Me ya sa ba a zaɓar mace Fafaroma?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muralitharan Kasi Viswanathan
- Aiko rahoto daga, BBC Tamil
- Lokacin karatu: Minti 4
Mace ba za ta iya shugabantar cocin Katolika ba. Aƙidar Katolika ba ta amince mata su zama manyan malaman addinin kirista ba. Amma mene ne dalilin hakan?
Bayan rasuwar Fafaroma Francis, wanda shi ne jagoran mabiya ɗariƙar Katolika na duniya, yanzu an fara batun zaɓen sabon fafaroma. Zaɓaɓɓun manyan malaman cocin ne za su zaɓi sabon fafaroma.
Amma bisa tsari na ɗariƙar Katolika, namiji ne kawai zai iya zama fafaroma.
Ɗaya daga cikin muƙamin jagoranci da ya shafe shekara 2000 a duniya ba tare da katsewa ba shi ne muƙamin fafaroma, wanda shi ne shugaban cocin Katolika.
Peter, wanda ɗaya ne daga cikin sahabban Isa Almasihu 12, ana ɗaukan shi a matsayin jagoran cocin Katolika na farko a duniya.
Tun daga wancan lokacin ne ba a samu katsewar wannan muƙami ba tsawon shekara 2000.
Ya zuwa yanzu an yi fafaroma fiye da 250, sai dai babu mace ko ɗaya daga cikinsu.
Matsayin mata a cocin Katolika

Asalin hoton, Getty Images
Baya ga cewa mata ba za su iya zama fafaroma ba, haka nan ba za su iya kaiwa matsayin manyan malaman darikar Katolika ba, kamar Priest ko Bishop.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A ɗarikar Katolika akwai matakan da ake bi domin kaiwa matsayin shugabanci. Na farko shi ne ka zama mai bin aƙidar Katolika, sai ka zama malami, daga nan sai ka zama Bishop, sai Archbishop daga nan sai Cardinal."
"Ɗaya daga cikin waɗannan Cardinal ɗin ne ake zaɓa domin zama fafaroma. Mace ba ta da ikon taka ko ɗaya daga cikin waɗannan matakai. Mace za ta iya zama mai hidima a coci, za ta iya taimaka wa malamin ɗarikar katolika amma ita ba za ta iya zama malama ba. Wannan ne tsarin a tsawon dubban shekaru. Babu wanda zai iya canza wannan tsari ko da fafaroma ne," in ji farfesa Cladson Xavier, malami a Kwalejin Loyola ta mabiya addinin Kirista da ke Indiya.
Fafroma Francis ma ya jaddada hakan ga manema labarai lokacin da yake kan hanyarsa a jirgin sama bayan wata tafiya da ya yi a shekarar 2016.
An sha yi masa tambaya kan ko mace za ta iya zama fafaroma. Yakan bayar da amsa cewa "Fafaroma John Paul II ya fayyace komai game da hakan. Ba za a iya canzawa ba." An sake tambayarsa kan ko babu yadda za a yi a canza, ya ce "Abin ke nan, in dai ka karanta dayanin Fafaroma John Paul II."
Bayanin da Fafaroma Francis ke inkiya da shi na ƙunshe ne a wata takarda da Fafaroma John Paul II ya rubuta a shekarar 1994.

Asalin hoton, Getty Images
John Paul ya rubuta wasiƙa zuwa ga malaman bishop-bishop na ɗariƙar Katolika kan cewa zama babban malamin katolika abu ne na maza kawai, kuma ya bayar da hujjojin hakan.
Fafaroma Paul VI ya taɓa rubuta wa shugaban cocin Ingila, Dr FD Cogan game da sanya mata cikin manyan malaman cocin Ingila.
A cikin wasiƙar, Fafaroma Paul VI ya ce "bayanan Littafi mai tsarki ya nuna cewa, Yesu ya zaɓi sahabbansa ne daga cikin maza kawai.
A tasa wasiƙar, Fafaroma John Paul II ya ambato hakan sannan ya ce maza ne kawai ake bari su zama manyan malamai.
Fafaroma John Paul II ya ƙara bayar da wata hujja mai ƙarfi. Ya rubuta a cikin wasiƙarsa cewa "Nana Maryam, Mahaifiyar Yesu, ba ta zamo manzo ko kuma mai wa'azi ba.
"Duk da cewar ba a amince mata su zama malamai ko masu wa'azi ba, ba yana nufin cewa an ƙasƙantar da su ko an nuna musu wariya ba ne. Sai dai a ce wani tsari ne na Allah ga ɗan'adam a doron ƙasa."
A ƙarshe, Fafaroma John Paul II ya rubuta a wasiƙarsa cewa "Domin kawar da duk wasu shakku a kan tsarin cocin, Ina tabbatar muku cewa Coci ba ta da hurumin tabbatar wa mata matsayin malamai, kuma wajibi ne duk mabiya su yi biyayya ga wannan ƙa'ida."
Rawar da mata suka taka a rayuwar Yesu

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da ya zanta da BBC game da wannan daga fadar Vatican, shugaban sashen harshen Tamil na gidan rediyon Vatican, Selvaraj, ya ce wannan ce al'adar cocin tun daga zamanin Yesu.
"Batun zaɓen maza a matsayin masu wa'azi abu ne da ya samo asali tun lokacin rayuwar Yesu. Duk da cewa akwai mata a cikin mabiya Yesu a wancan lokacin, amma ya zaɓi sahabbai 12 maza ne kawai," in ji Selvaraj.
To amma littafin Injila ya nuna cewa akwai mata da yawa waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a rayuwar Yesui, in ji Gladson Xavier. "Musamman akwai mahaifiyarsa, Maryam, wadda aka ambata kuma aka girmama a cikin littafin Bible. Sai kuma Martha da kuma Mary ta Bethany waɗanda su ma an ambace su kan rawar da suka taka a lokacin rayuwar Yesu," in ji shi.










