KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 15/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. A karon farko cikin shekaru an tattauna Isra'ila da Lebanon gaba da gaba

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila da Lebanon sun amince su ci gaba tattaunawarsu ta kai tsaye, bayan ganawarsu ta farko ta gaba da gaba da suka yi cikin gomman shekaru, yayin yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

    Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, wanda ya bayyana haka, ya ce zuwa yanzu ba a kai ga yanke shawarar lokaci da kuma inda za a yi zaman ba.

    Wakiliyar Lebanon a tattaunawar ta Washington - wadda ita ce jakadiyar Lebanon din a Amurka, Nada Hamadeh Moawad, ta bayyana tattaunawar a matsayin mai amfani, yayin da takwaranta na Isra'ila, Yechiel Leiter, ya ce sun yi tattaunawa mai armashin gaske.

    Sai dai babu wani ci gaba da aka samu kan batun dakatar da buɗe wuta da Lebanon ke neman a yi, inda Isra'ila ta kafe cewa lalle ilalla sai ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ɗin wadda Iran ke marawa baya, ta zubar da makamanta.

    Hezbollah dai ta yi watsi da tattaunawar.

  2. An cika shekara huɗu da fara yaƙin Sudan, wane hali ƙasar ke ciki yanzu?

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da yakin basasar Sudan ya shiga shekararsa ta hudu, masu bayar da agaji na taro a birnin Berlin na Jamus, domin tattauna yadda za a ci gaba da samar da taimako dafarfado da tattaunawar zaman lafiya, a kan halin tabarbarewar rayuwa mafi girma a duniya.

    Shekara 3 da ta gabata fada ya barke a Khartoum, babban birnin shi ne cibiyar wannan mummunan yakin basasa, kafin sojojin kasar su sake kwato shi daga mayakan RSF.

    Sama da mutum miliyan 12 ne rikicin, neman ikon tsakanin rundunar sojin Sudan da kuma kungiyar RSF ya raba da muhallinsu.

    fadan ya fara ne a babban birnin kasar Kahartoum, amma ya fantsama har zuwa yammaci da kudancin kasar.

    Duk wani kokari na cimma zaman lafiya ya dakata kuma tattalin arzikin kasar ta Sudan ya durkushe.

    Kashi 65 cikin dari na al'ummar kasar na bukatar abinci da ruwa da matsuguni da kuma magani.

  3. Masu bibiyarmu a wannan shafi Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan an wayi gari lafiya, da fatan nasara a wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da mu kamar kullum domin kawo muka labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran.

    Kazalika da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya na abubuwan nishaɗi, takaici, al'ajabi da kuma ban tausayi.

    Ku kasance da mu.