Mene ne ya yi ajalin fafaroma Francis kuma wace wasiyya ya bari?

Fafaroma Francis shi ne ɗan asalin nahiyar Amurka na farko da ya jagoranci cocin Katolika

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis shi ne ɗan asalin nahiyar Amurka na farko da ya jagoranci cocin Katolika
Lokacin karatu: Minti 4

Cocin Vatican ya sanar da rasuwar shugaban majami'ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.

A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.

Fafaroman ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya, inda a baya ya shafe makonni a wani asibiti, inda aka bayyana cewa yana fama da sanyin haƙarƙari mai tsanani.

A lokacin da aka naɗa shi a fafaroma, ana kallon Francis a matsayin mai sassaucin ra'ayi.

Ya yi ƙoƙarin sassauta ra'ayin cocin kan abubuwan da suka shafi rabuwar aure, da auren masu jinsi ɗaya sannan kuma ya yi ƙoƙarin ganawa da jagororin wasu addinan na daban, sai dai bai yi ƙoƙarin sauya koyarwar cocin ba na asali.

Akasarin shekarun jagorancinsa, cocin ya sha suka kan zarge-zargen cin zarafin yara ta hanyar lalata, inda ya yi kira da a ɗauki matakai masu ƙwari wajen magance batun rufa-rufa, sai dai wasu na ganin cewa bai yi abin da ya dace ba wajen ganin an hukunta jagororin da suka ƙi bayar da rahoton malaman katolika da aka samu da cin zarafin yara ta hanyar ba.

Mene ne ya yi ajalinsa?

Fadar Vatican ta sanar da cewa bugun zuciya da kuma mummunan ciwon zuciya ne suka yi ajalin jagoran mabiya darikar Katolika, Fafaroma Francis.

Wata sanarwa daga daraktan sashen lafiya da tsaftar muhalli na Vatican ta ce "fafaroma ya samu bugun zuciya sannan ya shiga dogon suma daga nan kuma sai zuciyarsa ta daina aiki ta yadda ba za a iya farfaɗo da ita ba."

Rahoton ya nuna cewa dama Fafaroma Francis na da tarihin lalurar hanyar shaƙar iska mai tsanani wadda ƙwayoyin cutar bakteriya masu haddasa cutar lumoniya suka haifar masa, sai kuma hawan jini da kuma ciwon suga nau'i na biyu.

Sanarwar rasuwarsa daga Vatican

Da safiyar Litinin ne ɗaya daga cikin jagororin cocin ya sanar cikin jimami game da rasuwar ta Fafaroma Fraincis, inda ya ce: "Ya ku ƴan'uwana, cikin alhini, ina sanar da ku game da rasuwar Babanmu a addini, Francis.

Da misalin ƙarfe 7:35 na wannan safiya (Agogon Vatican), Bishop ɗin Roma, Francis ya koma ga mahalicci. Ya sadaukar da rayuwarsa baki ɗaya wajen bauta wa ubangiji da kuma coci."

"Ya koya mana bin littafi mai tsarki sau da ƙafa, da karsashi da kuma soyayya a fadin duniya, musamman ga wadanda ke cikin talauci da kuma wadanda aka tauye."

"Cikin godiya mai tarin yawa kan matsayinsa na manzo daga Yesu, mun miƙa ruhin Fafaroma Francis gare ka, kasancewarka mai matuƙar rahama maras iyaka."

Wasiyyar da fafaroma ya bari

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga cikakkiyar wasiyyar Fafaroma Francis:

"Yayin da rayuwata a wannan duniya ke zuwa karshe, kuma nake da kyakkyawan zato game da (fara)rayuwa ta har abada, zan bayyana wasiyyata ta karshe, musamman game da inda za a binne ni.

"A tsawon rayuwata, da lokacin da nake wa'azi a matsayin fasto da kuma bishop, na miƙa amanar rayuwata ga mahaifiyar ubangiji, budurwa Maryam mai albarka. A saboda haka nake son a binne gawata - yayin da take jiran ranar tashin ƙiyama - a Cocin Papal Basilica of Saint Mary Major.

"Ina son ya kasance rayuwata ta duniya ta zo karshe ne a wannan muhalli na Maryamu, inda a kodayaushe nakan tsaya na yi addu'a a farko da kuma ƙarshen duk wata tafiya ta ibada, inda gaba-gadi nakan miƙa duk wata niyyata ga Uwa Tsaftatacciya, tare da miƙa godiya gare ta bisa kyakkyawar kulawarta.

"Ina son a shirya kabarina a filin da ke gefe tsakankanin Cocin Pauline da Cocin Sforza da ke Basilica, kamar yadda yake a zanen da na haɗo da shi.

A yi kabarin daga kasa; sassauka ba tare da wani ado ba, a rubuta: Franciscus kawai.

"Wani taliki ne zai biya kuɗin jana'izar, wanda na riga na tsara za a tura kudin ga cocin Papal Basilica of Saint Mary Major. Na riga na bayyana tsare-tsaren da za a bi ga Cardinal Rolandas Makrickas, na Cocin Liberian Basilica.

"Allah ya saka wa duk waɗanda suka nuna min ƙauna da kuma waɗanda suka yi min addu'a da alkhairi. Na sadaukar da wahalar da na sha a ƙarshen rayuwata ga zaman lafiya da mutanen da suka haɗu kan tafarki ɗaya."

Marigayi Fafaroma Francis ya yi ƙoƙarin kawo sauye-sauye masu dama ga mabiya ɗariƙar katolika, amma ya fi samun goyon baya daga masu ra'ayin mazan jiya.

Shi ne Fafaroma na farko daga nahiyar Amurka, kuma na farko daga ɓarin duniya na kudu.

Ba a taɓa samun wani fafaroma daga wata nahiya ba bayan Turai, tun bayan mutuwar Fafaroma Gregory III wanda aka haifa a Syria a shekarar 741.

Magabacinsa, Fafaroma Benedict XVI shi ne fafaroma na farko da ya yi ritaya daga kan muƙamin don ƙashin kansa a tsawon shekaru 600.