Dakatar da tallafin Amurka ka iya farfaɗo da Boko Haram – WFP

Kwano cike da masara

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen / BBC

Bayanan hoto, Wannan shi ne ƙarshen rabon abinci ga dubban mutane da ke neman mafaka daga Boko Haram a Gwoza.
    • Marubuci, Anne Soy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Gwoza
  • Lokacin karatu: Minti 6

Dakatar da tallafin jin ƙai da ake yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya zai iya bai wa ƙungiyar Boko Haram damar kara samun karfi, a cewar hukumomin agaji.

A watannin baya, rage kuɗin agajin da ake bai wa shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya tilasta masa dakatar da tallafin da yake bai wa yankin Arewa maso Gabashin ƙasar tallafi.

Kuma a halin yanzu, gaba ɗaya tallafin shirin ya ƙare.

"Dakatar da tallafin da ake bai wa mutane zai saka 'yan Boko Haram su rinjayi matasa su shiga kungiyar, cikin sauƙi wanda hakan zai ƙara haddasa rashin tsaro a ɗaukacin yankin," in ji Trust Mlambo, shugaban ayyuka a yankin daga WFP, yayin zantawa da BBC.

Ƙungiyar Boko Haram ta shahara a duniya bayan da ta sace fiye da dalibai mata 200 daga garin Chibok sama da shekaru goma da suka wuce.

Tun daga lokacin, ƙungiyar ta yi garkuwa da dubban mutane a hare-harenta, tare da korar fiye da miliyan daya daga gidajensu.

A shekarar 2009, Boko Haram ta fara amfani da karfin makami domin cimma burinta na kafa daular Musulunci a yankin.

Tun daga lokacin, ta haddasa rikice-rikice a Najeriya da makwabtan ƙasashe irin su Kamaru da Chadi da Nijar.

A shekarar 2015, wani reshe na ƙungiyar ya yi mubaya'a ga ƙungiyar IS, wanda hakan ya ƙara tsananta hare-haren da suke kaiwa.

Wata mace mai suna Aisha Abubakar, wadda ke zaune a jihar Borno, ta ce ta rasa fiye da rabin 'yan gidanta sakamakon harin Boko Haram da cututtuka.

"Mijina da yara shida sun mutu a daji," in ji Aisha mai shekara 40, a wata hira da BBC.

Aisha Abubakar

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen / BBC

Bayanan hoto, Aisha Abubakar ta kashe wani ɓangare na dala 20 da ta samu a wannan watan wajen sayen buhun masara.

Hudu daga cikin 'ya'yanta sun tsira da ransu, ciki har da ɗaya da aka ceto kwanan nan daga hannun 'yan bindiga bayan sace shi da suka yi.

Ta tsere zuwa Gwoza, wani gari mai sansanin soja da ke yammacin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Garin Gwoza yana gindin tsaunuka masu duwatsu. Amma bayan tsaunukan akwai dazuka inda 'yan Boko Haram ke ɓuya – abin da mazauna sansanin ke tsoro.

"Ba zan taɓa komawa garinmu ba," in ji Aisha. "Rayuwa a garin ta zama mai matuƙar wahala, kullum muna cikin tserewa ne."

Yanzu tana ƙoƙarin farfaɗowa ta fara sabuwar rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gwoza inda ta auri sabon miji kuma suna da jariri ɗan wata bakwai.

Tsaunukan da suka kewaye Gwoza.

Asalin hoton, Anne Soy / BBC

Bayanan hoto, MayaƘan Boko Haram na ɓuya ne a dazukan da ke bayan tsaunukan da suka kewaye Gwoza.

Aisha na daga cikin kusan mutane miliyan 1.4 da suka rasa matsugunansu a arewa maso gabashin Najeriya kuma kuma ke dogaro kacokan da agajin jin ƙai na WFP don rayuwa.

Ta yi magana da BBC bayan ta je da jaririnta ƙarami wurin rabon taimako a Gwoza. Tana jijjiga jaririn a jikinta yayin da take jiran layinta a wajen rajista, tana riƙe da katin ATM ɗinta.

Ana saka kuɗin wata-wata a cikin wanan kati da ta riƙe, kuma adadin kuɗin da ake bayar wa ya danganta da yawan mutanen da ke cikin gida.

Aisha ta samu dala 20 (kimanin fam 15), inda ta sayi buhun masara da wasu kayan abinci.

....

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen/BBC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mista Mlambo na WFP ya ce, "Babu sauran abin da za mu iya bayarwa bayan wannan watan. Komai ya ƙare a ɗakin ajiyarmu, muna buƙatar gudummawa na gaggawa."

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce wasu canje-canje a shirinta na agaji sun haifar da rage tallafi, bisa manufar "America First" ta Shugaba Trump.

Duk da haka, tace Amurka na ci gaba da zama ƙasa mafi bayar da agaji a duniya, tana kuma ƙarfafa sauran ƙasashe su taimaka.

An bayyana cewa tallafin Amurka ga WFP – wanda ya kai kusan kashi 80 – bai canza ba.

Amma ƙarancin tallafi daga gabaɗaya masu bada gudummawa ya janyo hauhawar rashin abinci mai gina jiki a Najeriya.

Kungiyar likitoc ta duniya MSF ta ce yawan yara da ke fama da mummunan rashin abinci mai gina jiki ya ninka sau biyu cikin rabin shekara.

Tun farkon 2025, yara 652 sun mutu a asibitocinsu saboda rashin samun kulawa da wuri.

Wakilin MSF a Najeriya, Ahmed Aldikhari, ya ce girman matsalar ya fi yadda ake zato, kuma 2024 ya zama wani muhimmin lokaci na rikicin abinci a arewacin Najeriya, bayan manyan masu tallafi kamar Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun rage ko sun dakatar da tallafinsu.

Yawancin waɗanda suka nemi mafaka a Gwoza manoma ne da ba sa iya komawa gonakinsu masu albarka a jihar Borno saboda rashin tsaro.

Asalin hoton, Ayo Bello / BBC

Bayanan hoto, Yawancin waɗanda suka nemi mafaka a Gwoza manoma ne da ba sa iya komawa gonakinsu masu albarka a jihar Borno saboda rashin tsaro.

Najeriya ƙasa ce mafi yawan mutane a Afirka kuma ɗaya daga cikin manyan tattalin arziki, amma tana fama da matsalolin tsaro da na cin hanci da rashawa tun da daɗewa.

Shekarun baya sun zo da hauhawar farashi da faduwar darajar kuɗin Najeriya, tare da gazawa wajen shawo matsalar tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kuma gwamnati ta fara nuna damuwa game da matsalar rashin binci mai gina jiki.

Mako biyu da suka wuce, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ce rashin abinci mai gina jiki ya hana kashi 40 na yara ƙasa da shekaru biyar girma yadda ya kamata.

Ya ƙaddamar da wata hukumar kula da abinci mai gina jiki a matsayin "ɗakin yaƙin da rashin abinci mai gina jiki" da za ta tunkari matsalar a duk faɗin ƙasar.

Amma tambayar ita ce ta yaya gwamnati za ta iya magance wannan matsala yayin da manyan masu ba da tallafi ke yankewa.

Fiye da cibiyoyi 150 da ke kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a arewa maso gabas na fuskantar rufewa.

A Gwoza, wata uwa mai yara biyu, Hauwa Badamasi, ƴar shekara 25, ta ce ta ji ba daɗi bayan jin cewa ɗiyarta ta fari, Amina, ta kamu da cutar rashin abinci mai gina jiki duk da ƙoƙarinta.

"Na ji ba daɗi, domin kowace uwa na so ɗanta ya kasance cikin koshin lafiya," ta shaida wa BBC.

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen Africa wanda ke fuskantar matsalolin tattalin arziƙi.

...

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen/BBC

Hauwa ta ce ba ta iya komawa gonar iyalinta da ke kusa da garinsu na tsawon shekaru saboda matsalar tsaro.

"An dakatar da tallafi, kuma ana kashe mutane a gona. Yanzu me za mu yi da rayuwarmu?" in ji ta, yayin da 'yarta Amina mai shekara uku ke cin abincin gina jiki da aka ba su a asibitin Hausari B.

Asibitin na kula da kusan mutum 90,000, yawancinsu manoma ne da rikici ya raba da muhallansu, kamar Hauwa.

"Za mu shiga matsala matuƙa idan ba mu da abinci ko magani," in ji ta. "Rayuwarmu na dogara da waɗannan abubuwan tallafin."

An ba ta jaka ɗaya na abinci mai gina jiki don ta ci gaba da jinya a gida – amma wannan na iya zama na ƙarshe idan ba a sami tallafi ba.

Mlambo na WFP ya ce matsalar ƙarancin abinci na iya sa wasu mutane su koma hannun 'yan bindiga saboda ƙuncin rayuwa.

"Idan mutane sun rasa abin dogaro har ba za su iya samun abincin gabaɗaya ba, za su iya tsallaka tsaunuka su shiga hannun ƴan Boko Haram" in ji shi.

Duk da cewa sojojin Gwoza suna ba da kariya, mutane da dama ba su da tabbaci kan ƙarshen rikicin, kuma suna fargabar makomarsu.