Balaguro 10 da Fafaroma Francis ya yi a ƙasashen Afirka da saƙonnin da ya kai musu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isidore Kouwonou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
- Lokacin karatu: Minti 5
A yunƙurinsa na sasanta rikice-rikice, da sauya rayuwar al'umma, Fafaroma Francis ya ziyarci sassan nahiyar Afirka da dama kafin rasuwarsa.
Fafaroman da asalin sunansa shi ne Jorge Mario Bergoglio, ya rasu ranar Litinin yana da shekara 88 da haihuwa sakamakon bugun jini da ya kwana biyu yana fama da shi.
An naɗa shi a muƙamin fafaroma a watan Maris na shekarar 2013, bayan Fafaroma Benedict XVI ya yi ritaya.
Fafaroman ya ziyarci Afirka sau biyar a rayuwarsa, inda ya je ƙasashe 10 bisa dalilai daban-daban.
Ziyararsa ta ƙarshe ita ce a 2023 lokacin da ya je Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Sudan.
Ga yadda ziyarar tasa ta kasance a ƙasashe 10 da ya je.
1. Kenya: A kawar da tsoro

Asalin hoton, Getty Images
A Nairobi, wuri na farko da ya fara ziyarta a Afirka, ya soki yadda masu arziki ke zaune da talakawa, yana mai cewa abin kunya ne ga al'umma gaba ɗaya.
"Ku jajirce game da imaninku, kada ku ji tsoro" shi ne saƙon da ya bar wa 'yan Kenya lokacin ziyarar tasa, inda kuma ya yi kira da a fito da arzikin ƙasa domin hidimta wa 'yan ƙasa marasa ƙarfi.
2. Uganda: Ziyara domin jaje

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ƙasa na da alaƙa mai ƙarfi da cocin Katolika a Afirka.
Ya je ne saboda mutanen da aka ayyana a matsayin waliyyai na cocin bayan rasuwarsu, waɗanda aka yi wa laƙbi da Holy Martyrs of Uganda.
Saƙon da fafaroman ya kai wa jama'ar Uganda shi ne: "Ku zama shaiduna".
3. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya: Kyautata fata bayan rikici

Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ce ƙasa ta ƙarshe da ya je a ziyararsa ta farko a Afirka.
Ya je ne domin "ƙarfafa imani da fatan mutanen ƙasar" bayan shafe lokaci cikin rikici.
"Mu tsallaka ɗaya ɓangaren" shi ne saƙonsa a ziyarar, inda ya nemi 'yan ƙasar su manta da tashin hankali, da yaƙi, da talauci kuma su "zaɓi zaman lafiya, da sasanci, da cigaba".
4. Mozambique: Aiki tare don cigaba

Asalin hoton, Getty Images
Mozambique ce wuri na 31 da fafaroman ya ziyarta kuma na huɗu a Afirka.
Ya shawarci mahukuntan ƙasar ta kudu maso gabashin Afirka su "haɗa kai domin cigaba" kuma ya taya cocin Mozambique murna, musamman mazauna Sant'Egidio saboda yadda suka taimaka wajen zaman lafiya.
Yayin ganawa da al'umma a filin wasa na Zimpeto, fafaroman ya jaddada batu kan "fata nagari, da zaman lafiya, da sasanci" a ƙasar da ta fuskanci rikice-rikice.
5. Masar: Zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar ta karɓi baƙuncin Fafaroma Francis ne a lokacin da take fuskantar rikicin ta'addanci. Saboda haka, fafaroman na ganin wajibi ne Masar ta zauna lafiya.
Kafin ziyararsa ta biyu a Afirka ranar 28 da 29 ga watan Afrilun 2017, ya samu wasiƙun gayyata huɗu, ciki har daga Shugaban Masar Abdel Fatah Al-Sisi da shugabannin cocin gurguzu, da babban limamin Masar.
Ya jagoranci taron neman zaman lafiya na ƙasashen duniya a jami'ar Azhar.
Ya kuma yi kira ga shugabannin ƙasar da su ci gaba da yunƙurin neman zaman lafiya a yankinsu na Gabas ta Tsakiya.
6. Morocco: Ƙarfafa zumunci tsakanin Musulmi da Kirista

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon gayyatar da Sarki Mohammed VI ya yi masa, Fafaroma Francis ya je Morocco daga 30 zuwa 31 na watan Maris ɗin 2019.
Yayin balaguron, fafaroma ya shawarci al'ummar ƙasar da kada su ji tsoron bambancin ra'ayi, su yi amfani da hakan wajen inganta zamantakewa.
A cewarsa, ya kamata addinai su zama sanadiyyar yaɗa zaman lafiya, da adalci, da kare halittu, da kuma kare mutuncin ɗan'adam.
Kazalika, ya yi magana kan ƙaura yayin wannan ziyara.
7. Madagascar: Shuka zaman lafiya da fata nagari

Asalin hoton, Getty Images
A birnin Akamasoa, wanda mai wa'azin coci Vincentian Father Pedro Opeka ya kafa wanda kuma fafaroman ya san shi a Argentina, Francis ya nemi manyan limaman Katolika su zama "masu shuka zaman lafiya da fata nagari".
Kafin haka, Francis ya shafe kwana biyu a Antananarivo, babban birnin Madagascar.
8. Mauritius: Fifita tattaunawa tsakanin addinai

Asalin hoton, Getty Images
Shekara 30 bayan ziyarar Fafaroma John Paul II, Fafaroma Francis ya je Mauritius a watan Satumban 2019, inda ya jaddada buƙatar "tattaunawa tsakanin addinai da kuma abota" da ke tsakanin shugabannin addinai.
Yayin taron addu'a da aka yi a kushewar Shrine of Mary Queen of Peace, fafaroman ya saka wa mutane da dama albarka.
9. Sudan ta Kudu: Kiran haɗa kan ƙasa

Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma ya haɗu da mahukuntan Sudan ta Kudu a birnin Juba, a gefe guda kuma ya gana da shugabannin cocin Angilika da cocin Scotland.
Ya yi addu'a tare da al'ummomin biyu.
Babban abin da ya fi fitowa fili a ziyarar shi ne ganawar da ya yi da 'yan gudun hijira a Juba.
Ya shawarci matan Sudan ta Kudu su zama "masu shuka irin sabuwar Sudan ta Kudu maras tashin hankali, dunƙulalliya kuma mai zaman lafiya."
10. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo: 'A daina zalintar Afirka'

Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo kamar "dutsen demon ce" a Afirka, amma ta zama "wurin tashin hankali, da fitina, da talautar da mutane," kamar yadda fafaroman ya bayyana a birnin Kinshasa a watan Fabrairun 2023.
Yayin ziyarar, fafaroma ya ja hankalin masu kallon Kongo da ma Afirka baki ɗaya a matsayin yankinsu. "Abin ya isa haka! Ku daina zalintar Afirka!", in ji shi.
Ya haɗu da mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita a gabashin ƙasar. "Saboda su nake cewa yaƙi ya isa haka, kada a cire haso, a yi ƙoƙarin sasantawa da fata nagari."











