Mutumin da ya fi gwamnati ƙarfin iko a cibiyar satar ɗanyen man fetur ta Najeriya

Bututun mai na sata

Asalin hoton, Jacob Abai

Rukunin haramtattun bututan man fetur da jami'an tsaron Najeriya ke ganowa na ƙara fito da matsalar satar man fili a ƙasar - wani abin al'ajabi hatta a yankin Neja-Delta da aka saba satar man.

A Jihar Delta, ɓarayi sun gina bututu mai tsawon kilomita 4 har zuwa Tekun Atalantika mai tsananin tsaro.

A can ne manyan jiragen ruwa masu tsawon ƙafa 24 ke yin lodin mai a filin Allah.

"Aiki ne na ƙwararru," a cewar shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPC, Mele Kyari, yayin da yake zagayawa don ganin ɓarnar ɓarayin ke yi wa Najeriya kai-tsaye a kafar talabijin.

Najeriya ta dogara ne kacokam kan ɗanyen mai da take haƙowa kuma kuɗaɗen shigarta na cikin matsala saboda satar man, kamar yadda jami'ai ke faɗa.

Man da ƙasar ke haƙowa ya ragu daga ganga miliyan 2.5 a kowace rana a 2011 zuwa miliyan ɗaya da kaɗan a watan Yulin 2022, in ji NNPC.

Hukumomi na cewa an yi asarar fiye da dala biliyan 3.3 sakamakon satar mai a shekarar da ta gabata a daidai lokacin da sauran ƙasashe masu arzikin mai ke samun maƙudan kuɗi, ita kuwa Najeriya ba ta iya cimma adadin da aka ƙayyade mata ba.

Kuma hakan ba ya nufin ba wata matsala ba ce idan ta yi asarar kuɗi saboda ɓarayin, akwai ɗimbin talauci a taksanin 'yan ƙasa mai yawan gaske.

Akwai matsalolin cin hanci da rashawa, daga maganar tallafin mai - inda babu wanda yake tabbas na man da ake shiga da shi - zuwa samun lasisin mallakar rijiyar mai.

Wani abu da ya ƙara ba da mamaki shi ne, wani kamfanin tsaro ne mai zaman kansa ya gano ɓarayin ba gwamnati ba.

Sai dai kuma ɗan gwagwarmaya Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ba ƙaramin ɗan kwangilar tsaro ba ne.

Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo

Asalin hoton, Jacob Abai

Bayanan hoto, Tompolo na da ƙarfin iko a yankin Neja-Delta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jagora ne mai shekara 51 daga masarautar Gbaramatu a Jihar Delta mai arzikin mai, Tompolo na cikin masu fasa bututan a baya waɗanda a yanzu yake gadi bayan wata yarjejeniya ta naira biliyan 48 tsakaninsa da gwamnatin Najeriya mai cike da cecekuce a watan Agusta.

Ana kallonsa a matsayin tsohon ɗan gwagwarmayar satar mai mafi arziki a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin masu laifi da ake nema ruwa a jallo. An ce ya taɓa sayar wa ƙasar jiragen yaƙi na ruwa.

Ya san tasawirar yankin Neja-Delta, inda rijiyoyin mai suke da bututan gwamnati, kuma mutane da dama sun yarda da rahotannin da ya bayar game da inda ɓarayin suke.

"Akwai hannun jami'an tsaro da yawa a ciki saboda babu yadda za a yi ka yi lodi a jirgin ruwa ba tare da ka bai wa jami'an tsaro cin hanci ba a wannan yankin," kamar yadda ya faɗa wa kafar talabijin ta Channels TV.

Ya kuma ce mafi yawan man an sace shi ne daga wurare da aka jibge sojojin ruwa da na ƙasa. Rundunar soja ba ta mayar da martani game da wannan iƙirari nasa ba, amma da wuya su ƙaryata mutumin da suka shiga yarjejeniya da shi don daƙile satar mai.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Lucky Irabor, wanda ke cikin mutanen da suka gane wa idonsu ayyukan ɓarayin bisa rakiyar dakarun Tompolo, ya ce “sun samu ƙarin ilimi” kuma ya yi alƙawarin ƙaddamar da bincike.

Sai dai ba wannan ne karon farko da ake zargin jami’an tsaron Najeriya da hannu a satar man ba. A watan Janairun da ya gabata, Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya ce akwai hannun wani jami’in ɗan sanda mai muƙamin sufuritanda a satar mai a yankin Emuoha da ke jihar.

Jami'an tsaro 'yan kwangila

Asalin hoton, Jacob Abai

Bayanan hoto, Sojojin haya sun yi wa jami'an tsaron Najeriya jagora zuwa inda ake satar mai

A 2019 ma, Wike ya zargi wani babban kwamandan soja da ƙarfafa wa ɓarayin fetur gwiwa, duk da cewa an musanta zargin.

Ganin cewa duka wannan na faruwa ne a ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban ƙasa kuma ministan mai, lamarin ya raunata yunƙurinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa, a cewar Salaudeen Hashim na gidauniyar CLEEN Foundation mai yaƙi da rashawa.

“Ba lallai a gane cikakkiyar ɓarnar ba har sai gwanatinsa ta sauka daga mulki a watan Mayu,” kamar yadda wani mai sharhi ya faɗa wa BBC.

Jirgin ruwan da aka ƙona a kwanan nan bisa zargi dakon ɗanyen mai na sata mai yawan lita 650,000 a Delta ya jawo cecekuce.

Mutane da dama na tambayar me ya sa jami’an tsaro suka yi gaggawar ƙona hujjar - ɗaya daga cikin nasarorin da Tompolo ya yi a baya-bayan nan – amma hafsan tsaro na Najeriya ya ce babu buƙatar bincike.

Yunƙurin Tompolo na taimakawa wajen daƙile satar man ta bai wa mutane mamaki. Yayin da ake biyan sa saboda aikin, ya bayyana irin ƙaunar da yake yi wa Najeriya da kuma muhallin Neja-Delta, amma kuma shi ne mutumin da yake da tarihin fasa bututai masu yawa a baya.

Kamar yadda wani ƙwararre ya bayyana, bututan sata da ake ganowa a yanzu suna Delta ne, inda yake da ƙarfin iko sosai.

Abu ne mai wuya wani mutum ya yi amfani da su wajen ɗanyen mai tsawon shekaru a wannan yankin ba tare da saninsa ba, a cewarsu.

A baya, an sha fafatawa tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga amma yanzu abubuwa sun ɗan lafa a kwanakin nan, amma wasu na cewa yarjejeniya ce a tsakaninsu cewa kowa ya yi “harkasa”.

Waɗanda kawai abin zai dama su ne ‘yan Najeriya na gari, masu bin doka, da kuma ƙila kamfanonin man, waɗanda ba lallai a ji wani tausayinsu ba a faɗin ƙasar.