Me ya sa jiragen shugaban Najeriya ke samun matsala?

Asalin hoton, Bashir Ahmed
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
A baya-bayan nan ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya soke tafiyar da ya tsara yi domin wakiltar shugaban ƙasa Bola Tinubu a taron ƙoli kan kasuwanci tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka a birnin Dallas.
Soke tafiyar tasa ta samo asali ne sakamakon tangarɗar da jirginsa ya fuskanta a yayin bulaguron.
Hakan ya zo ne kusan mako ɗaya da ba da rahoton cewa shugaba Tinubu ya tafi Saudiyya daga Netherlands a jirgin kasuwa saboda jirgin da ya tafi da shi ya samu matsala.
Me ya sa jiragen shugaban Najeriya ke yawan fuskantar tangarɗa?
BBC ta tuntuɓi Kyaftin Ado Sanusi, wani ƙwararre a ɓangaren sufuri kuma shugaban kamfanin jirgin sama na Aero Contractors domin jin abin da ya sa hakan ke faruwa da kuma hanyoyin magance matsalar.
Kyaftin Sanusi ya bayyana cewa kowane jirgi na iya fuskantar matsala, "ba wai jiragen shugaban ƙasa kaɗai ne ke fuskantar matsala ba".
Sai dai ya ce ana son a tabbatar cewa jiragen shugaban ƙasa a kodayaushe suna da ƙoshin lafiya kuma a duk lokacin da aka nemi su yi aiki za su yi
'A riƙa duba lafiyar jiragen a kai a kai'
Kyaftin Ado Sanusi ya ce ba zai iya cewa rashin kula da jiragen na bayar da gudummawa wajen yawan matsalar da jiragen ke samu sai dai ya ce a fahimtarsa matsalar ba za ta rasa nasaba da shekarun jiragen wato sun tsufa, hakan zai bukaci a rika kula da su a kai a kai.
Ya ba da misali cewa “idan aka sayi jirage na shugaban kasa a wannan shekarar, bayan shekara 10 ana amfani da jiragen, gyararrakin da za su ƙaru, tangarɗar da za a riƙa samu da jiragen bayan shekara 10 ko shekara 15 zai ƙaru shi ma.”
Ya ce watakila hakan ne yake sa ake ganin jiragen na yawan samun matsala saboda “jiragen an dade ana amfani da su”.
Ya kara da cewa idan aka dade ana amfani da jiragen “dole ne ka ci gaba da gyara su a kai a kai.” In ji kyaftin Sanusi.
A cewarsa, ya kamata a kullum a rika duba lafiyar jiragen shugaban kasa don a tabbatar da ingancinsu idan za a yi amfani da su.
Yawan jiragen shugaban Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kyaftin Ado Sanusi ya ce: “Akwai babban jirgin da shugaban ƙasa ke tafiya da shi kirar Boeing wanda ake kira 737 Business Check, akwai kuma wasu kananan jirage da yake amfani da su da kamar sun kai guda hudu.”
A bayaninsa, masanin ya ce zai yi wuya ya iya tantance yawan jiragen shugaban kasar da suke da lafiya da wadanda ba su da lafiya.
Ya bayyana cewa masu kula da jiragen ne kadai za su iya tantance hakan.
Kyaftin Sanusi ya kuma ce babu wani adadi na yawan jirage da shugaban kasa ya kamata a ce yana da su saboda “shi shugaban kasa ba kullum yake tafiya ba.”
Sai dai ana iya duba yanayin tafiye-tafiyen da yake yi domin a ga yawan jiragen da ya kamata a ce shi shugaban kasa a Najeriya na da su.
Ya yi misali da wasu kasashe inda masu kamfanin jirgin sama na kasa suke daukan jirage biyu su ce a ajiye don amfanin shugaban kasarsu ko wani wanda zai yi tafiya daga fadar shugaban kasa.
“Wasu kasashen za su saka jirage kamar guda shida su ce a bar su na shugaban kasa ne, ko idan zai yi tafiya ko mataimakinsa ko wasu a fadarsa za su yi tafiya da za su yi amfani da su.”
A cewarsa, kowace kasa tana duba bukatar shugaban kasa da fadarsa da yawan jiragen da za su bukata.
Tsarin jiragen shugaban ƙasa a wasu manyan ƙasashen duniya
Kyaftin Ado Sanusi ya soma bayar da misali da Amurka wadda ya ce ba ta cika fitowa ta bayyana abin da take da shi ba sai dai ya ce “mun san suna da jirage da shugaban kasarsu ke tukawa guda biyu.”
“Kuma su ma sun dan tsufa amma ana ta gyara su tare da bunkasa su.”
Da ya tabo Ingila kuwa, kyaftin Ado Sanusi ya ce kasancewar suna da kamfanin jirgin sama na kasar, “sun dauki Wadansu jirage daga cikin kamfanin don amfanin Firaiminista.”











