Talallafi biyar da Amurka ke bai wa Najeriya

...

Asalin hoton, Bola Tinubu da Donald Trump

Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da ake tattaunawa kan barazanar ɗaukar matakin soji a Najeriya da shugaban Amurka Donald Trump ya yi domin hana abin ya kira kisan Kiristoci da ake yi, akwai sauran barazana da shugaban ya yi da ya haɗa da janye tallafin da Amura ke bai wa Najeriya.

Tallafin Amurka dai ya shafi rayuwar talakawan Najeriya kai tsaye.

BBC ta tuntuɓi farfesa Abdullahi Shehu, tsohon jakadan Najeriya a ƙasar Rasha dangane da tallafin da Najeriya ke amfana daga Amurka.

Farfesa Abdullahi Shehu ya ce akwai tallafi daki-daki wanda Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa ciki har da Najeriya kuma ba wai tallafi ne da babu sharaɗi ba, akwai ƙa'idoji da manufofin Amurka a bayan tallafin.

Ya ƙara da cewa tallafin Amurka ga ƙasashe masu tasowa na zuwa ne ta manyan hukumomi kamar hukumar raya ƙasashe ta USAID wadda ke ba da tallafi ta hanyoyi guda biyar ga Najeriya da ya lissafa kamar haka;

Tallafin ingata kiwon lafiya

Tsohon jakadan ya ce, Amurka na zuba kuɗade wajen yaki da cututtuka kamar HIV/AIDS, TB, Polio da kuma kula da lafiyar mata da yara.

Shirye-shirye kamar na USAID sun shiga asibitoci da cibiyoyin lafiya musamman a yankunan da gwamnati ba ta iya kai wa sosai.

To sai dai a yanzu haka yanayin tallafin ya sauya tun bayan da Amurkar ta sanar da rushe hukumar ta USAID.

Tallafin ilimi

Abdullahi Shehu ya ce wannan ya haɗa da samar da kayan karatu, horar da malamai, gyara makarantu, da samar da karatu kyauta ga ɗalibai masu ƙaramin galihu kuma wannan shi ma a ƙarƙAshin hukumar USAID ne.

Tallafin jin ƙai da taimakon gaggawa

A lokacin bala'i ko rikici, Amurka na aikawa da abinci da magunguna da tantuna da kuɗaɗe don ceto rayuka da bai wa mutane kariya duk a ƙarƙashin hukumar USAID.

Tallafin bunƙasa tattalin arziki da noma

USAID na da shirye-shirye da ke tallafawa manoma wajen inganta irin noma da koya wa manoma dabarun noma na zamani da inganta shuka da tallafa wa masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i.

Wannan yana taimaka wa mutane su sami hanya mai dorewa ta samun arziƙi.

Tallafin inganta tsaro da zaman lafiya

...

Asalin hoton, State House NG, White House

Amurka na bai wa dakarun Najeriya horo da bayanan leƙen asiri da kayan aikin tsaro da kayan yaƙi domin yaƙi da ta'adanci da sauran ƙungiyoyin tada ƙayar baya.

Wannan tallafi ya shafi rundunoni da dama: Sojojin ƙasa, sama da rundunar yan sanda.

Ta yaya yanke tallafi zai shafi Najeriya?

Farfesa Abdullahi Shehu ya yi nuni da cewa idan aka yanke tallafi, ba gwamnati kaɗai za ta ji tasirin hakan ba, talakawa ma za su ji a jikinsu.

"Idan wani ya kawo maka tallafi kuma ya yanke shi, dole ne a ji ciwon hakan, za a sha ɗan wahala. Amma abin da ya rage shi ne a tashi, a ƙara ƙoƙari, a sake ɗaura ɗamara wajen nemo wasu hanyoyin taimako, ko daga wasu ƙasashe ne, ko daga kungiyoyin agaji don cike gurbin da talalfin ya janyo."

"Za a iya samun raguwar kayan aiki a asibitoci, dakatarwar wasu shirye-shirye na ilimi, ja da baya a ayyukan samar da ruwan sha da hanyoyi, da kuma raunana yunkurin yaƙi da rashin tsaro."

Ya ce janye tallafin Amurka zai zama jarrabawa, za a sha wahala, amma kuma ba zai zama karshen tafiya ba.

Me Najeriya ya kamata ta yi?
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsohon Jakadan ya ce abin da Najeriya ta fi buƙata a wannan lokaci shi ne ta ƙarfafa dogaro da kai, domin ƙasar ba za ta iya tauna ci gaban ta gaba ɗaya a kan tallafin waje ba.

"Ya kamata gwamnati ta dubi matsalolin da Amurka ke magana a kansu da kuma hanyar da za a bi a warware su," in ji shi.

Ya ce wannan zai nuna wa duniya cewa Najeriya tana da niyyar gyara kuskuren cikin gida, ba wai kawai jiran waje ya zo ya gyara mata ba.

Ya ƙara da cewa, inganta tsaro shi ne jigon duk wata magana ta ci gaban ƙasa. A cewarsa, "Yana da muhimmanci gwamnati ta ƙara ingaza ƙaiminta wajen inganta tsaro da yaki da ta'addanci da kuma abubuwan da ke addabar tsaro a Najeriya, domin idan babu zaman lafiya, ba za a samu ci gaba ba."

Saboda haka, dole ne Najeriya ta ƙara zuba jari a cikin rundunonin tsaro, da kuma makaman zamani domin rage dogaro da tallafin yaki da rashin tsaro daga ƙasashen waje.

A gefen tattalin arziƙi kuma, Farfesan ya ce: "Muna da arzikin ƙasa da yawa — daga man fetur zuwa ma'adinai."

Ya ce Najeriya na da filin noma da albarkatu da yawan matasa masu ƙirƙira da za su iya zama tushen sabon tattalin arziki idan an saka musu jari da tsari mai inganci.

"Dole Najeriya ta tsare muradunta da na 'yan ƙasa wajen gina ƙasarmu da haɓɓaka arziƙin da Allah ya ba mu," in ji shi.

Ya ce manufar ita ce a kai ga matakin da idan wani tallafi daga waje ya ragu ko ya tsaya, rayuwar talaka ba za ta durƙushe ba. Domin makomar ƙasa ta dogara ne a kan dabarun cikin gida da tsare-tsaren da gwamnati da kasuwanci za su iya gina su da kansu.