Nawa ne albashin ƴan majalisar dokokin Najeriya?

Asalin hoton, X/NGRSenate
Majalisar dokokin Najeriya ta mayar wa tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da martani game da kalamansa kan kudaden albashin ƴan majalisar
A ranar Juma'a ne tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo wanda ya sha sukar gwamnati ya yi zargi ƴan majalisar cewa su ke yankwa kansu albashi mai tsoka da kuma hanyoyin da suke samu kuɗi fiye da ƙima.
A cewar tsohon shugaban, hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ya kamata ta yanke hukunci kan albashin da kowane ma'aikaci zai karɓa.
A martaninta, majalisar dokokin ta ce duk abun da ake ba wa ƴan majalisar na kan tsari tare da cewa ba su ke yankawa kansu albashi ba.
Amma a cikin wata sanarwa da Yemi Adaramodu, kakakin majalisar dattawa ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana ikirarin tsohon shugaban a matsayin "marar tushe".
Sanata Lawal Adamu Usman ɗanmajalisa da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattawan kasar ya shaida wa BBC tare da rantsewa cewa "albashinsu bai kai miliyan daya ba."
‘’Duk albashinmu gabaɗaya bai kai miliyan daya ba wallahi, idan kuma maganar alawus-alawus ne za a yi, sai dai mu ciyo bashi, saboda girman zirga-zirgar da nake yi daga Abuja zuwa mazaɓun da nake wakilta domin kowa na zuwa da buƙatarsa," in ji sanatan.
Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya.

Asalin hoton, @SPNigeria
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarun baya baya nan ɓangaren majalisar dokokin Najeriya na daga ɓangaren gwamnati da galibin mutane musaman ma masu sharhi kan al'amurran yau da kullum da ƙungiyoyin fararen hula ke zargin cewa abubuwan da suke samu na wuce ka'idar da ya kamata a ce ana ba su a matsayin haƙƙoƙinsu na yi wa alumma dokoki.
Wasu ƙungiyoyi da ƴan Najeriya sun ta nuna tsaya ga ƴan majalisar a kan zargin yadda suke laftawa kansu kudin mazaɓu a kasafin kuɗi wanda wasu ke ganin sun fifita kansu.
A wasu lokutan ma wasu ƴan majalisar da kansu sun fito sun koka kan cewa ana nuna bambanci a rabon kuɗin mazabun.
A yanzu kuma tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ne ya soki ‘yan majalisar kan cewar suna yankawa kansu albashi da kuma samun kuɗi masu gwaɓi daga fadar shugaban kasa.
‘’Kudin jarida, alawus din ɗan kamfai da kudin bahaya, kuma kuna ba kanku abubuwa barkatai, cikin girmamawa kun san hakan ba daidai ba ne a ce ina yankawa kaina albashi, majalisar dattawa na yin haka, har ma tinkaho kuke yi da haka’’ in ji Obasanjo.
Tsohon shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa ana bai wa dukannin ‘yan majalisar naira miliyan 200.
Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sa ido kan harkokin Majalisun dokokin kasar ya ce akwai ƙamshin gaskiya a kalaman tsohon shugaban kasar:
‘’Akwai wasu kudade da a duk lokacin da za su tafi aikace-aikace ba ya cikin alawus -alawus dinsu, baya cikin albashinsu , hatta taron jin bahasin jama’a suna karbar alawus- alawus’’ in ji shi
Rafsanjaji ya yi gargadin idan har ba a kawo karshen wannan matsalar ba, to ba za a a daina rigimar siyasa da rigimar zabe ba.
A cewarsa "idan mutane sun san cewa idan suka zo majalisa za su sami irin wadannan makuɗan kudade na Halak da na haram to za a ci gaba da samun rikici lokacin zabe"
Me Obasanjo ya faɗa?

Asalin hoton, PASCAL PAVANI
An ruwaito tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, sa’ilin da ya karɓi baƙuncin wasu daga cikin wakilan majalisar dokokin ƙasar – yana magana kan batutuwa da dama.
Cikin abubuwan da ya yi magana a kai har da halin da ƙasar ke ciki a yanzu, da batun ƙayyade wa’adin zaɓaɓɓun shugabanni zuwa shekara shida da kama-kaman shugabanci tsakanin arewaci da kudancin ƙasar.
A lokacin tattaunawar, Obasanjo ya zargi ƴan majalisar da shata wa kansu albashin da suke so, inda ya soki hakan, tare da cewa hukumar tarawa da raba kuɗaɗen haraji ta ƙasar ce kaɗai ke da ikon tantance albashin ma’aikatan gwamnati.
Ya ce: “Ba ku ne ya kamata ku yanke wa kanku yawan albashin da za kuɗauka ba; hukumar RMFAC ce ke da wannan hurumin, amma kun yanzu ku ne ke tantance abin da za a biya ku.
“Bai kamata a ce ni ne zan yanke wa kaina abin da za a biya ni ba. Wannan ya saɓa wa ƙa’ida, amma kuna yin hakan.
“Sannan a wasu lokutta ɓangaren zartaswa na ba ku kudin da ba ku cancanta ba. Dukkanku kun samu naira miliyan 200,” in ji Obasanjo.
Nawa ne gaskiyar albashin ƴan majalisa?

Asalin hoton, Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission website
Ana yawan ce-ce-ku-ce kan yawan albashin da ƴan majalisar dokokin Najeriya ke ɗauka a kowane wata.
Sai dai har yanzu babu wata hukuma da ta fito ta yi bayani ƙarara a baya-bayan nan kan ainihin albashin ƴan majalisar.
Sai dai a wasu lokuttan wasu daga cikin ƴan majalisar sun ɗan tsakura wa mutane bayani game da albashinsu, musamman a lokutan da aka matsa musu su yi bayani.
A shekarar 2018, Sanata Shehu Sani daga mazaɓar Kaduna ta tsakiya ya ce shi da sauran ƴan’uwansa ƴan majalisa na karɓar naira miliyan 1.5 duk wata a matsayin alawus ɗin tafiyar da ayyuka, baya ga gundarin albashinsu da suke ɗauka.
A watan Yulin 2024, Benjamin Kalu, wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, kuma mai wakiltar mazaɓar Bende, ya ce naira 500,000 ne albashin ɗan majalisar tarayya.
Ya fadi hakan ne a lokacin da yake hanƙoron ganin ƴan majalisa sun zabtare kashi 50 cikin ɗari na albashinsu domin tallafa wa al’umma sanadiyyar matsin rayuwa.
Sai dai kuma shugaban Majalisar Wakilan Najeriyar, Tajudeen Abbas ya ce naira 600,000 ne albashin ƴan majalisar.
Binciken BBC ya gaza tabbatar da sahihancin alƙaluman da ƴan majalisar suka bayar.
Sai dai mun duna shafin Hukumar tarawa da rarraba kuɗaɗen haraji ta Najeriya (RMFAC), wadda ita ce ke tantance abin da ya kamata a biya zaɓaɓɓun shugabanni, kamar Shugaban ƙasa da mataimakinsa, da gwamnoni da mataimakansu, da masu bayar da shawarwari, da ƴan majalisa da duk masu riƙe da zaɓaɓɓun muƙamai, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada a sashe na 84 da na 124.
Lokaci na ƙarshe da hukumar ta wallafa albashi da alawus-alawus na masu riƙe da muƙaman gwamnatin shi ne tsakanin 2007 zuwa 2009.
Bayanin da hukumar ta wallafa ya nuna cewa albashi da alwus-alawus na sanatoci da sauran ƴan majalisa ya kama ne daga naira miliyan daya zuwa naira 700,000 a kowane wata tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.

Asalin hoton, Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission website

Asalin hoton, Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission website

Asalin hoton, Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission website











