Kwana 100 da janye tallafin Amurka: Yadda hakan ya shafi ƙasashen duniya

Biloniya Elon Musk, tsaye riƙe da saya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cikin mako uku hukumar kula da kashe kuɗaɗen gwamnati ta da Elon Musk ke jagoranta ta sanar da dakatar da tallafin USAID, da aka kafa a 1961
    • Marubuci, Stephanie Hegarty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Population correspondent
    • Marubuci, Antonio Cubero
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

A farkon shekarar nan ne, Donald Trump ya sanar da dakatar da tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashen waje, bayan shawarar sabuwar hukumar kula da kashe kuɗaɗen gwamnati.

A shekara 2024, Amurka ta kashe kashi 0.22 cikin 100 na arzikinta kan bayar da tallafi, inda ta bayar da dala biliyan 63, lamarin da ya sa ta zama ƙasar da ta fi kowace bayar da tallafi a duniya, a cewar OECD, mai kula da bayar da tallafi a duniya.

Da yawa cikin tallafin da Amurka ke bayarwa tana bayar da shi ne ta hanyar hukumar tallafa wa ƙasashe ta USAID.

Har yanzu fadar White House ba ta bayyana cikakken bayani game da lokacin da dakatarwar za ta ɗauka ba, to sai dai BBC ta yi nazarin bayanan da ake da su a fili, da wasu bayanai daga gwamnati, domin duba wanda zai fi tafka asara.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan USAID, wanda ya zanta da BBC, ya kuma buƙaci a sakaya sunansa saboda tsoro ya bayyana wata ukun farko na dakatarwar a matsayin mafiya ''tashin hankali'' bayan da hukumar kula da kashe kuɗaɗen gwamnatin ta fara aiki.

Ya kuma koka kan yadda matakin zai shafi al'umomin wasu ƙasashen marasa ƙarfi.

"Mutane na cewa tallafin na ciyar da aƙalla mutum miliyan biyu a Sudan, amma duk da haka ba su kula da hakan ba'', in ji shi.

Mako biyu bayan sanar da matakin, gwamnatin Trump ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen kare rayuka, kamar shirin samar da abinci a Sudan.

To amma duk da ɗaga ƙafa da aka yi wa wasu shirye-shiryen, ma'aikatan USAID na cewa tuni ma'aikatan hukumar kula da kashe kuɗaɗen gwamnati suka soke shirye-shiryen.

Kan haka ne wata jami'ar gwamnatin Amurka ta shaida wa BBC, cewa ''soke shirye-shirye 18 da aka yi a Sudan ba sa cikin tsarin waɗanda gwamnati ta amince a ci gaba da yinsu, yayin da ya ce har yanzu ake ci gaba da aiwatar da wasu 37 a Sudan''.

Wasu mutane zaune a tsakiya

Asalin hoton, Sumayya Nabara

Bayanan hoto, Sumayya Muhammad Bala (tsaye a gefe) na taimakawa wajen kula da wasu shirye-shirye a arewa maso gabashin Najeriya, domin bayar da tallafin magunguna da abinci.

"Ba abu ne mai sauƙi ka rasa aikinka rana tsaka ba,'' in ji Sumayya Muhammad Bala, wata ma'aikaciyar agaji a arewacin Najeriya,, ƙarƙashin wata ƙungiya da ke samun tallafin USAID.

Ta bayayna damuwakan halin ƙananan yara da ke fama da yunwa da masu shayarwa za su shiga , sakamakon tsayar da ba su tallafin, sannan kuma idan aka tilasta musu ficewa daga asibitocin da ke samun tallafin USAID.

"Danginsu ba za su iya ɗaukar ɗawainiyar jinyarsu a wasu asibitocin ba,'' in ji ta.''Ba ma tunanin gwamnati za ta iya cike giɓin da aka rasa'', in ji ta.

Lafiyar ƙananan yara da goyon ciki

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar Usaid ta dakatar da tallafin masu haihuwa da ƙananan yara, wasu bayanai daga ƙungiyar KFF, wata ƙungiyar agaji da ke aiki a fannin lafiya, sun nuna cewa Amurka ta kashe dala biliyan 1.3 a 2024 a fannin lafiyar ƙananan yara da mata masu haihuwa.

Hakan na zuwa ne kuwa, duk kuwa da rage yawan mata da ƙananan yaran da ke mutuwa a lokacin haihuwa a cikin shekara 25, wanda aka samu raguwarsa da kashi 40 cikin 100, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a watan Afrilu.

Mafi yawan kuɗin da aka kashe a fannin, an kashe su ne a ƙasashen Afirka, kudu da hamadar sahara, wanda ya rage mace-macen lokacin haihuwa da kashi 70 a 2023.

"Akwai matuƙar damuwa," in ji Dakta Muhammad Abdullahi, wanda ke aiki da wata ƙungiya da ke samun tallafin USAID a asibitoci 12 da ke wasu ƙauyukan arewacin Najeriya don tallafa wa ayyukan masu haihuwa har zuwa lokacin da aka dakatar da ayyukan USAID a watan Fabrairu.

Ayyukansu na tallafa wa ƙananan asibitocin da muhimman kayayyakin aiki, kamar magunguna da horas da ma'aikatan lafiya da ayyukan wayar da kai.

A ɗaya daga cikin asibitocin maras wutar lantarki, ya samo masa wutar sola daga USAID.

"Me kake tunanin zai faru idan aka samu matar da ke buƙatar gaggawa na kai ta asibiti ? Dole wani ya mutu tsakanin uwar da jaririn,'' in ji shi.

Ƙasashe da dama da ke fama da mace-mace mata masu ciki, sun dogara ne kan tallafin USAID kan haihuwa da kula da jarirai, a cewar Ayman Abdelmohsen, shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da lafiyar haihuwa ta, UNFPA.

"Fiye da shekara 30 zuwa 40 gwamnatocin waɗannan ƙasashe na dogara da tallafin na USAID,'' in ji shi.

"Ya kamata gwamnatoci su tashi tsaye, bai kamata su ci gaba da dogara da tallafin ƙasashen waje domin bunƙasa rayuwar mutanensu ba.''

Ministocin lafiya na wasu daga cikin waɗannan ƙasashe ciki har da Najeriya sun ce suna sane da irin illar da hakan zai yi, kuma suna koƙarin shawo kan matsalar, sai dai hakan na buƙatar dogon lokaci.

USAID na ɗaya daga cikin manyan masu samar da magungunan hana ɗaukar ciki a faɗin duniya, inda take kashe dala miliyan 600 a kowace shekara ka hakan.

Kuma duka wannan tallafi zai dakata, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ranar 10 ga watan Afruli ta nuna.

Kafin dakatar da tallafin, gwamnatin Amurka na kashe dala biliyan 12 a kowace shekara a fannin lafiya ga ƙasashen duniya.

Tallafin ya fi mayar da hankali kan cutuka uku da suka haɗa ta tarin fuka da Maleriya da kuma Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki (HIV).

Cutar Tarin fuka (TB)

Cutar tarin fuka (Tuberculosis ko TB), wadda ke kama huhu, ba a samun isassun kuɗin da ake buƙata don yaƙarta.

Cutar na cikin Manyan cutukan da suka fi kisa, inda take kashe aƙalla mutum miliyan 1, 200,000 a kowace shekara.

Amurka na samar da kashi ɗaya bisa uku na abin da ƙasashen duniya ke bayarwa domin yaƙi da cutar, inda take bayar da tallafin dala miliyan 406, a cewar Dakta Lucica Ditiu, shugabar shirin yaƙi da tarin fuka ta Majalisar Dinkin Duniya.

Wata ma'aikaciyar jinya na ɗaukar jini daga wani ƙaramin yaro.

Asalin hoton, KHANA

Bayanan hoto, Kafin katse tallafin USAID, ƙungiyar KHANA mai zaman kanta a Cambodia na tallafawa wajen gano masu ɗauke da cutar tarin fuka a kowace shekara.

Shirin na da ma'aikata 200 da ke kula da masu aikin sa kai 5,000 da ke bi gida-gida domin gano waɗanda ke ɗauke da cutar, domin taimaka musu wajen samun kulawa, tare da daƙile yaɗuwar cutar.

Cuta mai karya garkuwar jiki (HIV/Aids)

Cikin shekara 10 da suka gabata, Amurka na kashe dala biliyan biyar a kowace shekara kan yaƙi da cutar HIV.

Mako guda bayan sanar da katse tallafin, gwamnatin ta sanar da cewa za ta ɗaga ƙafa kan wasu ayyukan.

''Ya kamata a ce yyyukan hana yaɗa cutar daga uwa zuwa jaririnta na daga cikin ayyukan da za a cire a jerin waɗanda za a dakatar da tallafinsu'', in ji Dakta Muhammad Abdullahi.

To amma cikin watan Afrilu,Jaridar New York Times ta bayar da rahoton cewa an shaida wa ma'aikatan shirin su 270,000 cewa su dakatar da ayyukansu.

A cewar wani bincike da Mujallar Lancet ta wallafa a farkon watan Afrilu, idan aka dakatar da wannan tallafi, to za a samu sabbin jarirai da za su kamu da cutar HIV kusan miliyan guda, yayin da za a fuskanci mace-mace 500,000 tsakanin ƙananan yara zuwa shekarar 2030.

Wani ma'aikacin ƙaramin asibiti a Kenya ke duba ƙwalayen kayan tallafin USAID

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikacin ƙaramin asibiti a Kenya na duba ƙwalayen kayan tallafin USAID

Cutar Maleriya

A baya Amurka kan kashe dala biliyan guda kan yaƙi da cutar maleriya a duniya.

A arewacin Najeriya, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa tuni aka rufe wasu ƙananan asibitocin yaƙi da maleriya.

Haka ma a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo - inda Amurka ce babbar mai bayar da kayayyakin gwajin cutar maleriya a asibitocin gwamnati - dakatar da tallafin ya shafi asibitocin.

Kawo yanzu dai babu tabbas kan wane shirin yaƙi da Maleriya ne zai tsallake wannan katse tallafin.

Baya ga kuɗin da Amurka ke zuba wa kai tsaye domin yaƙi da waɗannan cutuka, ƙarƙashin USAID, a kowace shekara kuma takan bayar da dala biliyan biyu ga Majalisar Dinkin Duniya don yaƙi da Cutukan Tarin fuka da Maleriya da kuma HIV.

Duk da cewa gwamnatin Amurka ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafi kan shirye-shiryen tallafa wa rayuka, abin da ke cikin sanarwar 10 ga watan Afrilu ya nuna cewa za a rage tallafin da kashe 55 cikin 100.

Shekaru da dama da suka gabata, masu suka da yawa na cewa Amurka na asarar kuɗaɗe masu yawa domin sanya wasu ƙasashe su ci gaba da dogaro da tallafi daga waje.