Dalili hudu na yawan karyewar darajar naira

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Darajar takardar kudin Najeriya - Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin kasar.
A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,415 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.
Wannan karyewar da darajar naira ta yi ya jefa rayuwar al'ummar Najeriya cikin halin kunci tare da jefa 'yan kasuwa cikin rudani kasancewar da dama a cikinsu ba su da tabbacin ko za su iya tsallake wannan jarrabawa ganin yadda farashin dala ya tashi sosai.
Duk da cewa naira ta yi ta fuskantar koma-baya tun a gwamnatin da ta wuce wadda ta mika ragama ga gwamnatin Bola Tinubu a Mayun bara, takardar kudin ta sake yin kasa wata daya bayan nan.
A watan Yunin 2023 ne babban bankin Najeriya, CBN ya soma aiwatar da tsarin daidaita darajar naira a wani yanayi na barin kasuwa ta yi halinta wajen tsayar da farashin dalar.
Sai dai tsarin da gwamnati ta bijiro da shi na da sarkakiya saboda akwai abubuwa da dama da ke kawo tarnaki ga tsarin.
Wani kwararre kan sha'anin kudi, Victor Aluyi ya ce irin wannan faduwa da naira ke yi ba ya nuna darajar takardar kudin.
Ya kara da cewa babbar matsalar da ke janyo tashin farashin dala shi ne tsarin da gwamnatin ta bijiro da shi kan naira na fuskantar babban kalubale saboda rashin dalar da ake bukata domin aiatar da tsarin.
Tattalin arzikin Najeriya na bukatar dala wajen tafiyar da shi kasancewar galibi ana shigo da kayayyakin da kasar ke amfani da su ne daga wasu kasashen amma ba ta iya samar da kayayyakin da al'ummarta ke bukata.
Abin da ya sa darajar naira ke ci gaba da karyewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin ya ce tsarin daidaita naira da aka soma aiwatarwa watanni shida da suka gabata na fama da kalubale da dama.
Daya daga cikin matsalolin, a cewarsa shi ne mutane ba su yi amanna da tsarin ba - dalilin ke nan da mutane ke sayen dala duk da yadda farashinta ya yi sama saboda suna tunanin za su samu kudi idan suka yi hakan.
Kwararren, Victor Aluyi ya bayyana cewa tsarin na CBN bai fayyace abubuwa ba saboda bankin ba ya samar da bayanai abin da ya sa mutane ba su fahimci abin da ke faruwa ba. Ya kuma ce wannan ne ya sa wasu tsiraru ke amfani da yanayin da ake ciki domin amfanar kansu.
Akwai kuma yan kasuwa da suke yada jita-jita ba wai saboda suna son musayar kudin idan naira ta fadi ba amma saboda ba su da tabbacin abin da zai faru idan suka bukaci siyan dala nan da wata biyu masu zuwa.
Abu na biyu shi ne lokacin da gwamnati ta soma aiwatar da tsarin, ya bude musu ido sun gane cewa tashin da dala take a yanzu ba karami bane.
Abin da hakan ke nufi, a cewar Aluyi, shi ne, "abubuwa sun cunkushe wa CBN".
"Ba za ka iya daidaita darajar naira kawai da baki ba... a hakikanin gaskiya da zarar ka daidaita naira, dole ne ka samu kudin dala da zai tallafa wa tsarin. Idan ba ka samu dala don taimaka wa tsarin ba, toh babu abin da zai faru.
"Babban kalubalen shi ne babu dalar da za ta taimaka wa tsarin, ana yawan bukatar dala dalilin da ya sa darajar naira ke ci gaba da sauka a kan dala ke nan."
Kamar hakan bai wadatar ba, a ranar 23 ga watan Janairu, CBN ya rage farashin dala lamarin da ya kara karyar da naira. Wannan ne ya janyo matsala ta uku.
Farashin dala ya fadi kasa bayan da gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya sanar a ranar Laraba cewa babban bankon yana kokarin kara yawan kudaden a kasuwar hada-hadar musayar kudaden kasashen waje na kasar.
Wani mai sharhi kan musayar kudaden waje, Kyle Chapman, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faduwar da naira ke yi ya zama ruwan dare kasancewar abin na faruwa a kai a kai.
Chapman ya kara cewa idan darajar naira na yawan faduwa, ba za a rika samun masu saka hannun jari a Najeriya ba.
Yadda za a magance faduwar darajar naira
Aluyi ya ce yana ganin watakila wani abu ya faru nan kusa da zai sauya yadda darajar naira ke tafiya a yanzu.
Baya ga wannan, ya ce dole ne gwamnati ta kara shigar da dala cikin tattalin arziki.
Ya ce gwamnati za ta iya kara abin da take samu daga danyen mai ta hanyar kara samar da shi.
Ra'ayin Chapman ya zo daya da na Aluyi inda ya ce farashin naira a hukumance ya kua yin daidai da na kasuwar bayan fage saboda CBN ba zai iya warware basukan da yake bi ba sabo da karancin dala.
Ya kuma ce akwai bukatar gwamnati ta kara kudin ruwa ta yadda hakan zai karkato da hankalin masu hannun jari.
Aluyi ya ce idan aka kara kudin ruwa, zai kara yawan kudaden kasshen waje wanda hakan ka iya yawan kudaden waje da ke hannun gwamnati.
Ya kara da cewa duk da cewa wannan ba tsari bane na dindindin, amma zai taimaka wa gwamnati wajen shawo kan matsalar faduwar darajar kudin naira.
Yadda musayar naira kan dala ta kasance tun 2013
2013 - ₦157.27
2014 - ₦169.68
2015 - ₦196.99
2016 - ₦305.22
2017 - ₦306.31
2018 - ₦306.92
2019 - ₦306.95
2020 - ₦381
2021 - ₦410.47
2022 - ₦449.05
2023 - ₦897.6
Zuwa lokacin hada rahoton, a yanzu, farashin dala a hukumance ya kama kan ₦892 yayin da a kasuwar canji ake sayar da ita kan ₦1,415.











