Majalisar Magabata ta Najeriya ta jaddada amincewa da salon mulkin Tinubu

Wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ke jagorantar taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ke jagorantar taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023
Lokacin karatu: Minti 3

Majalisar Magabata ta Ƙasa a Najeriya ta jaddada amincewarta ga salon shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ‘yan kwanaki bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a faɗin kasar.

Haka nan, majalisar ta nuna rashin amincewarta ga duk wani yunƙuri na sauyin gwamnati ba ta hanyar zabe ba a zaman da ta yi na yammacin Talata.

Majalisar kan yi zama ne a duk lokacin da wani muhimmin abu ya tunkaro ƙasar domin bayar da shawarar yadda za a tunkare shi, kuma wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ke jagorantar taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Majalisar ta ƙunshi tsofaffin shugabannin ƙasar zaɓaɓɓu da na mulkin soja, da gwamnoni, da ministoci, da shugabannin majalisar tarayya, inda suke tattauna halin da ƙasa ke ciki da kuma matakan da suka kamata a ɗauka.

Cikin tsofaffin shugabannin da suka halarci zaman na Talata akwai Muhammadu Buhari, da Goodluck Jonathan, da Abdulsalami Abubakar, da Yakubu Gowon, wanda ya halarta ta bidiyo.

Ƙudirorin da majalisar ta cimma

Najeriya

Asalin hoton, State House

A cewar wani Ministan Tama da Ƙarafa Dele Alake, gabanin jaddada amincewar majalisar ta saurari bahasi daga ministoci da wasu shugabannin hukumomi kan halin da ƙasar ke ciki a ɓangaren tsaro, da tattalin arziki, da aikin gona, da dai sauransu.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya ce sau biyu suna kaɗa ƙuri'ar amincewa da shugabancin Tinubu a taron.

"Ina mai farin cikin shaida muku cewa mu ma gwamnoni, kamar Majalisar Magabata, mun kaɗa ƙuri'ar jaddada amincewa da salon mulkin shugaban ƙasa," in ji shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe na ciki gwamnonin da suka halarci zaman kuma ya faɗa wa wakilin BBC Haruna Tangaza muhimman abubuwan da suka tattauna a zaman:

Tsaro

Gwamnan ya ce majalisar ta tattauna kan matsalolin da suka shafi tsaro a faɗin ƙasar.

"Malam Nuhu Ribadu [mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro] ya ba mu cikakken bayani kan halin da ake ciki da kuma matakan da ake ɗauka a yanzu," in ji gwamnan.

Tattalin arziki

Ministoci sun gabatar da bayanai da suka shafi tattalin arziki.

"Ministan kuɗi ya kawo bayani kan yanayin tattalin arziki."

Yunwa

"Haka nan, shi ma ministan noma ya yi bayanai kan halin da ake ciki game da tsadar farashin kayan abinci a faɗin ƙasa, inda aka faɗa yanayi kamar na yunwa."

Da aka tambaye shi ko akwai wasu ƙudirori takamaimai da suka cimma bayan jin waɗannan bayanai, sai ya ba da amsa da cewa:

"Ba ƙudirori ba ne kawai, sun ba mu bayanai ne da kowa zai je ya duba, sannan kuma gwamnati ta ɗauki matakai a gwamnatance."

Abin da shugaban ƙasa ya faɗa wa gwamnoni

Bayan kammala taron majalisar Shugaba Tinubu ya sake keɓewa da gwamnonin jiha, inda suka sake yin wata ganawar.

"Abubuwa ne da suka shafi dangantakar gwamnoni da gwamnatin tarayya, musamman s suaboda matsalar da aka samu yayin wannan zanga-zanga, da kuma buƙatar mu haɗa kai," a cewar Gwamna Inuwa Yahaya.

"Ma'ana ya kasance gwamnatocin jiha da na tarayya suna tafiya kan babi ɗaya ba gtare da an samu bambance-bambance ba, saboda bambanci zai iya kawo mana damuwa."