Abubuwan da suka biyo bayan zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da ɗan majalisar dokokin ƙasar Amurka, Sanata ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da bari ana yi wa Kiristoci "kisan kiyashi", hukumomi da al'ummu da dama sun mayar da martani.
Sanata Ted Cruz dai ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisar dattawan Amurka a watan Satumba, inda ya yi zarge-zargen.
A ranar Talata ta 8 ga watan Oktoban nan ne kuma Ted Cruz ɗin ya wallafa a shafinsa na X cewa ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi a Najeriyar sun kashe Kiristoci 50,000 daga shekarar 2009 kawo yanzu a faɗin ƙasar, sannan sun lalata makarantun mabiya addinin Kiristan 2,000 da coci 18,000.
Ted Cruz ya nemi majalisar dokokin Amurkar ta ƙaƙaba wa jami'an gwamnatin Najeriya waɗanda ya zarga da "kawar da kai da ma wani lokacin taimakon masu ɓarnar, takunkumai.
Ga jerin martani guda huɗu tun bayan zarge-zargen:
Martinin gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, Mohammed Idris/X
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen na Sanata Ted Cruz, cewa ana harar Kiristoci ne inda ta ce ƙungiyoyn da suke yin hare-haren suna harar ƴan Najeriya ba tare da banbanci ba, sannan ta kuma amince da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar amma ta ce ana samun cigaba.
Gwamnatin ta kuma musanta zargin cewa ba sa yin komai wajen hana kisan Kiristocin.
Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙari wajen ƙoƙarin fattakar ƙungiyoyin ƴanta'adda a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin ƴanƙasar, kuma ana ganin sakamakon hakan.
''Tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025 kadai, fiye da ƴanbindiga 13,543 ne sojojinmu suka kashe tare da kuɓutar da kusan 10,000 da ake garkuwa da su a faɗin ƙasar'', a cewar gwamnatin ƙasar.
Gwamnatin ta yi kira ga kafofin yaɗa labarai na duniya da saran masu sharhi su riƙa aiki bisa doka, tare da mutunta gaskiya a aikinsu.
''Muna kira ga masu ruwa da tsaki su riƙa aiki da ilimi wajen gudanar da ayyukansu , sannan su guji yaɗa labaran ƙarya da za iya kawo rarrabuwar kai a ƙasarmu, a maimakon haka su ƙarfafa wa gwamnati gwiwa a ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da laifuka a ƙasar''. In ji Mohammed Idris.
Majalisar Dattawa za ta aike da tawaga zuwa Amurka

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE
Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da zarge-zargen na sanata Ted Cruz ta kuma amince da aike da tawaga zuwa Amurkar domin fahimtar da su yadda batun yake.
Majalisar ta ce zarge-zargen babbar barazana ce ga hadin kan Najeriya.
Ƴan Majalisar sun yanke shawarar yin aiki tare da gwamnatin tarayya kan matakan da suka fi dacewa na yaƙi da ta'addanci da kuma matsalar tsaro.
Sanata Ali Ndume, shi ne dan majalisar da ya gabatar da wannan ƙuduri a gaban majalisar, ya lissafa illolin da ke tattare da zarge-zargen da suka haɗa da hana ƴan Najeriya biza da hana su amfani da kadarorinsu da dai sauransu.
Majalisar wakilai ta yi watsi da zargin

Asalin hoton, NASS
Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da iƙirarin da Amurka ta yi na cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya saboda addini, tana mai cewa wannan labari ba gaskiya ba ne kuma yana da ruɗani.
Majalisar ta kuma buƙaci a samu haɗin kai tsakanin diflomasiyya da hukumomin cikin gida wajen mayar da martani kan ƙudirin doka da ake shirin gabatarwa a Majalisar Dattawan Amurka, wanda ke neman a saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke take hakkin 'yancin addini.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Okezie Kalu, da wasu 'yan majalisa suka gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.
Kungiyar CAN ta musanta zargin

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta musanta zargin da sanata Ted Cruz ya yi cewa ta na mai cewa adadin waɗanda aka kashe bai kai haka.
Rabaran Joseph John Hayab, shi ne shugaban kungiyar Kiristoci reshen jihohin Arewacin Najeriya, ya min ƙarin bayani.
"Mu Kirista a Najeriya ba mu goyi bayan abin da shi Sanata ke yi domin idan aka saka Najeriya a cikin ƙasashen da za a ware su ba za a yarda sojojin Najeriya su sayi makamai ba. Kenan ƴan ta'adda za su ci gaba da kashe Talakawa. An ce wani ma wai ya ce an kashe Kiristocin Najeriya har guda 500 wannan ba haka ba ne." In ji Joseph Hayap.
Rabaran ya ƙara da cewa matsala ce da take fuskantar Kiristoci da Musulmi kuma dole ne dukkannin al'ummar ƙasar tare da gwamnati su tashi domin tunkarar yan ta'adda.











