Mummunar faɗuwar darajar naira a tarihi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
Darajar kuɗin Najeriya ta yi mummunar faɗuwa da ba ta taɓa yin irin ta ba, tun bayan ƙaddamar da naira a watan Janairun 1973.
A lokacin da naira ta maye gurbin tsohon kuɗin fam, wanda ƙasar ta yi amfani da shi.
Hukumomi sun sanya darajar kuɗin, a kan naira ɗaya daidai da shilling ko sule goma.
Sai dai, shekara hamsin bayan samar da kuɗin, darajar naira na fuskantar jarrabawa da ba ta taba fuskanta ba a gomman shekarunta.
Har ta kai a wani lokaci cikin wannan mako, an canji dalar Amurka ɗaya a kan takardar naira mafi girman daraja, wato naira dubu ɗaya.
Ko da yake, a farashin hukuma har yanzu ana sayar da dala ɗaya a kan naira 785 ya zuwa yammacin ranar Talata.
Wasu masanan tattalin arziƙi na ganin karyewar darajar naira, wata barazana ce ga Najeriya.
Faɗuwar darajar naira a kasuwar canji, kamar yadda masu cinikin kuɗin suka bayyana, ta faru ne saboda buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje musamman dalar Amurka, wadda ta yi ƙaranci a cibiyoyin da ke hada-hadar kuɗin a farashin hukuma da kuma masu shaci-fadin farashi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An sayar da dala ɗaya a kan sama da naira 1,000, kafin ta sauko zuwa naira 995 da safiyar Talata a kasuwar canji ta Abuja, in ji wani mai hada-hadar kudi. A makon da ya gabata, dala daya an sayar da ita a farashin naira 980.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani ɗan canji yana cewa mako uku ke nan Babban Bankin kasar bai samar da dala a cibiyar hada-hadar kuɗin hukuma ba, abin da ya ta'azzara karyewar darajar naira.
Lamarin na faruwa ne daidai lokacin da sabon gwamnan Babban Bankin ƙasar, Olayemi Cardoso ya kama aiki, bayan majalisa ta tabbatar da naɗa shi, kan wannan muhimmin muƙami.
Wani mai canji a kasuwar canji da ke bakin Wapa Kano, Alhaji Auwalu Soja, ya shaida wa BBC cewa, a Kano ma an samu tashin farashin dala da ba a taɓa ganin irin sa ba a tarihi.
"Muna yin iyakar bakin ƙoƙarinmu saboda ba gwamnati ce ke ba mu dalar ba, mu ne muke iya bakin ƙoƙarinmu wajen samo kuɗin don biya wa kwastomominmu buƙata."
"A ranar Talata 26 ga watan Satumba, muna sayen dala a kan naira 980, mu sayar da ita naira 995, amma gaskiya a nan Kano, farashin dala bai taɓa kai wa 1,000 ba.
"Amma mun sa mu labari a wasu sassan (kasar) cewa ta kai hakan," in ji shi.
Ina matsalar take?
Gwamnati kullum na cewa tana ƙoƙari wajen ganin ta shawo kan matsalar, inda a baya babban bankin ƙasar ke samar da dala ga ƴan kasuwa a farashin hukuma.
Sai dai bayan hawan mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnati ta fitar da wani tsarin da ta kira "kasuwa ta yi halinta".
Masana tattalin arziki a kasar na ganin ƙarfin arziƙin Najeriya, bai kai a saki kasuwar musayar kuɗi ba tare da an sanya ƙa'ida ba, saboda hakan na iya haddasa hauhauwar farashin dala, lamarin da ke faruwa yanzu haka ke nan.
Dr Murtala Abdullahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziƙi a Jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua Katsina, ya ce "Lamarin akwai tashin hankali saboda idan dala ta kai naira dubu ɗaya, ko ba ta da taƙamaiman farashi, to zai shafi tattalin arziƙin Najeriya gaba ɗaya, saboda yadda ƙasar ta dogara da dala."
A cewarsa, "Za a iya kwatanta tashin farashin dala a Najeriya da kamar mutum mai zazzaɓi, wanda ya fara da ciwon kai, ke nan akwai yiwuwar komai zai iya ƙara taɓarɓarewa gaba kaɗan."
"Matukar kuma ba a yi hoɓɓasa ba, tattalin arzikin zai iya shiga mummunan yanayin da zai yi wahalar fita."
Masanin ya ce tashin dalar na iya jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Ya ce babbar matsala ce idan ya kasance abin da ƙasa ke samu, bai kai abin da take kashewa ba.
Dr Murtala ya ƙara da cewa "Gwamnatin Najeriya tun 2002, abin da ake samu bai kai kuɗin da take kashewa ba, hakan na haifar da janyewar masu zuba jari daga ƙasashen waje."
"Bashin da Najeriya ta ci ya kai mata iya wuya, kuma zai iya tsorata masu zuba jari wajen shiga ƙasar domin yin hulɗar kasuwanci," in ji Dr Murtala Ƙwara.
Sai dai a ɓangaren ƴan canjin suna ganin rashin samar da dalar daga hannun hukumomi kuma a kan farashinta ne ya ƙara haddasa halin da ake ciki.
"Gwamnati ba ta ba mu dala, mu ne muke samo ta kamar masu sayar da wake ko tattasai da tumatir ne da yake shiga kasuwa ya sayo haja sannan ya zo ya sayar, to haka muke shiga lungu da saƙo muna nemowa." Cewar Auwalu Soja.
Ko hakan na da wani alfanu?
Masana na ganin tashin farashin dalar na da nasa amfanin kamar yadda yake da illoli.
"Wani lokaci tashin farashin kuɗaɗen waje na da alfanu amman idan tattalin arziƙin ƙasa yana da ƙarfi."
Saboda yana taimakawa wajen janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Haka zalika, matakin na ƙarfafa gwiwar mazauna ƙasashen waje su shiga ƙasar domin yin kasuwanci, cewar Dr Murtala Kwara.
Hakan kuma, in ji masanin, zai taimaka wajen shigar kuɗaɗen waje cikin ƙasar kuma zai taimaka wajen sauke farashin dalar.
Ina mafita ?
Masanan tattalin arziƙi a Najeriyar na ganin gwamnatin ƙasar ba ta kama hanyar shawo kan matsalar ba saboda, "kullum bashi sama yake yi, kuma gwmanati ba ta buɗe hanyoyin da za ta ƙara samun kuɗaɗen ƙasar waje ba."
"Abin da Najeriya take sawowa daga ƙasashen waje bai kai abin da take fitarwa ba, hakan matsala ce babba wadda idan gwamnati ta tafi a haka yadda take tafiyar hawainiya, to lallai farashin dala yanzu ya fara tashi," cewar Dr Murtala Ƙwara.
Dr Murtala Abdullahi Ƙwara, ya ce "idan gwamnati za ta yi abin da ya dace lallai komai zai daidaita kuma za a samu sauƙin rayuwa, farashin dalar zai sauka matuƙa."
"Hanya mafi sauƙi da za a samu mafita ita ce gwamnatin Najeriya ta ƙarfafa tattalin arziƙin cikin gida, ta rage dogaro da ɗanyen man fetur, a ƙarfafa hanyoyin kasuwanci yadda zai kasance abubuwan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje su zama ana yin su cikin gida, ma'ana a inganta masana'antun cikin gida," inji Dr Ƙwara
Masanan na hasashen cewa gwamnati za ta iya cimma nasarar shawo kan matsalar ne idan ta yi tsarin da ya dace.
"Kamar misali sai gwamnati ta ce, rubu'in farko na shekara za ta rage abubuwan da ake shigowa da su daga ƙasashen ƙetare da kamar kashi 30 cikin ɗari, daga nan duk lokaci zuwa lokaci sai ta sanya abin da take son cimmawa."
Har wa yau, masanin tattalin arziƙin na ganin rashin gyara matatun man fetur na cikin gida na kan gaba wajen ƙara ta'azzara koma baya ga tattalin arziƙin Najeriyar.
Sai dai a ɓangaren ƴan canjin suna ganin mafita guda ce a sake buɗe masu kamfanonin, a ci gaba da ba su dala a farashin gwamnati.
"Mutane na ganin dala na tashi amma ba laifinmu ba ne, laifin gwamnati ne saboda ya kamata a dawo mana da kamfanoninmu, mu ci gaba da hada-hadarmu shi ne kawai zai sauko da farashin dalar nan.











