Me hare-haren Amurka a Sokoto da Kwara ke nufi ga tsaron Najeriya?

Asalin hoton, US Defence Department
Ana ci gaba da tafka muhawara kan hare-haren da gwamnatin Amurka ta sanar da ƙaddamarwa a wasu sassan Najeriya.
A daren Alhamis ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa sojojin ƙasarsa sun kai wani harin da ya kira mummuna a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Haka kuma da safiyar Juma'a sai aka samu labarin wani harin a garin Offa da ke ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, inda aka ga kwankon bam.
A garin Jabo, rahotanni sun nuna cewa harin ya sauka ne a wasu gonakin albasa, amma a wani harin na garin Tangaza, rahotanni sun ce harin ya kai ga sansanin ƴan Lakurawa, kuma an ga mayaƙan suna tserewa.
A Tangaza, shugaban ƙaramar hukumar ta Tangaza Isa Saleh Bashir, ya shaida wa BBC cewa "tabbas an kai hare-hare cikin daji kuma sansanonin ƴan ta'adda ne. Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren sun haɗa da wani ƙauye da ake kira Tandami.
"Ba mu samu labarin mutanen da suka mutu ba amma dai tabbas an jikkata. Rahotanni na nuna cewa an ga jami'an tsaron jamhuriyar Nijar da ke sintiri sun ce sun ga Lakurawa na tserewa daga yankin," in ji shugaban ƙaramar hukumar.
Me hakan yake nufi?
A game da abin da hare-haren suke nufi, BBC ta tuntuɓi Barrista Bulama Bukarti wanda masanin tsaro ne kuma lauya mai zaman kansa a Birtaniya, inda ya ce ƴan Najeriya za su yi maraba da taimakon Amurka matuƙar an yi abin da ya dace.
Bulama ya ce, "Trump ya fara magana ne kan matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta kimanin wata biyu da suka gabata.
"Ya fara magana ne yana goyon bayan zargin muzgunawa kiristoci da yi musu kisan gilla, sannan ya yi barazanar cewa zai ɗauki mataki idan gwamnatin Najeriya ba ta magance matsalar ba."
Sai dai Bulama ya ce tun lokacin da Trump ya fara barazanar ne suka yi gargaɗin cewa akwai buƙatar ya yi aikin tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya.
"Don haka mun ji daɗin ganin yadda ya kai hare-haren da amincewar gwamnatin Najeriya."
Tasirin hare-haren

Asalin hoton, Abdganiy Saad
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai tuni muhawara ta kaure a tsakanin mutanen ƙasar, inda wasu ke ganin fargar jaji kawai Trump ya yi, a wani ɓangaren kuma wasu ke ganin an buɗe ƙofar fatattakar ƴanbindigar ke nan.
Da yake jawabi kan hakan, Bulama ya ce hare-haren za su yi tasiri matuƙar gaske wajen magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta, "matuƙar an yi abin da ya dace."
Ya ce akwai buƙatar hare-haren su kasance an amfani da bayanan sirri, "sannan hare-haren su kai inda ya kamata, sannan a kan waɗanda suka kamata a kai wa harin."
Masanin harkokin tsaron ya ce hare-haren za su taimaka wajen rage ƙarfin jagororin mayaƙan, "wanda hakan zai taimaka wajen rage musu ƙarfi da daƙile hanyoyin da suke gudanar da ta'addancinsu."
Sai dai Bulama ya ce akwai buƙatar a aiwatar da aikin sojin cikin tsanaki kuma ba tare da ɓoye-ɓoye ba.
"Za mu jira mu gani domin ya kamata gwamnatin Najeriya da ta Amurka su fito su bayyana wuraren da aka kai hare-haren da kuma kan waɗanda suka kai wa hare-haren. A lokaci irin wannan, yana da matuƙar muhimmanci a fito fili a bayyana abubuwan da ke faruwa."
Lauyan ya ƙara da cewa ƴan Najeriya za su yi matuƙar farin ciki idan har hare-haren suka kasance kan mayaƙan da suka addabe su ne.
"Ƴan Najeriya za su yi farin ciki, duk da cewa shi Trump yana sanya addini a cikin matsalar, wanda hakan ke ƙara haifar da rabuwar kai a tsakanin maimakon gyara," in ji shi.
Bulama Bukarti ya ce matuƙar a kan mayaƙa aka ƙaddamar da hare-haren, kuma ba a kashe fararen hula ba, ƴan ƙasar murna za su yi, kuma za su yi maraba da taimakon na ƙasar Amurka.
A game da iƙirarin Trump na kai hari kan mayaƙan IS, Bulama ya ce a yankin arewa maso gabas ne akwai mayaƙan IS.
"A arewa maso yamma da aka kai harin, ƴanbindiga ne suka fi yawa, sannan akwai ƴan Lakurawa da suka ɓulla. Shi ya sa ƴan Najeriya suka yi mamakin jin Trump yana cewa ya kai harin ne kan mayaƙan IS," in ji Bulama.












