Manyan ayyukan da aka zargi ƴan majalisar Najeriya da cusawa cikin kasafin 2025

Asalin hoton, BBC/Pidgin
Tun bayan fitar rahoton wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da ake kira da 'BudgIT' da ya ce ya gano wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2025, ƴan Najeriya ke ta fama mayar da martani.
Ƙungiyar ta BudgIT ta ce ta gano kwangiloli har 11,122 waɗanda za su lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la'akari da cancanta ba.
BudgIT ta ƙara da cewa an cusa irin waɗannan ayyuka ne a kasafin hukumomi da ma'aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan ma'aikatun.
Kan haka ne BBC ta fayyace jerin ayyukan guda tara da rahoton ya ce ta nan ne aka yi cushen.
Jerin manyan ayyuka tara
- Fitilun kan hanya: Rahoton ya ce an yi cushen tsabar kuɗi har naira biliyan 393.29 da sunan samar da fitilun kan titi guda 1,477 a mazaɓun ƴan majalisar wakilai da na ƴan majalisar dattawa a faɗin Najeriya.
- Birtsatse: Za a samar da rijiyoyin birtsate guda 538 a mazaɓun ƴan majalisar dattawan da na wakilai a kan kuɗi naira biliyan 114.53.
- Ayyukan masu alaƙa da fasahar sadarwar zamani: Waɗannan za su laƙume naira biliyan 505.79. Za kuma a gina guda 2,122 a mazaɓun ƴan majalisar dokokin da ke faɗn Najeriya.
- Gina/kwaskwarima ga ɗakunan taro na al'umma: Gina ko yi wa ɗakunan taro 43 kwaskwarima a wasu mazaɓun ƴan majalisar dokokin ƙasar zai laƙume kuɗi har naira biliyan 17.23.
- Gina azuzuwa/samar da littafai da horas da malamai: Wannan ma kamar yadda rahoton na BudgIT ya nuna zai lame tsabar kuɗi har naira biliyan 179.96.
- Ayyuka da suka jiɓanci sha'anin lafiya: Za a samar da abubuwa da ayyuka masu yawan 319 a kan kuɗi naira biliyan 420.09.
- Inganta rayuwar sarakunan gargajiya: Rahoton na BudgIT ya nuna cewa ɗaya daga cikin cushen da ƴan majalisar dokokin Najeriyar suka yi wa kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 shi ne sanya tsabar kuɗi har naira biliyan 6.74.
- Gina da yi wa tituna kwaskwarima: Za a gina tituna 1380 a kan tsabar kuɗi har naira tiriliyan ɗaya da biliyan 44 a mazaɓun ƴan majalisar dokokin ƙasar.
- Sayen ababan hawa ga jami'an tsaro: Bisa rahoton na BudgIT, ƴan majalisar sun yi cushen naira biliyan 11.7 domin sayen ababan hawa ga jami'an tsaro.
Shawarar da BudgIT ta bayar

Asalin hoton, ASO ROCK
Rahoton ƙungiyar mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da ake kira da 'BudgIT', ya ce duk da cewa tsarin mulkin Najeriya ya tanadi tabbatar da adalci to amma ba a aiwatar da su.
"Ba a kama jami'an gwamnati kan laifukan rashawa da cin hanci da almubazaranci abin da ke janyo matsaloli a tsarin aikin gwamnati.
"Ya kamata hukumomin da ke hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa kamar EFCC da ICPC su rinƙa hukunta masu rashawa da cin hanci da almubazzaranci da ke alaƙa da kasafin kuɗi." In ji rahoton na BudgIT.
Martanin majalisar dattawa
Majalisar dattawa ta bakin shugaban kwamitin majalisar kan watsa labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa zargin ba shi da tushe ballantana makama, inda ya ƙara da cewa sai da aka tantance ƙudirin kasafin kuɗin na 2025 sannan aka amince da shi bayan duba na tsanaki ga alƙaluman da ɓangaren zartarwa ya miƙa musu.
"Ƙudirin kasafin kuɗin na 2025 da ɓangaren zartaswa ya gabatar wanda kuma majalisun dokokin suka yi wa duban tsanaki kafin su amince da shi bisa dogaro haƙiƙanin yawan kuɗin da ɓangaren zartaswar ya gabatar mana." In ji Adaramodu.
Ya kuma ƙara da cewa zarge-zargen na yin cushe na siyasa ne.
"Muna shawartar duk waɗanda ƴan siyasa ke amfani da su da su tattauna batutuwa na gaskiya maimakon ƙage irin na siyasa." In ji ɗan majalisar.











