Ko ya kamata a riƙa bai wa kowane ɗan'adam tallafin kuɗi?

Asalin hoton, Khaled Desouki/AFP via Getty Images
- Marubuci, Nick Ericsson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Kaddara a ranka cewa kowanne wata an yi maka tanadin kuɗi, ba tare da la'akari da karfin tattalin arzikinka ko yanayin da mutum ke ciki ba.
Wannan shi ne amfanin kafa hukumar samar da tallafin kuɗi wato "Universal Basic Income Grant" - wato UBIG - wanda gwamnatoci a sassan duniya suka shafe tsawon shekaru suna tafka muhawara a kai. Sannan wannan tsari ne da aka jimma ana kokarin gwaji a kansa.
A Jamus, wata ƙungiya mai zaman kanta - Mein Grundeinkommen (My Basic Income) - sun bibbiyi wasu mutane 122 na tsawon shekara uku wanda kowannesu ake ba wa $1,365 duk wata.
Bincike ya gano cewa mutane ba sa ƙin aiki, kusan ma kowannesu na aiki na cikakke lokaci. Sai dai kuma galibin mutanen ba su da tabbacin zama a wuri aiki guda. Sun kuma bada labarin samun gamsuwa da samun rarrar lokaci cigaba da karatu.

Asalin hoton, JustGiving
Wani babban mai bincike da ake kan aiwatarwa a yanzu haka a Kenya na gidauniyar, GiveDirectly, ya nuna makamancin wannan sakamako - koda yake na wucin gadi ne.
A wuraren akwai kauyuka 295 a gundumomi biyu da ake bai wa kuɗaɗe ta hanyar tura musu kuɗi kai-tsaye a wayoyinsu na tsawon shekara biyu zuwa 12.
A faɗin duniya, ba a samu raguwar mutanen da ke kwadago ba, sai dai da dama sun bar aikinsu sun rungumi nasu sana'o'in.
"Na tashi da safe cikin kwanciyar hankali babu wani tunanin zan fita babu abinci, shi ne abin da nake jindadinsa," a cewar Kadi, wata da ta rasa mijinta da bata da tabacaccen hanyar samun kuɗin shiga a Kenya.
Tana aikin wucin-gadi ne kuma tana cikin wadanda ke samu wannan tallafi, inda take samun dala 34 a kowanne wata daga gidauniyar GiveDirectly, wadannan kuɗaɗe ne da ke riketa da ba ta kwarin-gwiwa a kowanne lokaci.
Matsaloli

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shin ka yi mamakin sakamakon wannan bincike? Ban yi mamaki ba, a cewar Dakta Kelle Howson, wanda babban mai bincike ne a kwalejin nazarin tattalin arziki da ke Afirka Ta Kudu.
"Duk wani kokari na mayar da hankali kan daidaito tsakanin kuɗin shigar mutane ba zai taɓa nasara ba, a cewar Dakta Howson.
Bama bukatar sake gwaji domin tabbatar mana ko tsarin UBI mai dorewa ne, kuma abin bai tsaya kan cire kuɗin ba. Galibi mutanen da suka ci wannan gajiyar sun gina kansu ko kafa ta su sana'ar.
A Afirka ta Kudu, misali, damar samun kuɗaɗen tallafi, ya ta'alaƙa kan mutanen da ke da wayewa ta fannin fasaha, inda kashi 20 cikin 100 na al'ummarta ba su da damar samun intanet.
Sannan wadanda za su ci gajiyar tallafin ana sa ran su kasance masu wayoyin zamani saboda cimma duk ka'idojin da ake bukata. Saboda haka, a cewar Dakta Howson, galibin mutanen da ya kamata a ce sun samu tallafin a ci da rabonsu.
A India, 'yanƙasar da ke fama da talauci da ya kamata a ce sun ci gajiyar tallafin gwamnati idan suna da katin ɗan kasa, bincike ya nuna cewa rabin al'umma da ke cikin talauci ba su da katin.
Kuɗi ga kowa?

Asalin hoton, Alex Plavevski/EPA-EFE/REX/Shutterstock
Akwai ƙasashe da dama da suka aiwatar da shirin UBI na gwaji musamman a ƙasashe masu tasowa a shekarun baya-bayanan, ciki harda jihar Madhya Pradesh ta India, da wasu kauyukan Namibia da tsarin tura kuɗaɗe ga 'yan kasa na Iran da suka samar a 2011 domin tallafin abinci da man fetur.
Ƙungiyoyin ƙwararru a fannin tattalin arziki ciki harda Abhijit Banerjee wanda ya lashe kyautar Nobel, wanda kuma ta rubuta maƙala ga hukumar bincike ta tattalin arziki kan wannan batu a 2019.
Zai yi wahala ka yanke hukunci daga waɗannan misalai, a cewarsu.
Sai dai tallafin sun taimakawa wadanda suka ci gajiyarta wajen samun sauki da yin abubuwa da dama lokaci guda. Ana iya cewa sun mayar da hankali wajen kashe kuɗaɗensu ta hanyar inganta rayuwarsu, walau fannin abinci ko magunguna.
Masu fafutika irinsu attajiran 'yankasuwa da 'yansiyasa Elon Musk ya ce a baya tsarin bada tallafi na UBI ya taimaka wajen inganta rayuwar masu cin gajiyarsa da cigaba a fannin fasahar AI.
Shi ma, Dr Howson na cewa matan da ke cikin wannan tsari a Kenya da India sun bada labarin cewa a yanzu sun ji su masu cikakken 'yanci ba tare da dogaro kan maza ba a harkokin da hidimar gida. Ana iya cewa wannan tsari ya taimaka wata wajen dogaro da kansu ta fannnin wadatuwar kudi. Wannan ya taimaka wajen kare mata fadawa cikin mu'amalar aure ko rayuwa mai cutarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Prof Eva Vivault daga Jami'ar Toronto na Canada ya jagoranci wani bincike a kan UBIG a jihohi biyu da ke Amurka - Texas da Illinois.
Acan, mutanen da suka karɓan tallafin dala 12,000 a shekara tsawon shekara uku na aikin ƙasa da sa'a biyu a mako, idan aka kwatanta da Jamus, wanda kuɗaɗensu ya ragu da dala 1,500 a kowacce shekara.
Ya batun masu biyan haraji?
Dr Howson ya ce har yanzu akwai gibi tsakanin wadanda suka yi imanin cewa shirin UBIG na iya ta'azzara "rayuwar zaman kashe wando" sannan zai kasance matsin lamba ga masu biyan haraji - kuma mutanen da ba sa aiki za a ga kamar da gumin wasu suke morewa.
Farfesa Flora Gill ta Jami'ar Sydney na Australia ba ta gama gamsu da shirin UBI ba. A wani rubutanta da aka wallafa a wani shafi na "Transforming Society" a 2023, ta ce: "Idan mutane na son aiki, ya kamata su samu dama. A yanzu, abubuwan ba sauki. Kafin tabbatar da tsarin UBIG, dole mu duba batun hakkin dan adam."
Prof Gill ta nuna damuwarta domin tana ganin hanya ɗaya tilo na samar da kuɗaɗen tafiyar da shirin - wanda take ganin akwai takura - zai ta'alaka kan kara kuɗin haraji.
Sai dai Dr Howson na ganin tsarin ne da za a cimma nasara ba tare da rashin amincewa da tunanin Gill.
Wasu matsalolin
Duk da alfannusa, masu bincike sun ce akwai sauran damuwa kan tsarin UBIG. Misali, fannin fita kwadago zai ragu sosai idan mutane su ka kasance masu zaman banza.
Hauhawan farashi zai kai wani matsayi. Tsarin da Iran ta yi amfani da shi a 2011 ya haifar mata da hauhawan farashin da har yanzu ba ta farfado ba, a cewar wani bincike na NBER da aka gudanar a 2019.
Kwararru na cewa tsarin daidaito da bunkasa zai kasance cikin hadari.
A takaice dai, a ra'ayin Farfesa Vivault, duk wadannan bayanai da nazari za su ta'alaka ne kan raddin gwamnatoci da bai wa al'umma zabi. Sannan dole kasa ta duba hanyoyin mafi sauki da ba za su kassara tattalin arziki ba, a cewarta.











