Ina naira 'tiriliyan 14' da aka bai wa gwamnonin Najeriya bayan cire tallafin man fetur?

Asalin hoton, @jidesanwoolu
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta yi barazanar maka gwamnonin Najeriya da ministan babban birnin tarayya Abuja, a kotu idan ba su bayyana yadda suka yi da naira tiriliyan 14 na rarar man fetur da gwamnatin Najeriya ta ba su ba daga asusun kason tarayya wato FAAC.
Ƙungiyar ta ce ta ba gwamnonin wa'adin mako ɗaya su yi bayani dalla-dalla yadda suka kashe kuɗaɗen ta hanyar bayyana ayyukan da suka yi, da matakin da ayyukan suke yi, da kuɗaɗen da suka kasafta wa kowane aikin.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci gwamnonin su bayyana tsare-tsaren kashe kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin na man fetur da za su samu a nan gaba daga asusun kason gwamnatin tarayyar.
A wani ɓangaren kuma, ƙungiyar ta buƙaci gwamnonin da ministan Abujan su gayyaci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa irin su ICPC a EFCC da kansu su riƙa bibiyar kasafin kuɗaɗensu domin tabbatar ba a wofantar da kuɗaɗen ba.
Ta yi zargin cewa wasu jihohin na amfani da kuɗaɗen gwamnati, wanda ta ce wataƙila a ciki har da wanda suka samu daga rarar kuɗin tallafin man fetur domin tafiye-tafiye marasa amfani da sayen motocin alfarma da sauran kashe kuɗaɗen da ba su dace ba.
Cire tallafin fetur

Asalin hoton, Twittter/@officialABAT
A watan Mayun shekarar 2023 ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a Najeriya, bayan sanar da cewa babu tallafin man fetur a gwamnatinsa kamar yadda ya sanar a ranar karɓar rantsuwar mulkinsa a babban birnin tarayyar ƙasar Abuja.
Cire tallafin man fetur ɗin ke da wuya farashinsa ya tashi daga ƙasa da naira 200 zuwa sama da naira 1,000 kafin daga baya ya sauka, lamarin da ya jefa ƴan ƙasar cikin mawuyacin hali saboda tsadar rayuwa.
Sai dai a wani jawabi da Tinubu a ranar 25 ga watan Fabrailun 2025 a lokacin da yake ganawa da shugabannin jam'iyyar APC a fadar gwamnati a Abuja, ya ce cire tallafin man fetur ya sa gwamnatinsa ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi daga asusun tarayya sau uku.
"Babu ta yadda za a yi Najeriya ta ɗore matuƙar ba a daina biyan tallafin [man fetur] ba," in ji shi.
"Mun ninka kaso na kuɗin da jihohi ke samu sau uku. Muna da isassun kuɗin da za mu bai wa ƙananan hukumomi. Mun kafa hukumar Nelfund da za ta dinga biyan kuɗin karatun ƴaƴanmu," in ji Tinubu a lokacin.
A wata wasiƙar neman bayanai da ƙungiyar SERAP ta fitar, wadda mataimakin daraktanta Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu, ta ce ya kamata a ce ƙarin kuɗin da gwamnonin suka yi daga asusun tarayya ya amfani talakawan Najeriya ne kai-tsaye.
'Ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyar SERAP ta ce cire tallafin man fetur ɗin ya fi wahalar da talakawa, wanda hakan ya sa ta ce tana buƙatar a bayyana yadda talakawan suke amfana daga kuɗaɗen da ake samu bayan cire tallafin.
Hakan ya sa ta ce ƴan Najeriya sun cancanci sanin yadda gwamnonin da ministan Abuja suke kashe kuɗaɗen da suka samu.
"Magance cin hanci da rashawa da ke tattare da wannan kuɗin zai taimaka wajen rage talauci da inganta rayuwar al'umma kuma zai taimaka wa gwamnonin jihohi wajen cika alƙawuran da suka ɗauka."
"Bayanan da muka samu sun nuna cewa asusun kason wata-wata na gwamnatin Najeriya ya raba naira tiriliyan 28.78 a shekarar 2024 zuwa ga matakan gwamnati uku - tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi, wanda ya nuna ƙarin kashi 79 daga shekarar da ta gabata.
"Kuɗaɗen da aka ba jihohi ya ƙaru da kashi 45.5 zuwa naira tiriliyan 5.22, kuma rahotanni na nuna cewa kason wata-wata na 2025 yana haura naira tiriliyan 1.6," in ji ƙungiyar
"Amma duk da ƙarin samun kuɗin, har yanzu miliyoyin ƴan Najeriya na fama da talauci kuma ba sa morar kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin. Har yanzu akwai jihohin da ma'aikata suke bin albashi da fansho, wasu kuma suna ci gaba da cin bashi domin biyan albashi," in ji SERAP.
'Babu tsarin bayyana kashe kuɗi'
Bayan ƙungiyar ta SERAP, akwai wasu ƙungiyoyin da suka daɗe suna sa ido kan hanyoyin da ake bi wajen kashe kuɗaɗen gwamnati, kamar cibiyar bibiya ta 'Center for Fiscal Transparency and Public Integrity'.
Dr Umar Yakubu, babban darakta ne a ƙungiyar, ya bayyana wa BBC cewa cibiyarsu ta gano cewa yawancin gwamnoni ba su da wani tsari ingantacce na bayyana hanyoyin da suke kashe kuɗaɗe.
"Kun dage sai an cire tallafin mai, to amma ina tsarin da za ku sarrafa kuɗin? burin gwamnonin kawai a cire tallafin, a ba su kuɗaɗen su ci gaba da kashewa ba tare da wani tsari inganttace ba. Sun fi so a ci gaba da kashe kuɗaɗen kamar yadda aka saba ba tare da wani tsarin bibiyar hanyoyin sarrafa kuɗin ba."
Ya ce cibiyar tasu ta yi nazarin hanyoyin kashe kuɗaɗen al'umma, inda a cewarsa suka fahimci cewa yawancin gwamnonin ba su da wani tsari mai kyau a ƙasa na bayyana wa al'umma yadda ake kashe kuɗaɗen da ake samu.
Ya yaba da ƙoƙarin SERAP wajen yunƙuri da ta yi na ɗaukar mataki, inda ya ce yana tare da matakin na ƙungiyar na zuwa kotu bayan wa'adin da ta bayar.
Sai dai ya ce ba kuɗin tallafin man fetur ɗin ba ne kawai ya kamata a bincika yadda gwamnonin ke kashewa, "domin bayan kuɗin tallafin man fetur da ya ƙara musu kason da suke samu na wata-wata, akwai kuma kuɗin ƙananan hukumomi.
Ka san kotun ƙolin Najeriya ta ce kuɗaɗen ƙananan hukumomi su riƙa zuwa asusunsu kai-tsaye, amma akwai zargin gwamnonin suna kawo cikas. Don haka shi ma su yi bayani."
Kuɗaɗen da ya kamata a bayyana
A game da kuɗaɗen da ya kamata a yi bayanin hanyoyin kashewa, Dr Umar Yakubu
Ya bayyana wasu ɓangarorin kuɗaɗen da jihohin ke samu, waɗana ya ce ya kamata gwamnonin su fito su bayyana yadda suke kashewa:
- Kuɗin kason wata-wata na tarayya
- Kuɗaɗen ƙananan hukumomi
- Harajin cikin gida
- Basussukan cikin ƙasa
- Basussukan ƙasashen waje











