Hanyoyi biyar da ƴan Najeriya ke bi wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akasarin ƴan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa yayin da hauhawar farashi ke ƙaruwar da ba a taɓa ganin irin ta ba
    • Marubuci, Yusuf Akinpelu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Wakilin BBC Lagos

Yayin da farashin kaya ya yi tashin da ba a taɓa gani ba a cikin kusan shekara talatin a watan Janairu, kusan rabin al'ummar Najeriya na rayuwa cikin talauci, suna rayuwa kan ƙasa da dala ɗaya duk rana. Ba sa iya sayen muhimman abubuwan tafiyar da rayuwarsu.

Matakin gwamnati na kawo ƙarshen bayar da tallafin man fetur tare da karyewar darajar naira cikin wata goma sha biyu ya daɗa ingiza farashin kayayyaki sama. Lamarin na bugun ƴan Najeriya da dama abin da kuma ya haddasa zanga-zangar nuna fushi.

Babban bankin Najeriya a baya-bayan nan ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100 a ƙoƙarin magance hauhawar farashin kayayyaki. Sai dai yayin da kuɗin ruwan ya yi ƙasa da hauhawar farashin kayayyaki, ƙimar ajiyar kuɗi na raguwa bayan shekara ɗaya.

Ya ƴan Najeriya suke fama da halin matsin? Ga wasu dabaru da suka ɓullo da su - daga dabarun sayayya zuwa hanyoyin ajiya.

Tsarin biya yanzu, biya daki-daki

Yayin da hauhawar farashi ke ƙara tashi, farashin kayayyaki na iya ninkawa sau biyu ko uku cikin ƴan kwanaki ko makonni. Idan mutum zai duba yiwuwar sayen kayayyaki na musamman ko ma kayayyakin yau da kullum, masu sayen kaya na tsintar kansu a wani yanayi na tsaka mai wuya: saya yanzu ko kuma biyan kuɗi mai yawa daga baya.

Raguwar sayen kayayyaki na nufin ba kowa ne ke da kuɗin tanadin da zai dogara a kai ba.

Abike Jaji, wata mai sayar da kayan sawa ce a jihar Legas, ta zaɓi tsarin sayi yanzu ka biya daga baya da wani mai sayar da kayan girki da tukwane a unguwarsu ya yi mata.

Matar mai shekara 60 ta ce da farashin tukwanenta da sauran kayan girki sun kusa ninkawa da a ce babu tsarin biya daga baya mara kuɗin ruwa.

"Na sayi waɗannan tukwanen a Disamba kuma ban jima da kammala biyan kuɗinsu ba a watan Fabarairu," in ji ta.

"Mai kayan yanzu yana karɓar naira dubu ɗari biyu da hamsin ga irin setin tukwanen, waɗanda na saya a kan naira 165,000 a cikin wata uku. Da a ce babu zaɓin biya daki-daki, da sai na biya fiye da haka."

Sayayya da yawa

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cire tallafin mai da gwamnatin najeriya ta yi ya dagula harkokin tattalin arziki ga ƴan Najeriya da dama

Ga waɗanda suke da damar samun rarar kuɗi daga albashinsu a ƙarshen wata, yin tanadi a kuɗin naira babu auki. Hauhawar farashi na ƙara karya darajar kuɗin a don haka babu wani amfani ka sayi kayayyaki da yawa a lokaci guda.

Wakeelah Lawal-Tijani, wata ɗaliba a cibiyar karatu ta gwamnatin tarayya tana sayen kaya ne da yawa.

"Idan akwai abin da nake buƙata, kawai ina saye. Ba na jiran sai na tabbatar da farashin saboda farashin kayayyaki na ƙaruwa kowane minti," in ji ta.

Tana girki tare da alkinta kayan abinci masu saurin lalacewa a firji sannan tana ajiyar waɗanda suke daɗewa ba su lalace ba a wuri mai sanyi da ke gidanta har sai lokacin da take bukatar su.

"Game da nama ko kaza, misali, ina tafasa su ko na soya sama-sama sannan na sa cikin leda na kuma ajiye a cikin wurin ƙanƙara. Soya abu sama-sama na taimakawa wajen takaita amfani da mai."

Rage yawan kashe kuɗi

Sai dai ba kowa ba ne ke iya sayen abu da yawa. A don haka sai su rage kashe kuɗi sannan su yi watsi da duk wani abu da ya zama kamar nishaɗi.

Mutum uku sun faɗa wa BBC cewa a yanzu suna sayen abu mai sauƙin farashi, sun daina cin abinci a waje sannan sun daina zuwa wuraren casu da watayawa. Suna haɗuwa a mota guda a maimakon yin tafiya daban-daban sannan wani lokacin suna taka sayyadarsu a maimakon shiga motar haya.

Wani mutum da BBC ta yi magana da shi ya ce a yanzu yana zuwa tarukan aure da bikin zagayowar ranar haihuwa domin kawai samun abinci a kyauta. Wata kuma ta ce ba kullum take cin abinci ba.

Ibrahim Babangida, wani mai bincike a Katsina, ya ce “na daina amfani da motata har sai ya zama dole".

Ya ce: "Na daina yawan zuwa wuraren cin abinci da shan askirim tare da mai ɗakina kusan na fiye da wata biyu. A karon farko tun Disamban 2019, ban sabunta kuɗin kallon DStv ba."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farashin kayayyaki na karuwa yayin da hauhawar farashi ke tashin gwauron zaɓo a Najeriya

Shiga tsarin adashe da adashen gata

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga wasu mutane da suka san za su buƙaci ƙarin kuɗi na yin wani abu a gaba kamar bikin aure da kuɗin makaranta ko kuɗin magani, suna shiga tsarin adashe.

Mambobin ƙungiyar adashen gata suna tabbatar da ƙudurinsu ta hanyar yin zubi a kai a kai na wani lokaci da aka tsayar. Bayan sun kammala zubin, suna iya neman bashi mara kuɗin ruwa da dole su biya cikin watannin da aka amince.

Waɗanda suka karɓi bashi suna biyan wasu kuɗaɗe da ake amfani da su wajen tafiyar da ƙungiyar amma kuɗin bai kai tsarin bashin banki ba.

Ta irin haka Halima Ibrahim da mijinta suke bayar da gudummawa wajen tafiyar da sana'arsu ta kayan gine-gine tare da aika matasan yaransu mata makaranta.

"Wannan ne karon farko da muka karɓi irin wannan bashi. Na ƙarfafa wa mijina gwiwar mu karɓa kuma ya taimaka mana wajen biyan buƙatu tare da sayen filaye," in ji ta.

"Mun karɓi rancen naira miliyan biyu kuma za mu biya cikin wata 10," kamar yadda ta bayyana.

Waɗanda suka kafa ƙungiyoyin ajiyar kuɗi suna haɗuwa wajen saka kuɗin da aka ƙayyade kowane wata. Wani a ƙungiyar na ɗaukan duka kuɗin da aka zuba a kowane wata kuma ana juyawa ta yadda kowa a ƙungiyar zai kwashi zubin da aka yi.

Irin wannan tsarin abu ne da aka fi gani tsakanin ma'aikata da ƴan kasuwa ko al'ummar wani yanki, saboda yana taimakawa wajen tsuke bakin aljihu da biyan bashi da kuma iya sayen abu babba lokaci ɗaya.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikata na haɗewa a karƙashi ƙungiya domin yin ajiyar kuɗi

Amfani da wasu hanyoyi na gargajiya

A watan Fabarairu, farashin kilo daya na gas din girki a Najeriya ya kai naira 1,300 daga naira 800 a farkon wannan shekarar. Farashin ya kusan nunki biyu cikin wata goma sha biyu da suka gabata.

Wasu mutane sun koma amfani da itace ko gawayi wajen yin girki. Shafukan sada zumunta a Najeriya cike suke da tallace-tallace da ke neman mutane su sayi rishon girki na gawayi da itace.

Haka nan, mutane na ƙoƙarin kauce wa kashe kuɗi kan ruwa. A wani gari da ke jihar Ogun, a wajen Legas, masu sayar da ruwa suna cika gorar ruwa da ruwan famfo yayin da farashin ruwan gora ya ninka sau biyu cikin shekara ɗaya.

Yayin da a wasu yankunan Benin da ke Kudancin Najeriya, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa masu sayar da ruwan sun koma sayar da ruwan sanyi na leda. Ruwan famfo ne mai sanyi da ake zubawa a leda wanda ya yi fice a shekarun 2000 - ya fi sauƙin kuɗi a kan ruwan gora sai dai ba a tsaftace yake ba.