Yadda marasa lafiya ke fuskantar tsadar magani a Najeriya

Rage darajar kuɗi and hawa da saukar sa a Najeriya ya janyo tashin farashin magunguna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashin tabbas da rage darajar kuɗi a Najeriya ya sa farashin magunguna sun yi gauron zabi, abin da ya sa marasa lafiya da yawa ba sa iya daukar nauyin kulawarsu
    • Marubuci, Makuochi Okafor & Chigozie Ohaka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lagos, Nigeria

Tashin farashin muhimman magunguna a Najeriya ya sanya mutane da yawa ba sa iya saye, yayin da suke fama da tsadar rayuwa.

Farashin wasu magungunan ya ruɓanya ko ya ninka sau uku a ƴan watannin da suka wuce, lamarin da ya sa ba a iya sayen su a ƙasar, wadda fiye da kashi 60 cikin ɗari na mutanenta talakawa ne da ke rayuwa kan ƙasa da dala biyu a rana.

Ƴan Najeriya na fuskantar hauhawar farashin kaya da ta kai kashi 33.2 cikin ɗari, mataki mafi ƙololuwan da aka taɓa gani a kusan shekara talatin. Cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi a shekarar da ta gabata ya taimaka wajen tashin farashin kaya a ƙasar.

Ministan lafiya na ƙasar, Muhammed Ali Pate ya shaida wa BBC cewa farashin magunguna na da alaƙa da hawa da saukar farashin kuɗaɗen musaya, abin da ya ƙara tsadar shigo da magani ƙasar.

Haka kuma ministan ya yi nuni da rashin yawan mutanen da suka shiga tsarin inshorar kiwon lafiya na ƙasa, hakan ya sa da yawa ke biyan kuɗin magani, kuma hakan ya zama wani ƙarin nauyi a kan farashin da ke ƙaruwa.

Gwamnatin ta bayyana wasu matakan da ta ce za ta ɗauka domin magance matsalar tsadar magani. A baya-bayan nan ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ɗauki alƙawarin sauƙaƙa wa kamfanonin sarrafa magunguna na cikin gida wajen shigo da abubuwan da ake buƙata wajen haɗa magunguna da kuma kayan aiki domin su fara sarrafa magani a cikin ƙasar.

Sai dai, ba a fayyace nan da wane lokaci za a fara aiwatar da wannan shiri ba.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) kashi 95 cikin dari na duka magungunan da ake amfani da su a Afrika shigo da su ake yi daga waje.

Nahiyar na samar da kashi uku ne kawai cikin ɗari na magungunan da ake yi a duniya, Kenya, Najeriya da kuma Afrika ta Kudu ke da kamfanonin sarrafa magunguna masu ɗan dama.

Annobar Covid-19 ta ƙara fito da ɓuƙatar sarrafa magunguna na cikin gida.

A watan Fabairu, shugabannin ƙasashen Afrika ƙarƙashin jagorancin cibiyar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙungiyar tarayyar Afrika, (CDC) suka amince da wani shiri na haɗa kai waje guda su sayi magunguna da rigakafi tare domin samun su a farashi mai gwaɓi.

Shirin na kuma fatan bunƙasa sarrafa magunguna na cikin gida, yayin da ƙasa da kashi ɗaya ne kawai na rigakafin ceton rai ne ake yi a nahiyar. Shirin na fatan ganin an sarrafa kashi 60 cikin dari na magunguna a nahiyar nan da shekarar 2040.

Rhoda Husseini mace ce da ke kula wa da ƴaƴanta huɗu kuma ba za ta iya sayen maganin cutar Asma ba, abin da yasa ta koma yin na gargajiya.
Bayanan hoto, Rhoda Husseini mace ce da ke kula wa da ƴaƴanta huɗu kuma ba za ta iya sayen maganin cutar Asma ba, abin da yasa ta koma yin na gargajiya.

'Ina amfani da magungunan gargajiya'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu ƴan Najeriya kamar Jane Aibangbe, mai shekaru 29 da ke zaune a Legas da ke buƙatar magani akai-akai na fuskantar barazana saboda tashin farashin gwauron zabin da magunguna suka yi.

Jane na fama da cutar da ta shafi tsarin garkuwar jiki (systemic lupus erythematosus).

Kuɗin da take kashewa wajen samun kulawar likita ya ƙaru daga naira 21,000 a watanni uku na ƙarshen shekarar da ta wuce, zuwa naira 35,000 a watan Fabairun 2024.

“Sam ban ji dadi ba, amma me zan iya yi?”

Jane da ke fafutukar sayen magani tana tambaya.

Ita ma Sarah Erekosima mai shekara 28 ta kwashe shekaru tana fama da cutar Asma.

ƙarin kuɗin magani ya tilasta mata sauya rayuwarta domin tabbatar da cewa ba ta samu matsalar tayar da cutar ba ta yadda dole sai ta nemi magani.

“Dole nake shan ruwan ɗumi maimakon na sanyi duk da tsananin zafin da ake fama da shi a Legas,” tana magana kan kauce wa tayar da cutar ta ta asma

Kuɗaɗen da take kashewa wajen sayen magani sun ƙaru daga naira 9,000 a watan Mayun 2023 zuwa sama da naira 67,000 a watan Maris 2024.

“Haƙiƙa lafiyata ce kuma ina so na yi tsawon rai ko? amma akwai kashe kuɗi,” in ji ta.

Rhoda Husseini daga garin Wamba, wadda ita ma take fama da matsalar cutar asma, ta ce ba ta iya sayen abin shaƙawa na Ventolin wanda yakan sa ta ji sauƙi nan da nan.

“Ba zan iya sayen abin shaƙawar ba, su ma ba a samun su a wasu lokutan. A yanzu ina amfani ne da magungunan gargajiya” ta ce, duk da cewa babu wata shaidar da ke nuna cewa suna aiki.

Uche Tralagba, wata likita ce da ke zaune a Legas ta bayyana damuwarta kan yadda tashin farashin magunguna ke shafar marasa lafiya.

“Wasu marasa lafiyar suna sane suke ƙin shan magunguna kamar yadda ya kamata saboda magani ya daɗe suna amfani da shi. ” a cewar ta.

“Akwai wasu ma da kwatakwata ba sa shan maganin saboda ba za su iya saye ba. Kuma hakan ya ta'azzara yanayin da suke ciki, wasu ya kai ga ajalinsu.”

A cewar Dr Tralagba, matsin tattalin arzikin da ake ciki ya tilasta wa wasu marasa lafiyan sadaukar da lafiyarsu.

“Wasu sun kasa daukar hutu daga aikin da suke yi, duk da cewa lafiyarsu ba za ta ɗauka ba, kuma an ba su shawarar su huta.

Sun ci gaba da aiki saboda su samu kuɗin sayen magani, suna hana jikinsu hutun da yake buƙata domin su murmure da wuri,” In ji ta.

Cyril Usifoh, shugaban ƙungiyar masu kamfanonin sarrafa magunguna na Najeriya, ya ce gwamnati za ta iya inganta yanayin da ake ciki idan ta ɗage biyan haraji ga dillalai tare da rage haraji a kan magunguna.

Haka kuma a cewarsa dokokin gwamnati a kan farashin magunguna za su iya taimaka wa masu sarrafa su na cikin gida, abin da zai iya rage shigo da su, kuma marasa lafiya su samu sauƙin saye.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana inganta inshorar lafiya

Asalin hoton, Getty Images

Me gwamnati ke yi?

A farkon wannan shekarar, ministan lafiya Muhammed Pate ya sanar da cewa shugaba Bola Tinubu na shirin sanya hannu kan wata doka wadda za ta rage tsadar magunguna. Sai dai babu cikakken bayani game da shirin.

Ministan ya kuma sanar da fitar da naira biliyan 1.3 ($72 miliyan) domin zubawa a muhimmin asusun kula da lafiya, wanda shi zai samar da kuɗaɗe ga tsarin inshorar lafiya na ƙasa domin ƴan ƙasar marasa galihu.

A shekarar 1999 ne ƙasar ta kaddamar da shirin inshora na ƙasa domin rage kashe kuɗi a ɓangaren jama'a.

Inda ya fara aiki shekara shida bayan nan, sai dai ya shafi wasu ƙalilan ne na al'ummar ƙasar, mafiya yawan su ma'aikatan gwamnati.

Ƴan ƙasar da yawa, musamman waɗanda ba sa aikin gwamnati da wasu hukumomi da kuma mazauna yankunan karkara har yanzu ba su da inshorar, sun dogara ne wajen biya daga aljihunsu.

A shekarar 2022 ne ƙasar ta zartar da ƙudurin dokar kafa hukumar sanya ido kan inshorar lafiya, dokar da ke tilasta wa masu harkokin kasuwancin da ke da ma'aikata biyar zuwa sama biyan inshorar lafiyarsu. Sai dai masana sun ce babu niyya mai ƙarfi daga masu riƙe da muƙaman siyasa kuma babu faɗakarwa sosai na aiwatar da shirin cikin nasara.