Me ya sa kwangilar titin Legas zuwa Calabar ke haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya?

Asalin hoton, Tinubu Facebook
A baya-bayan nan wani babban batun da ya fi kowanne jan hankalin 'yan Najeriya da janyo ka-ce-na-ce shi ne batun aikin gina titin Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 700 da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi a watan Fabrairu.
Titin wanda zai fara daga birnin Legas zuwa birnin Calabar na jihar Rivers zai kasance mai hannu 10 sannan kuma za a kammala shi a tsawon shekaru takwas.
To sai dai da alama aikin na shan suka daga 'yan Najeriya da suka haɗa da 'yan siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma talakawa.
Hakan ne ya sa muka duba wasu batutuwan da ke ci gaba da haddasa ce-ce-ku-ce dangane da wannan aiki.
'Seyi (ɗan gidan) Tinubu na da hannu a kwangilar'
A ƙarshen makon nan ne tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya ɓara dangane da yadda ɗan gidan shugaba Tinubu, Seyi Tinubu yake cikin aikin gina titin dumu-dumu.
Atiku Abubakar a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Seyi Tinubu na cikin shugabancin kamfanin CDK Integrated Companies wanda wani ɓangare ne na kamfanin Chougry Group, mallakar Gilbert Chagoury, ɗaya daga cikin abokan kasuwancin shugaba Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, ya ce "kasancewar kamfanin ɗaya daga cikin waɗanda ke gudanar da aikin titin na Calabar zuwa Legas ya ci karo da dokokin yin aiki ba tare da son rai ba."
Atiku ya rawaito daga wani kamfanin dillancin labarai da ke Faransa, mai suna Africa Intelligence News Agency wanda ya rawaito cewa hukumar da ke kula da rijistar kamfanoni ta Najeriya, Corporate Affairs Commission ta bayyana cewa Seyi Tinubu na ɗaya daga cikin masu kamfanin Chagoury Group.
Wannan suka dai ba ta yi wa fadar shugaban Najeriya daɗi ba, inda ta mayar da martani, inda a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, Tinubu ya zargi Atiku Abubakar da hautsina alƙaluma da bayanai dangane da aikin titin.
Abin da ake zargin Tinubu shi ke faruwa a wasu jihohi - masana
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu fashin baƙin siyasa a Najeriya irin su Kwamared Abdulmajid Babangida Sa'ad suna ganin duk da cewa gwamnatin Najeriya ta fito ta ƙaryata al'amarin amma "idan babu rami mai zai kawo batunsa."
Ya ce "al'amarin yana da ban takaici yadda za ka ga shugabanni a Najeriya suna aiwatar da al'amura da ke nuna sun fi damuwa da kansu da iyalansu maimakon bai wa abubuwan da talakawan da suka zaɓa fifiko." In ji Kwamared Abdulmajid.
Ya ƙara da cewa "wannan tsari ba daidai ba ne koda kuwa an yi aiki mai kyau domin idan ka duba dokokin da'ar ma'aikata da na kwangila sun haramta shugaba ya bai wa kamfanin da ke da alaƙa da kansa ko iyalansa kwangila."
To sai dai kwamared Abdulmajid Babangida ya ce ba "Tinubu ba ne kawai yake da laifi a wannan fannin domin irin abin da ke faruwa kenan a wasu jihohi inda wasu gwamnoni ke bai wa ‘ya’yansu da makusantansu da kamfanoninsu kwangilar aiki.
Sannan irin ayyukan da ake yi na gadoji da titina da ke sa a cire wannan kaso 10 ai yawanci duk hanyar azurta kansu ne." In ji Kwamared Abdulmajid.
Kowace kilomita za ta ci naira biliyan huɗu

Asalin hoton, David Umahi Facebook
Wani batun dangane da wannan aikin titin da shi ma ya janyo musayar yawu tsakanin 'yan ƙasa da gwamnati shi ne haƙiƙanin adadin kuɗin da za a gina kowace kilomita ɗaya ta aikin mai tsawon kilomita 700.
Da farko dai sai da tsohon mataimakin shugaban na Najeriya kuma ɗan takara shugabancin ƙasar a jam'iyyar adawa ta PDP, ya yi zargin cewa kowacce kilomita za ta laƙume har naira biliyan takwas.
To sai dai ministan ayyukan Najeriya, David Umahi ya fito ya musanta hakan, inda a karon farko ya sanar da cewa kowace kilomitar titin za ta ci naira biliyan huɗu ne ba takwas ba da Atiku ya faɗi.
Dangane kuma da adadin kuɗin da aikin zai lanƙwame, David Umahi ya ce akwai yiwuwar aikin zai lashe tsabar kuɗi fiye da naira tiriliyan 15.
A ranar 1 ga watan Mayun wannan shekarar ne, ministan ayyuka na Najeriya, David Umahi ya sanar da fara biyan kuɗin diyya ga waɗanda aikin titin Legas zuwa Calabar ya shafa.
Ministan ya ce gwamnati ta ware naira biliyan 2.75 ga mutanen da titin ya ratsa ko kuma ya shafi filaye da gidajensu.
'Irin su Atiku na taka wa gwamnati burki'

Asalin hoton, bbc
Mai fashin baƙin, Abdulmajid Babangida Sa'ad ya yaba wa tsohon shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin Najeriyar ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar dangane da yadda yake yin kakkusar suka kan abubuwa da dama da wani lokacin ma 'yan Najeriya ko dai ba su sani ba kwata-kwata ko kuma ba su fahimta ba.
"Ai mun gode Allah akwai irin su masu adawa domin idan ba don suna irin wannan ba to ai da wasu batutuwan da dam haka za su wuce. Ko da zarge-zargen nasu ba gaskiya ba ne amma hakan na taka rawa wajen sanya gwamnati ta shinga taitayinta." In ji Kwamared.
A baya-bayan nan dai za a iya cewa ɗan takarar jam'iyyar ta adawa ta PDP, Atiku Abubakar yana ƙara matsa wa gwamnati lamba wajen sukar ayyuka da ƙudirce-ƙudircenta.
Ko a farkon makon nan sai da Atiku Abubakar ya soki shirin tafiyar shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ƙasashen wajen domin halartar wasu taruka daban-daban.
Kuma masu fashin baƙi da dama sun alaƙanta fasa tafiyar mataimakin da kakkausar sukan da Atikun ya yi wa gwamnatin.











