Matsin rayuwa bai hana saya wa shugaban Najeriya Bola Tinubu jirgi ba

Asalin hoton, State House
- Marubuci, Nkechi Ogbonna
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi sabon jirgi ƙasa da mako biyu bayan zanga-zangar da 'yan ƙasar suka yi kan tsadar rayuwa.
Ba tare da wata-wata ba, Tinubu ya hau jirgin na Airbus A330 ranar Litinin zuwa Faransa, wanda shi ne mafi sabunta cikin tawagar jiragen da suka zarta biyar.
Sai dai babu tabbas ko majalisun dokokin ƙasar sun amince da sayen jirgin ganin cewa ba a sani ba ko yana cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2024, kuma ba a bayyana kuɗin da aka kashe wajen sayensa ba.
Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X, ya tabbatar da balaguron amma bai faɗi dalilin zuwan Tinubu Faransa ba ko kuma tsawon lokacin da zai ɗauka.
"Sabon jirgin da aka sayo ƙasa da farashin kasuwa, zai taimaka wa Najeriya rage kashe kuɗin tattali da na mai, wanda ya kai miliyoyin dala duk shekara," a cewar sanarwar.

Asalin hoton, State House
'Yan kwanaki kaɗan da suka wuce ne aka dawo wa gwamnatin Najeriya da jirgin bayan wani kamfanin China mai suna Zhangson Investment Co. Limited ya ƙwace shi bayan umarnin kotun da ya samu na ƙwace wasu kadarorin ƙasar sakamakon rikicinsa da gwamnatin jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.
Jirgin mai shekara 15 da ƙerawa wanda kuma aka ƙiyasta farashinsa kan dala miliyan 600, an ce yana da faffaɗan wurin zama na alfarma kuma yanzu yana ɗauke ne da lamba 5N-NGA, inda ya maye gurbin Boeing BBJ 737-700 mai shekara 19 da ƙerawa.
Wasu jami'an gwamnatin ƙasar sun faɗa a baya cewa akan kashe kuɗaɗe masu yawa na kula da jiragen shugaban ƙasar ne saboda tsufansu.
A watan Yuni, 'yanmajalisar tarayya sun ba da shawarar saya wa fadar shugaban ƙasar sababbin jirage biyu, suna masu cewa tsofaffin ba su cikakkiyar lafiya.
A watan da ya gabata ne 'yanmajalisar suka amince da ƙaramin kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar musu, inda aka ƙara yawansa daga naira tiriliyan 28.7 zuwa N35.06. Sai dai babu tabbas ko an saka sayen jirgin a cikin sabon kasafin.
BBC ta tuntuɓi ofishin shugaban majalisar dattawa da kuma na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba mu samu amsa ba.
Ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka na fuskantar matsalolin tattalin arziki sakamakon hauhawar farashi, da faɗuwar darajar naira, da kuma ƙarancin hanyoyin samun kuɗin shiga na gwamnati.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu masu sharhi na siffanta sayen jirgin a lokacin da ya dace a ce ƙasar ta matse bakin aljihu a matsayin rashin tausayi ga miliyoyin 'yan ƙasa da ba su iya samun abincin da za su ci.
Mutum kusan miliyan 161 ne a Najeriya ke fama da matsalar abinci, yayin da 39.4 ke fama da ƙarancin abincin mai gina jiki, a cewar wani rahoto kan yanayin abinci a duniya.
"Ganin cewa gwamnatin Najeriya ta yi gaban kanta wajen sayen jirgin duk da koke-koken da aka yi game da matsin rayuwa, ya nuna rashin sauraro na wannan gwamnati," kamar yadda ɗantakarar adawa a zaɓen da ya gabata, Peter Obi, ya wallafa.
Bayan shekara ɗaya da hawan Tinubu mulki, fadar shugaban ƙasa ta sayi sabon jirgin sama, da sabon jirgin ruwa, ta ware naira biliyan 21 don gyara gidan mataimakin shugaban ƙasa, ta saya wa jami'an gwamnati motocin hawa ciki har da ware naira biliyan 1.5 wajen saya wa matar shugaban ƙasa motoci.
A cikin shekara ɗaya, ƙungiyoyin ƙwadago sun yi yajin aiki da zimmar neman ƙarin albashi mafi ƙanƙanta, inda sai daga baya gwamnatin ta amince da mayar da shi N70,000 daga N30,000.
Tsawon wata 18 kenan a jere hauhawar farashi na ƙaruwa a Najeriya, inda ta kai ƙolouwa kashi 34.19 a watan Yunin 2024, kafin ta sauko zuwa 33.4 a watan Yuli.
Amma duk da haka, akasarin kayan abinci ba su sayuwa a wajen mafi yawan 'yan Najeriya, waɗanda darajar kuɗinsu ke zubewa akai-akai.
Najeriya ta koma ta huɗu a jerin ƙasashen Afirka da suka ƙarfin tattalin arziki maimakon ta ɗaya a baya, kamar yadda alƙaluman asusun lamuni na duniya IMF ya nuna. Darajar naira kuma ta faɗi da sama da kashi 60 cikin shekara ɗaya.
Mako kusan uku kenan da dogayen layukan mai suka dawo a faɗin ƙasar, inda masu ababen hawa ke shafe awanni a layi kafin su sayi man a gidajen mai, kuma haka abin ya kasance a lokuta da dama na shekarar da ta gabata.
Duk da cewa Najeriya ce kan gaba a azrikin fetur a Afirka, takan shiga da kashi 90 cikin 100 na tataccen man da take amfani da shi daga ƙasashen waje saboda matatun manta ba su aiki. Hakan ya jawo ƙaruwar neman kuɗaɗen ƙasar waje daga 'yan kasuwa domin sayo man.
"Gwamnati ba ruwanta da damuwarmu. Wahalarmu ba ta dame su ba, suna kashe kuɗinmu ne kawai wajen tafiya ƙasashen waje. Amma mun ƙyale su da Allah," kamar yadda wani mai aikin faci a Legas ya shaida wa BBC.











