Ko shinkafar da gwamnati za ta raba wa talakawa za ta rage raɗaɗin yunwa a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ɗin wannan mako ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar cewa ta bai wa gwamnoni tirelolin shinkafa waɗanda za su raba wa al'umma domin rage raɗaɗin yunwa.
A lokacin da ya yi bayani bayan taron ɓangarren zartaswa na gwamnatin tarayya, ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya ce an bai wa kowace jiha haɗi da Abuja tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.
Ya ce kowace tirela tana ɗauke da buhun shinkafa 1,200 kg25 da aka ba gwamnonin jihohi a wani mataki na rage wa talakawa raɗaɗin ƙarancin abinci da tsadarsa da ake fuskanta a ƙasar.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabuƙata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Hakan na nufin kowace jiha, da kuma babban birnin tarayya za ta samu jimillar buhunan shinkafa masu nauyin 25kg guda 24,000.
Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake alaƙantawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.
Shin wane tasiri wannan taimako zai yi ga halin da mutanen Najeriya ke ciki?
Halin da ƴan Najeriya ke ciki

Asalin hoton, Getty Images
A alƙaluman da ta fitar na baya-bayan nan, Hukumar abinci da aikin gona ta duniya ta ce kusan mutum miliyan 32 ne ke cikin matsananciyar yunwa a Najeriya.
Alƙaluma da hasashen Bankin Duniya sun nuna cewa kimanin kashi 40.7 cikin ɗari na al'ummar Najeriya na cikin ƙangin talauci a shekarar 2024.
Wannan na nufin kusan kimanin mutum miliyan 100 ke nan a Najeriya ke cikin ƙangin talauci a ƙasar wadda ke da yawan al'umma sama da miliyan 200.
Matsin tattalin arziƙi da tashin farashin kayan masarufi na ci gaba da ingiza al'umma cikin talauci.
Tashin farashin kayan masarufi ya kai ƙololuwa a bara, inda ya kai kashi 24.7 cikin ɗari.
Ya zuwa watan Mayun 2024 tashin farashin ya kai kashi 34.19, in ji Hukumar ƙididdiga ta Najeriya.
Wannan na ƙara ƙazancewa sanadiyyar cire tallafin man fetur da karyewar darajar naira da kuma sabbin manufofin ɓangaren kuɗi da gwamnatin ƙasar ta samar.
Shinkafa buhu 24,000 ga kowace jiha
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin tattalin arziƙi a Najeriya, Shu'aibu Idris Mikati ya ce a ƙasa wadda kusan kimanin mutum miliyan 100 ke cikin talauci, zai yi wahala wannan mataki ya yi tasiri.
Haka nan ya bayyana cewa bin wannan hanya wajen taimaka wa al'umma abu ne da bai dace ba domin zai iya haifar da yamutsi.
A cewar sa, "mu ɗauki a misali jihar Legas wadda ke da mutane kusan miliyan 22, kusan miliyan bakwai na cikin yunwa, kuma an ce a raba tirela 20 ta shinkafa, wannan kusan an ce a yi yamutsi ke nan.
"Jihohi kamar Zamfara da Yobe kusan kashi 60 cikin ɗari na mazauna jihar na cikin talauci ne saboda haka wannan zai iya haifar da rikici."
A baya dai an ga yadda rabon abinci a Najeriya ya haifar da ruɗani, lamarin da a wasu lokuta kan haifar da raunata mutane ko ma rasa rai.
Ko a watannin da suka gabata mutane sun riƙa tare motoci masu dakon abinci da rumbunan ajiye kayan abinci na gwamnati da na ƴan kasuwa ana wawushe kaya.
Haka nan masanin tattalin arziƙin ya ce wata matsalar ita ce rashin gaskiya tsakanin al'umma.
A cewarsa: "Da zaran ka ba wasu mutane wani abu su raba wa wasu, kusan fiye da rabi za ka ga sun yi sama-da-faɗi da kayan ne.
"Wasu za su raba wa na kusa da su ne wasu kuma za su sayar ne su sanya kuɗin cikin aljihunsu, a maimakon bai wa waɗanda ke da buƙata."
Raba abinci ne mafita?

Asalin hoton, Getty Images
Masanin tattalin arziƙi kuma malami a jami'ar Nile da ke Abuja, Ahmed Adamu ya ce idan har Najeriya na son ta fitar da al'ummarta daga matsi, to ya kamata ne ta riƙa duba ɓangarori biyu a maimakon mayar da ƙarfi kan ɓangare ɗaya.
Ɓangarorin biyu su ne:
- Farfaɗo da tattalin arziƙi
- Huce raɗaɗi na wucin-gadi
Dakta Ahmed Adamu ya ce abin da gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali a kansa yanzu shi ne tallafin huce raɗaɗi na wucin-gadi.
Ya ce raba abinci da tallafin kuɗi wani abu ne da ba mai ɗorewa ba "saboda idan ka ba mutum buhun shinkafa ɗaya, bayan wata ɗaya ya cinye, zai jira ka ne ka ƙara ba shi.'
"Kuɗin da ake bai wa mutane ta hanyar tallafi ko bayar da abinci, kamata ya yi a karkata akalarsu zuwa ɓangaren farfaɗo da tattalin arziki," in ji malamin jami'ar.
A cewar dakta Adamu halin da ake ciki a Najeriya yanzu shi ne mabuƙata sun yi yawa, sannan kuma hanyoyin samar da abubuwan buƙata na raguwa.
Saboda abin da ake buƙata shi ne a faɗaɗa hanyoyin samar da abubuwan buƙata ta yadda za su wadatu, wanda hakan ne zai sauko da farashin kaya sannan ya samar da aiki ga al'umma.
Tun bayan da ta cire tallafin man fetur, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da tallafi a ɓangarori da dama waɗanda take ganin za su rage wa talaka wahala, sai dai har yanzu tamkar matakan ba su aiki.
Ko a cikin watan da ya gabata, shugaban Najeriya ya sanar da shirin gwamnati na janye haraji kan wasu nau'ukan kayan abinci da ake shiga da su ƙasar.
Haka nan shugaban ya ce zai bayar da tallafin kuɗi ga wasu iyalai masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.











