Me ya sa kasafin kuɗin Najeriya ke dogaro da bashi?

Asalin hoton, Tinubu Facebook
Ana ci gaba da cecekuce kan bukatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika wa majalisar dokokin ƙasar, ta amince wa ya karbo wani sabon bashi na dala biliyan biyu da miliyan dari biyu, wato kusan naira tiriliyan biyu daga waje, don samar da kudin aiwatar da wani bangare na giɓin kasafin kudin wannan shekara ta 2024.
Masu sukar lamarin dai suna ganin ƙaruwar bashin da kasar ke ciwowa daga waje dai wata babbar barazana ce ga gudanar da tattalin arziki yadda ya kamata.
Akwai damuwar da wasu ke ta bayyanawa game da yadda kasafin kudin badi shi ma zai dogara matuka kan bashi.
Tun da bukatar karbo sabon bashin karasa aiwatar da kasafin kudin Najeriyar na bana ta taso dai, ake ta bayyana damuwa da ganin baiken abin.
Kodayake Dokta Murtala AbdulLahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziki na jami'ar Umaru Musa Ƴar-Adua da ke Katsina, yana ganin har yanzu yawan irin wannan bashi da kasar ke ciwowa daga waje, bai kai ga munana ba.
"Har yanzu bashin da Najeriya ke karɓa bai yi muni ba idan aka ɗora shi kan GDP, masana na ganin cewa sai bashi ya kai kashi biyu cikin uku na GDPn ƙasar ne zai zama mai ta'annati."
Me ya sa ake cecekuce?
Buƙatar karbo rancen domin cike giɓin kasafin kuɗin Najeriyar na bana ya haifar cecekuce da saɓanin ra'ayi
Masanin tattalin arziki Dokta Murtala Abdullahi Kwara na ganin al'amarin bashi ga tattalin arziƙi ba gaba daya ne yake da muni ba, sai dai me aka yi da bashin shi ne abun tambaya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yawancin kuɗin da ake ciwo wa bashi a Najeriya ana amfani da su ne wajen tafiyar da gwamnati, wadanda suke zuwa aljihun wasu mutane shafaffu da mai, wadanda suke riƙe da madafun iko," in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa ya kamata duk bashin da za a ciwo a yi amfani da shi wajen assasa sana'a ko kuma inganta masana'antu da za su fitar da mutane daga talauci da samar wa mutane ayyukan yi.
Wasu masanan na ganin idan aka shiga irin halin da Najeriya ta tsinci kanta a fannin tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta waiwayi cikin gida don neman mafita, a madadin ƙara ciwo bashin.
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta ce batun ba shi abu ne da ake yi kuma yana bisa tsari, kuma 'an samu sauƙin ciwo bashi a ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu.
Malam Abdul'Azeez Abdul'Azeez, mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen tafiyar da gwamnati, musamman ayyuka, "Misali bunƙasa aikin noma, da tituna."
Duk wadannan bayanai dai, har yanzu wata fargabar nan ta yi likimo, cewa bashin da Najeriyar za ta ciwo daga waje, don cike giɓin kasasfin kudin badi na iya nunka adadin wanda aka ciwo a bana.











