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.

    Rahotanni sun nuna cewa ƴan fashin ruwa wadanda suka yi amfani da ƙananan jiragen ruwa masu gudu sun kai wa jirgin wanda ke tafe daga Najeriya zuwa Kamaru hari a gaɓar tashar kamun kifi ta Kombo a kogunan Kamaru

    Sojoji sun samu kiran gaggawa kan lamarin inda suka yi saurin ɗaukar mataki suka bi ‘yan fashin abin da ya haifar da musayar wuta wanda ya sa ɗaya daga cikin jiragen ƴan fashin ya kife.

    Sakamakon haka, ‘yan fashin suka tsere zuwa cikin koguna suka bar fasinjojin inda daga bisani sojojin suka ceto su cikin ƙoshin lafiya.

    ...

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy

    Kwamandan 13 Brigade na rundunar, Brigadiya Janar PO Alimikhena, ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da kwarewarsu a aikin ceton inda ya ce; “Za mu ci gaba da tabbatar da tsaron yankunan da muke aiki da su da kuma kare ‘yan kasa daga duk wani laifi.”

    Ya kuma bukaci al’umma da su taimaka wajen bayar da bayanai masu amfani ga sojojin don yaƙi da laifuka a kogunan Cross River da kewaye inda ya jaddada cewa haɗin kai da al’umma na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro.

    ...

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy

  17. Binciken da ake yi wa Malami ba shi da alaƙa da siyasa - Shugaban EFCC

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Olanipekun Olukoyede ya mayar da martani ga masu cewa hukumar na binciken tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami ne saboda ya bar jam’iyyar APC.

    Olukoyede ya ce binciken da ake yi wa Malami ba shi da alaƙa da siyasa ko bambancin jam'iyya.

    A cikin wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin Channels, Olukoyede ya bayyana cewa binciken Malami ya fara ne tun kafin ya karbi shugabancin hukumar.

    “Tun shekarun baya da suka wuce kafin na zama shugaban hukumar aka fara binciken shi. Abin da na yi shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken cikin tsari da inganci,” in ji shi.

    Shugaban ya kuma nanata cewa ba za a iya ciyar da ƙasar gaba ba idan ana tsangwama saboda bambancin siyasa.

    “Idan muna so Najeriya ta ci gaba, dole ne mu yarda cewa wannan yaƙin cin hanci da rashawa da hukumar ke yi cikin aikinta ne kawai kuma duk sai mun amince da yaƙar cin hanci da rashawa ba tare da ɗaukar ɓangare ba, wannan shi nake so ‘yan Najeriya su fahimta su kuma yarda da mu,” Olukoyede ya ce.

    Olukoyede ya ce binciken Malami ya kasance tsawon kusan shekaru biyu da rabi, inda hukumar ke ƙoƙarin tabbatar da gaskiyar zargin da ake masa.

    Hukumar dai ta kai Malami da iyalansa kotu kan zargin halasta kuɗaɗen haramun wanda ya kai ga kai su gidan yarin Kuje da ke Abuja amma daga bisani kotun ta bayar da belinsu kan kuɗi naira miliyan 500 tare da kawo mutum biyu a matsayin waɗanda za su tsaya musu.

  18. Gas ɗin girki ya kashe amarya da ango a darensu na farko

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani ango and amaryarsa sun rasa rayukansu bayan fashewar tukunyar gas ɗin girki a wani gida da ke Islamabad, inda suka kwana bayan kammala bikin aurensu, a cewar ‘yan sanda.

    Baya ga amaryar da angon, wasu mutum shida ciki har da ‘yan uwa da baƙin bikin su ma sun mutu, yayin da sama da mutum goma suka jikkata.

    Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar Lahadi, inda fashewar ta haddasa rushewar rufin gidan tare da lalata bangon ginin.

    Jami’an agajin gaggawa sun bayyana cewa tsiyayar iskar gas ce ta cika ɗakin kafin fashewar.

    Haka kuma, gidaje uku na maƙwabta sun lalace yayin da aka ceto wasu mutane da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

    Mahaifin ango, Hanif Masih, ya ce sun mutu ne a darensu na farko lokacin da suka barci.

    A Pakistan, mutane da dama na amfani da gas wajen girki, inda ake yawan samun irin wannan mummunan hatsari sakamakon tsiyayar iskar gas.

  19. Birtaniya za ta ƙera wa Ukraine sabbin makamai masu linzami

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Birtaniya ta bayyana shirin kera wa Ukraine sababbin manyan makamai masu linzami domin taimaka mata kare kanta daga hare-haren Rasha.

    A cewar gwamnati, ana sa ran za a kammala ƙera tare da gwada makaman nan da wata 12, kuma makaman za su bai wa Ukraine damar kai hari har cikin ƙasar Rasha.

    Tun farkon yaƙin, Moscow ke kai hare-hare kan manyan biranen Ukraine ta amfani da makamai masu linzami, yayin da Kyiv ta fi dogaro da makaman da Amurka ke ba ta waɗanda kuma Washington ta takaita amfani da su iya wani takaitaccen zango.

  20. Tinubu ya isa Abu Dhabi don halartar taron makamashi

    Tinubu da sarkin Dubai

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar wani taron makon makamashi.

    Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya samu tarba daga ministan harkokin wajen ƙasar UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, da jakadan UAE a Najeriya a ƙasar, Salem Saeed Al-Shamsi.

    Shugaban Tinubu ya isa Abu Dhabi ne daga Turai, inda ya yi wani ɓangare na hutunsa ƙarshen shekara, inda ya tattauna da shugaban ƙasashen Rwanda da na Faransa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Tinubu da tawagarsa lokacin da suka isa Dubai

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Fadar shugaban Najeriyar ta ce sarkin UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci Tinubu taron, wanda shugabannin duniya da ƙwararru da ƙungiyoyin fararen hula ke tattauna batutuwan da suka shafi makamashi da yadda za a inganta shi.