Shin har yanzu gwamnatin Najeriya na biyan tallafin man fetur?

Asalin hoton, State House
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Tun bayan jawabin 29 ga watan Mayu da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi, 'yan ƙasar ke cigaba da tantama kan ko da gaske tallafin man fetur "ya tafi" kamar yadda shugaban ya sanar.
Tantamar ta ci gaba da ƙaruwa ne ganin cewa duk da ninka kuɗin man da aka yi har sau uku, har yanzu 'yan ƙasar kan shafe awanni a kan layi kafin su sha man a gidajen mai.
'Yan watanni bayan haka ne kuma rahotonni a watan Satumban 2023 suka bayyana cewa gwamnatin ta ci gaba da tallafin. Sai a wannan makon kuma wani rahoton ya ce Tinubu ya amince wa NNPCL ya biya tallafin da ribar da ya samu a 2023.
Kamfanin mai na NNPCL ya musanta rahoton, yana mai cewa ba su taɓa biyan wani mahaluki kuɗi ba da sunan tallafin mai cikin shekara tara da suka wuce, kawai dai "sauƙaƙa farashi yake yi".
Sai dai masana sun ce da ma biyan tallafi ba aikin NNPCL ba ne bisa doka ko bisa al'ada, kuma hakan na nufin gwamnatin Najeriya na cigaba da biyan tallafin man fetur amma da wani suna daban.
A ranar Litinin NNPCL ya sanar da samun riba mafi yawa a tarihinsa, inda ya bayyana naira tiriliyan 3.297 a matsayin ribarsa ta 2023, ƙarin naira biliyan 700 (kashi 28 cikin 100) kenan idan aka kwatanta da biliyan 2.548 da ya samu a 2022.
Dokar Petroleum Industry Act (PIA) da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a 2022 ta sauya alƙiblar kamfanin na NNPCL zuwa cikakken kamfanin kasuwanci maimakon na gwamnati kawai.
Sauƙaƙa farashi ne kawai ba tallafi ba - NNPCL

Asalin hoton, X/NNPCL
Bayan tsawon lokaci gwamnatin Najeriya na musanta cigaba da biyan kuɗin tallafin, yanzu ta tabbata tana biyan tallafin ne ta wata hanya daban.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin rahoton da jaridar intanet ta TheCable ta ruwaito, Shugaba Tinubu ya amince wa NNPCL ya yi amfani da kason da yakamata ya bai wa gwamnatin tarayya a matsayin riba wajen biyan tallafin man fetur.
Jaridar ta ce wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta faɗa mata cewa kamfanin ya faɗa wa shugaban ƙasar cewa ba zai iya biyan haraji da sauran kuɗaɗe ba saboda tallafin da yake biya wanda ya kira da "cike gurbi ko kuma giɓin canji tsakanin naira da dala".
Har wa yau, rahpoton ya ce wani daftari na kamfanin ya nuna cewa kuɗin tallafin da za a biya daga Agustan 2023 zuwa Disamban 2024 zai kai naira biliyan 6.884.
Sai dai yayin wani taron manema labarai ranar Litinin, Babban Akanta na NNPCL, Umar Ajiya, ya tabbatar da kashe kashe kuɗin amma ya ce ba na tallafin mai ba ne.
"Cikin shekara takwas ko tara da suka wuce, wannan kamfani bai taɓa biyan wani mutum ko kwabo ba a matsayin abin da ake kira tallafin man fetur," in ji shi.
"Abin da yake faruwa shi ne, mukan sayo mai a wani farashi sai kuma gwamnati ta ba mu umarnin sayar da shi a rabin farashin da muka sayo shi. Bambanci tsakanin farashin da muka sayo da kuma wanda muke sayarwa shi ake kira giɓi (shortfall) ko kuma tallafi.
"Kuma wannan yarjejeniya ce tsakaninmu da gwamnati. Wani zubin sukan biya mu da kuɗi, wani lokacin kuma mu yi zamiya. Saboda haka, babu wasu kuɗi da aka bai wa wani da sunan tallafi."
A taƙaice dai, bayaninsa na nufin gwamnatin Najeriya har yanzu tana sauƙaƙa farashin man fetur ta hanyar bai wa NNPCL damar sayar da shi a kan rabin farashin da yakamata ya sayar.
Manyan dalilai biyu da ke jawo ƙara kuɗin man fetur su ne: ƙaruwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya da kuma karyewar darajar naira. Duka waɗannan abubuwan sun faru tun bayan da Tinubu ya sanar da cire tallafin.
'Rainin hankali'
Tuni masana harkokin mulki da ma'adanai suka fara mayar da martani game da kwangaba-kwambaya da gwamnatin Najeriya ke yi.
Tsohon babban sakatare na hukumar tabbatar da adalci a ɓangaren ma'adanai ta Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative (Neiti), Waziri Adio, ya kwatanta kalaman NNPCL a matsayin "rainin hankali".
"Wannan ɓaɓatun da NNPCL ke yi rainin wayo ne kawai," in ji shi cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
"Da ma ba aikin NNPCL ba ne biyan tallafi...Tsohuwar hukumar PPPRA da aka rushe ce ke da alhakin tantance 'yankasuwar da za a biya tallafi da kuma NNPCL. Sai ma'aikatar kuɗi ta biya 'yankasuwar kuɗi bayan tabbatar da aikinsu.
"Bambancin wannan da na NNPCL a yanzu shi ne; kawai dai yana cire kuɗin tallafin ne daga cikin kuɗin man da ya kamata a dinga sayar wa 'yan ƙasa.
"Maganar cewa babu tallafi saboda sayar da mai ƙasa da yadda aka sayo shi yarjejeniya ce tsakanin NNPCL da gwamnati kawai wasa da kalmomi ne da kuma raina wa jama'a wayo."
Biyan tallafi a ɓoye
Da ma wasu daga cikin masu sukar gwamnatin Tinubu sun sha yin zargin cewa ana biyan tallafin a ɓoye.
A watan Afrilun da ya gabata, tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya na biyan tallafi a ɓoye fiye da yadda ake biya a baya.
"Har yanzu gwamnati na biyan tallafin fetur amma mutane ba su sani ba...Idan kuna so ku gane sai ku kwatanta shi da farashin man dizel," in ji shi yayin da yake amsa tambayoyin 'yanjarida a birnin Maiduguri.
"Ya kamata a ce fetur ya fi tsada, amma yanzu dizel ya fi N1,000 kan lita daya, yayin da fetur yake a N600. Kuɗin da gwamnatin ke biya kan tallafi a yanzu ya ma fi na da."
Shi ma tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa gwamnatin ta Tinubu ta ci gaba da biyan tallafin saboda hauhawar farashin kaya a ƙasar.
Obasanjo ya faɗa yayin wata hira da jaridar Financial Times a farkon watan Agusta: "Akwai jan aiki da yakamata a yi, ba wai ka wayi gari lokaci guda ka ce ka cire tallafi ba. Saboda hauhawar farashi, tallafin da muka cire bai ciru ba. Ya dawo."
Wasu daga cikin dillalan man fetur na Najeriya ma sun alaƙanta ƙarancin man fetur da ƙasar ke fuskanta a yanzu ga gazawar gwamnati wajen biyan kuɗin da take bai wa NNPC domin rage farashin man ga al'umma.
Shugaban ƙungiyar IPMAN a shiyyar arewacin Najeriya, Salisu Tenten ya ce "babbar matsalar ita ce su (NNPC) suna cewa kuɗn litar mai da ake shigaowa ya wuce naira 1,000, gwamnati ne ya kamata ta dawo wa NNPC wannan giɓin da ake samu, inda ana cike musu wannan giɓin da ake samu a kan lokaci da ba a samu wannan matsala ba."
Abin da za a zuba ido a gani shi ne ko har zuwa yaushe gwamnatin za ta ci gaba da haƙura da nata kason a ribar da NNPCL ke samu duk da irin raguwar da take fama da ita a yawan kuɗin shigar da take samu.










