Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya

.

Asalin hoton, others

A ranar Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

A shekarar 2019 ne dai kamfanin mai na ƙasar NNPC ya bayyana gano tarin arzikin albarkatun man fetur a yankin na Kolmani da ke kan iyakar Bauchi da Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce yankin Kolmani na da arzikin albarkatun man fetur da ya kai ganga biliyan ɗaya da kuma kyubik biliyan 500 na iskar gas.

Shugaban ƙasar ya faɗa a wajen taron cewa an samu masu zuba waɗanda suka zuba jarin da ya kai dala biliyan uku domin aikin haƙo man na Kolmani.

Haka kuma shugaban ƙasar ya umarci kamfanin mai na NNPC tare da abokan aikinsa da su yi aiki tare da mazauna yankin tare da kiran da su koyi darasi daga abin da ke faruwa a yankin Niger Delta , inda 'yan bindiga ke fasa bututun mai, bayan da suka zargi kamfanonin da ke haƙo man a yankin da yin watsi da su.

Shugaban ƙasar ya ce ya tattauna da gwamnonin Bauchi da Gombe, inda suka tabbatar masa cewa za su bayar da haɗin kai domin ci gaba da aikin bunƙasa haƙo man fetur ɗin.

BBC ta tattauna da ɗaya daga cikin manyan jami'an kamfanin mai na NNPC da ke kula da inda kamfanin ke zuba jari, Bala Wunti, inda ya shaida wa BBC cewa ana fatan gina matatar mai da kamfanonin samar da taki da kuma iskar gas.

Ga wasu jerin alfanu da masana suka ce za asamu sakamakon wannan aiki:

Alfanu ga Najeriya

.

Asalin hoton, Getty Images

Ɗaya daga cikin alfanun da za a samu sakamakon haƙo man na Kolmani shi ne Najeriyar kanta za ta samu ƙarin arziki, kamar yadda Dakta Ahmed Adamu, Malami a Jami'ar Nile da ke Abuja kuma masanin harkokin man fetur a Najeriya ya shaida wa BBC.

Ya ce ''A tsarin dokar ƙasar a duk inda aka samo mai a kowanne ɓangare na Najeriya to mallakin gwamnatin Najeriya ne, ba wai mutanen yankin za a raba wa ba''.

Da wannan a iya cewa samun wannan mai wani ƙarin arziki ne ga Najeriya wadda ita ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a nahiyar Afirka, abin da zai sa a samu ƙarin masu zuba jari daga cikin da wajen ƙasar.

Kamar yadda shugaban ƙasar ya faɗa a lokacin ƙaddamarwar inda ya umarci kamfanin mai NNPCL ya yi duk mai yiwuwa a hurumin da doka ta ba shi, domin tabbatar da sun janyo masu zuba jari domin bunƙasa sarrafa man fetur a arewacin Najeriya.

Dokar kashi 13 cikin dari

Haka kuma Dakta Ahmed Adamu ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa a duk inda ake tono arzikin ƙasa to gwamnatocin jihohin na da kashi 13 cikin dari na abin da ake samu a duk wata.

Ya ce ''kashi goma 13 cikin 100 da ake bai wa jihohin yankin Nager Delta a baya yanzu jihohin Bauchi da Gombe su ma za a riƙa basu, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada''

Dakta Adamu ya ce za a fara bayar da wannan ne kawai idan an fara tono man.

Dokar PIA

Masanin harkokin man ya ce dokar Petroleum Industrial Act ta tanadi cewa za a riƙa bai wa al'umomin da ke zaune a yankin da ake aikin haƙo man kashi uku cikin dari na abin da ake samu na man fetur a duk shekara.

Don haka al'umamar yankin Kolmani za su amfana da wannan a duk shekara sakamakon wannan aiki da suka samu.

Rage gorin da ake yi wa Arewa kan fetur

Samun wannan mai na Kolmani zai rage gorin da ake yi wa yankin arewacin Najeriya na dogara da yankin kudancin ƙasar kamar yadda Injiniya Kailani na kamfanin NNPC ya shaida wa BBC.

Ya ci gaba da cewa '''Yan kudu sun daɗe suna zanga-zangar cewa a daina ɓata kuɗi ana neman mai a arewacin ƙasar, amma Alhamdulillahi yau an samu mai a arewa''.

Ya kuma yi kira ga gwamnonin arewacin ƙasar da su mai da hankali wajen haƙo sauran ma'adinan da yankin yake da su.

Samun aikin yi ga 'yan yankin

.

Asalin hoton, Getty Images

Kasancewa aikin yana buƙatar ƙwararru, kuma duk da cewa babu wata doka da ta ce dole sai an ɗauki 'yan yankin aikin a masana'antar, amma idan 'yan yankin suna da ƙwararru da suka cancanta su samu aiki, to za su iya samu, kamar yadda Dakta Ahmed ya ce.

Sannan akwai ayyukan ƙarfi kamar gini da ƙananan ayyukan gadi da leburanci to wannan mutanen yankin duk su za su samu wannan, hakan kuma zai sa su samu kuɗin shiga.

''Haka kuma watakila idan nan gaba aka samu sauyi game da kundin tsarin mulki inda ake cewa jihohi su mallaki albarkatun da ke yankunsu, to ga ka johohin za su ci ribar wannan,” in ji Dakta Ahmed.

Sai dai duk da wannan alfanu akwai wasu ƙalubale da ke tattare da wannan aiki, waɗanda suka hadar da gurɓacewar muhalli ta hanyar gurɓata musu ƙasar noma da haddasa musu hayaƙi da zai guɓata musu muhalli