Hanyoyin da Najeriya da Amurka za su iya bi don magance matsalar tsaro

Bola Tinubu da Donald Trump

Asalin hoton, Bola Tinubu da Donald Trump

Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da ake ci gaba da takfa muhawara kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump ta shiga Najeriya domin yaƙi da ta'addanci a, hankali ya fara komawa ne kan hanyoyin da Amurka za ta iya taimakon Najeriya wajen samun wannan nasara.

A makon jiya ne dai Najeriya ta tura tawagar manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar zuwa Amurka domin tattaunawa da takwarorinta na can domin lalulo hanyoyin da za a iya magance matsalolin tsaron da suka yi wa Najeriya ɗaurin gwarmai.

Gwamnatin ta sha nanata cewa batun kisan kiyashi ga Kiristoci a ƙasar ƙanzon-kurege wanda ba shi da tushe ballantana makama, inda ta ce lallai ƙasar na fama da matsalar tsaro, amma kashe-kashen da ake yi ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilar mutum.

Sai dai wani abu da ya ɗauki hankalin mutane shi ne yadda ƙasar ta rikice a cikin kwana kaɗan bayan barazanar ta Trump, inda aka sace ɗalibai a jihohi uku na ƙasar, sannan aka kashe wani hafsan tsaron, tare da kashe wasu manoma a wasu jihohin daban.

Barazanar ta ƙara fitowa fili ne bayan wasu jihohin sun sanar da rufe wasu makarantunsu na gwamnati, inda suka umarci ɗaliban su koma gida har sai an samu tabbacin tsaro.

Abubuwan da Najeriya za ta yi

Domin duba yiwuwar aiki tare tsakanin Najeriya da Amurka, BBC ta tuntuɓi Dokta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security & Intelligence Limited, inda ya ce dama can akwai haɗakar tsaro ƙasashen biyu, inda ya ce sai dai a inganta tsarin.

"Ba sabon abu ba ne. Amma in dai da gaske sun shirya inganta tsarin, wanda dama tun a shekarun baya akwai to akwai aiki babba."

Amma masanin tsaron ya ce matuƙar ana so a yi aikin a tare, kuma a samu nasara, to lallai akwai wasu abubuwan da yake ganin dole sai Najeriya ta yi, "saboda yanzu nauyi a kanta yake musamman bayan barazanar Trump.

''Inganta abubuwan ne zai sa duk ƙasar da za ta taimaka mata ta samu ƙarfin gwiwa."

  • Tabbatar da kare mata sirri: "Ƙasar na fargabar kada bayananta na sirri su faɗa hannun abokan adawarta."
  • Daƙile bara-gurbi a cikin jami'an tsaro: "Su kansu jami'an tsaron sun sha bayyana cewa akwai baragurbi a cikinsu, har ma akwai sayar wa ƴanbindiga makamai."
  • Inganta hanyoyin sadarwa: "Hanyar sadarwa ta salula da ma Whatsapp ba hanyoyi ba ne masu inganci wajen isar da bayanan sirri. Duk saƙonnin da aka fitar ana iya bibiya kuma a naɗe su."
  • Tabbacin amfani a makamai: "Dole sai Najeriya ta inganta kare haƙƙin ɗana'adam saboda ƙasashen waje na tsoro a yi amfani da makamansu a muzguna wa ƴan ƙasa, sannan a riƙa cewa misali an yi amfani da makaman Amurka wajen cutar da al'umma."

Kabiru Adamu ya ce taimakawa da bayanan sirri na buƙatar samun tabbacin sirri da ma cewa bayanan ba za su ƙare a hannun abokan adawa ba.

"Kuma abin takaici akwai rauni a wannan ɓangaren na kare sirri a Najeriya."

jigbe sansani a Najeriya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai a game da batun yiwuwar jigbe sojojin Amurka a Najeriya, lamarin da wasu ƴan ƙasar suke bayyana fargabarsu, Kabiru Adamu ya ce lura da muradun Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a zahiri, za a iya cewa akwai yiwuwar su buƙaci kafa sansani a Najeriya.

"Yanzu haka Amurka na gina ofishin jakadanci mafi girma a yankin Afirka ta Yamma a Legas. Wannan zai nuna maka cewa akwai wani buri da suke da shi ko da kuwa a can gaba ne," in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai gasa mai zafi na tattalin arziki da ke tsakanin Amurka da China, musamman kan ma'adinan ƙasa masu muhimmanci.

"Waɗannan ma'adinan na 'rare earth minerals' da ake haɗa batura da ake amfani da su a motocin da ba sa amfani da fetur da sauran kayayyakin lantarki sun ƙara zafafa gasar tattalin arziki tsakanin Amurka da China, kuma akwai waɗannan ma'adinan jibge a Najeriya''.

''Sannan kuma yanzu Amurka ba ta da sansani a Afirka. A baya suna da shi a Nijar da Kamaru amma sun rufe."

Tsaka mai wuya

Wani abu da yake ɗaukar hankali a game da wannan tata-ɓurzar da ake yi ita ce fargabar ƴan Najeriya ta kasancewar ƙasarsu da zama filin daga na bayan fage tsakanin Amurka da China.

A game da wannan ne Kabiru Adamu ya ce ai an riga an makara, domin a cewarsa, Najeriya ta riga ta shiga tsakiya.

"Najeriya ta riga ta makara, har ta shiga tsakiyar gasar tattalin arziki tsakanin Amurka da China, kuma za su iya amfani da Najeriya wajen yaƙin bayan fage. Daga ganin irin labaran ƙarya da ake yaɗawa za ka san an fara wannan yaƙin na bayan fage."

Ya ce ya kamata Najeriya ta tsaya ta tantance muradunta, ta san abubuwan da take buƙata daga kowace ƙasa kafin ta fara mu'amala da ita.

"Amma kuskure ne ba mu ɗinke kanmu ba a cikin gida ba, sannan mu fita waje muna neman taimako''.

''Mu fara daga gida, sai mu tantance irin abin da muke so daga ƙasashen waje. Ya kamata a ce muna abin da muke buƙata daga taron BRICS da G20 da ma abubuwan da muke so daga Amurka da China ɗin."

Ya ce tsarawa da tantance muradu na taimakawa tare da sauƙawa wajen ƙulla alaƙa da ƙasashen waje, wanda masanin na tsaro ya ce har yanzu Najeriya ba ta yi ba.

"Har yanzu ma wannan gwamnatin ba ta da jakadu a ƙasashen waje. Don haka dole ne gwamnatin Najeriya ta gyara kanta, sai ta fuskanci waje, amma maganar gaskiya Najeriya ta riga ta shiga tsakanin gasar tattalin arziki tsakanin Amurka da China kan abubuwan da suke buƙata a Najeriya da ma Afirka."

China za ta iya hana ruwa gudu?

A game da fargabar da wasu ke yi ta gudun ƙara ta'azzarar rikice-rikicen da Najeriya ke fama da su idan Amurka ta shigo saboda alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin ƙasar da China, Kabiru Adamu ya ce zai yi wahala sojojin Amurka su haifa wa Najeriya da ɗa mai ido.

"Ai China ba za ta bari ba, kuma ga shi Najeriya ta karɓi basuka a hannunta, har basukan ma sun fara shaƙe ta''.

''Sannan kuma ita ce take riƙe da hanyoyin sadarwar Najeriya, kuma bashi aka karɓa wajenta ta gina, misali hanyar sadarwa ta 5G," in ji shi.

Ya ƙara da cewa Amurka da China ba sa jituwa a wannan ɓangaren, "idan Amurka tana waje, Amurka ba za ta je ba.

Don haka idan Amurka ta shiga Najeriya, dole za a samu matsala. Sai dai kawai Najeriya ta shirya fuskantar matsalar, misali idan za ta ba Amurka dama, to ta yaya za ta biya China bashinta?"