Petroleum Industry Bill: Abubuwan da dokar ta ƙunsa da amfaninsu ga talakan Najeriya

Bayanan bidiyo, Bidiyon bayani kan dokar man fetur ta Najeriya
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

A ranar Litinin 16 ga watan Agusta ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rattaba wa dokar man fetur ta Petroleum Industry Bill (PIB) hannu bayan majalisun dokokin kasar sun amince da ita a watan Yuli.

An shafe fiye da shekara 20 ana ce-ce-ku-ce a kan dokar. Sai dai duk da sukar da wasu ƴan ƙasar ke yi mata, shugaban kamfanin mai na Najeriyar (NNPC), Alhaji Mele Kyari, ya kare dokar da cewa tana da matuƙar muhimmanci.

'Yan majalisar da suka fito daga yankin arewacin ƙasar ne a wannan karon suka fi nuna goyon bayansu ga kudirin dokar, saboda abin da suka bayyana da cewa alfanun da suka hango tattare da ita.

Ana kuma sa ran wannan doka za ta yi wa kowanne ɓangare da ya shafi harkar mai a kasar garanbawul.

BBC Hausa ta duba tanade-tanaden dokar da sauyin da za ta haifar ga NNPC, da kuma alfanunta ga gwamnati da talakawan Najeriya.

Wane sauyi PIB ta kawo wa NNPC?

Bajon kamfanin NNPC

Asalin hoton, NNPC

Dokar da Najeriya ke aiki da ita a harkokin man fetur kafin yanzu mai suna Petroleum Act, an kafa ta ne tun 1969, lokacin da ƙasar ta gano arzikin man.

Tun da ta zama doka, daga yanzu za a dinga kiranta da suna Petroleum Industry Act (PIA) - maimakon PIB.

Kamfanin mai na NNPC zai zama na 'yan kasuwa maimakon na gwamnati. Kazalika, dokar ta haɗe dokokin harkokin man fetur na Najeriya 16 waje ɗaya.

Za a sauya wa kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) suna zuwa National Petroleum Corporation - ko kuma NPC a taƙaice.

Kazalika, za a kafa wata hukuma ta daban mai suna National Petroleum Regulatory Commission wadda za ta dinga kula da sa ido kan ayyukan kamfanin. Hukumar za ta maye gurbin sauran hukumomi irin su Department of Petroleum Resources (DPR), da Petroleum Equalisation Fund (PEF).

Ma'aikatar Man Fetur mai suna Ministry of Petroleum Resources za ta koma Ministry of Petroleum Incorporated.

Me dokar PIB ta tanada?

Mele Kyari

Asalin hoton, NNPC

Bayanan hoto, "Saka hannu kan dokar ma kawai nasara ce," in ji Mele Kyari, shugaban kamfanin mai na NNPC

Daga cikin tanadin da aka yi a dokar, za a ware kashi 30 cikin 100 na ribar da ake samu daga man da Najeriya ke sayarwa domin aikin haƙo ɗanyen mai a yankunan da bincike ya nuna akwai ɗanyen mai a can. Dokar ta kira wuraren da suna 'Frontier Basins', wato wuraren kan tudu da ba a fara haƙo mai ba domin sayarwa.

Su ma al'ummomin da ake haƙo fetur a garuruwansu za su samu kashi 3.0 cikin 100 na duk abin da za a kashe yayin haƙo man wajen haɓaka yankunan nasu ta hanyar wani asusu da ake kira Host Communities Trust Fund.

Kafin yanzu, ana bai wa jihohin da ke da arzikin mai kashi 10 ne cikin 100. 'Yan majalisar tarayya sun bayyana cewa kashi 3 cikin 100 zai kai tsabar kuɗi dala miliyan 500 duk shekara - fiye da naira biliyan 200.

Sai dai dokar ta tanadi cewa hatta garuruwan da bututun mai ya wuce ta cikinsu za su samu kashi 3 su ma.

Yaushe NNPC zai koma na 'yan kasuwa?

Shugaba Buhari kenan lokacin da yake tattaunawa da shugaban kamfanin mai na Total Mr Patrick Pouyanne a Faransa

Asalin hoton, NNPC

Bayanan hoto, Shugaba Buhari kenan lokacin da yake tattaunawa da shugaban kamfanin mai na Total Mr Patrick Pouyanne a Faransa

Ɗaya daga cikin tanade-tanaden dokar shi ne cewa a rusa NNPC zuwa ɓangarori cikin wata shida da fara amfani da dokar PIB.

A ranar Talata 18 ga watan Agusta fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa za a rusa kamfanin domin aiwatar da sauye-sauyen, inda ta ce za a maye gurbinsa da wani mai zaman kansa.

Wannan na daga cikin ayyukan da aka ɗora wa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.

Ƙaramin Ministan Mai Timipreye Silver ne zai jagoranci kwamitin, kamar yadda Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasa shaida wa BBC Hausa.

Ya batun tallafin man fetur (Oil Subsidy)?

Man fetur

Asalin hoton, Getty Images

Aiki da dokar PIB na nufin gwamnati ba za ta sake ƙayyade farashin mai ba a Najeriya sannan kuma za a daina biyan tallafin mai kwata-kwata - ko kuma dai aƙalla ba irin yadda aka saba gani a yanzu.

Sai dai Minista Timipreye Silver ya ce gwamnati za ta ci gaba da biyan tallafin har zuwa wani lokaci.

Jami'an gwamnatin sun sha bayyana cewa Najeriya na kashe kusan naira biliyan biyar a kullum wajen biyan tallafin mai, suna masu cewa idan za a sayar da shi ba da tallafi ba zai kai N230 kan kowace lita ɗaya - saɓanin N183 da yake a yanzu.

Sannan kuma za a kafa wani kwamati da zai tsara sayar da mai ba tare da ƙayyade farashi ba ta yadda za a rage wa 'yan Najeriya raɗaɗin abin da ka iya biyo bayan janye tallafin, a cewar ministan.

Wane alfanu Najeriya za ta samu?

Buhari da Mele Kyari

Asalin hoton, NNPC

Wannan ƙudirin dokar dai kamar yadda 'yan majalisar suka bayyana zai kawo muhimman sauye-sauye masu alfanu ga Najeriya da 'yan kasar, la'akari da albarkatun man da kasar ke samarwa.

Shi ma shugaban kamfanin mai na Najeriyar (NNPC), Alhaji Mele Kyari, ya shaida wa BBC Hausa cewa sanya hannu kan dokar ma kaɗai nasara ce.

Ya koka cewa kusan shekara 50 ke nan ba a samu wani sauyi a kan ayyukan da ake yi a ɓangaren man fetur ba a ƙasar.

"Duniya ta ci gaba, irin ayyukan da muke yi duk an sauya yadda ake gudanar da su, amma mu mun gagara yi tsawon shekara da shekaru.

"A misali, kamfanoni suna zuba jari a Afirka na dala biliyan 50, amma a ciki biliyan uku ne kawai suka shigo Najeriya cikin shekara 10 da suka gabata.

"Kuma ba komai ya jawo hakan ba sai kasancewar dokokinmu ba irin na zamani ba ne, saboda ba su da tabbas kan yadda kuɗinsu zai fito idan suka zuba jarin, da sauran abubuwa da dama."

Mista Kyari ya ƙara da cewa a kwanakin baya manyan kamfanonin haƙo mai irin su Shell da Chevron har barazanar janyewa daga Najeriya suka yi.

Sauran sauye-sauyen sun haɗa da sauƙaƙa yadda ake biyan haraji da kuma kuɗin da kamfanonin mai da ke aiki a Najeriyar suke biyan gwamnati, wanda ake fatan zai bunƙasa jarin da 'yan kasuwa daga kasashen waje suke zubawa a cikin kasar.

Ta yaya dokar za ta amfani talaka?

Wata mace a layin sayen man fetur

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mace a layin sayen man fetur

Wasu da dama na ganin cewa masu kuɗi da 'ƴan boko kawai dokar za ta yi wa amfani, ban da talaka.

Sai dai Mista Kyari ya musanta hakan, inda ya ce "ai duk bayanan da na yi a sama ma za su amfani talaka.

"Misali, idan masu zuba jari suka shigo ƙasar aka samar da masana'antu, ai za a samu ayyukan yi sosai. Sannan gwamnati za ta samu dukiya ta yi wa mutane aiki.

"Da zarar dokar nan ta ɗore za a ga ayyuka sun samu, jarin 'ƴan kasuwa ya bunƙasa, bankuna za su shigo ƙasar sannan za a samu damar wadata ƙasar da iskar gas da wutar lantarki.

"Talaka ne zai fi cin ribar wannan sauyi," in ji Mista Kyari.

Me ya sa aka shafe shekaru ba a amince da dokar ba?

Sanatocin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Senate

Bayanan hoto, Shekara kusan 20 aka shafe ana ce-ce-ku-ce a kan ƙudirin dokar ta PIB

Kyari ya ce da ma abu ne sananne a duniya cewa masana'antar man fetur rigimammiya ce, shi ya sa kullum idan aka tashi gyara sai ya gagara.

"Na farko ba a samu cikakkiyar alaƙa tsakanin majalisun dokoki da gwamnatin tarayya ba tsawon shekara 20 ɗin nan.

"A lokutan baya an yi ta ƙorafin a gyara dokar amma sai ka ga ko dai shugaban ƙasa na lokacin ya ƙi ko kuma 'ƴan majalisa su ƙi.

"Bambancin da aka samu a yanzu shi ne akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin 'ƴan majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa.

"Wannan ne ya sa aka cimma nasara wajen kawo ƙarshen wannan tataɓurzar," a cewarsa.

Kazalika ya ce an samu dama ta tattaunawa da manyan kamfanonin da abin ya shafa.

Me ya sa wasu ke sukar dokar?

Gwamnonin Kudu

Asalin hoton, @SEYIMAKINDE

Bayanan hoto, Gwamnonin kudancin Najeriya sun soki dokar PIB a taron da suka yi ranar 5 ga watan Yuli

Batun dokar PIB ya gamu da kakkausar suka musamman daga yankin kudancin kasar, inda ake haƙo man a yanzu.

Kason da za a rika bai wa al'ummomin yankunan da ke samar da man fetur na ɗaya daga cikin abubuwan da suka rika haifar da taƙaddama.

Bayan wani taro da suka yi a Legas ranar 5 ga watan Yuli, ƙungiyar gwamnonin yankin kudu ta ce ba ta amince da kashi 3 cikin 100 da za a bai wa yankunan da ake haƙo mai ba.

Haka nan sun yi watsi da tanadin da ya ce a ware kashi 30 cikin 100 na ribar da ake samu domin ayyukan duba albarkatun mai a wasu yankunan ƙasar.

Gamayyar ƙungiyoyin farar hula a arewacin Najeriya ma ta nuna adawa, inda ta yi zargin cewa kudirin dokar na cike da wasu kura-kurai da za su iya cutar da al`ummar yankin arewacin kasar.

Kungiyar ta ce ta haɗa kai da wasu kwararru wajen nazarin kudurin dokar, kuma ta fahimci cewa mai zai yi tsada a arewa fiye da kudancin kasar sakamakon ɗawainiyar da ke cikin dakonsa.

Ta kuma ce tanadin da aka yi na amfani da kashi 30 cikin 100 na ribar da kamfanoni za su samu wajen hakar mai a kan tudu ba zai biya muradin haƙar mai a arewacin kasar ba, saboda haka bai kamata Shugaba Buhari ya sa hannu a kan dokar ba.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Nastura Ashir Shariff, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun lura an tafka rashin gaskiya a cikinta, don haka ba za su amince da ita ba.

Najeriya ce ƙasa mafi arzikin mai a Afirka, inda take haƙo gangar ɗanyen mai miliyan biyu da dubu ɗari biyar a kowace rana.

Hakan ya sa ta zama ƙasa ta shida a duniya mafi arzikin man.

Sai dai kuma matsalar cin hanci da rashawa da ƙarancin kayan aiki na shafar yanayin ayyukan haƙar man cikin shekara 60 da aka shafe ana yi.