Abin da jagororin Katolika na Arewacin Najeriya ke cewa kan rasuwar Fafaroma

..

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban babban cocin Najeriya da ke Abuja Archbishop Ignatius Kaigama da kuma shugaban cocin Katolika na Sokoto Bishop Mathew Hassan Kukkah
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Litinin ne fadar Vatican ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis.

Marigayin wanda ya yi shekara 88 a duniya ya rasu ne sakamakon fama da cutar bugun jini da bugawar zuciya bayan jinyar da ya yi ta tsawon makonni, a cewar fadar.

Mabiya ɗariƙar katolika da dama a faɗin duniya na ci gaba da alhinin mutuwar Fafaroman, wanda ya kasance babban jagoran addininsu na tsawon shekara goma 12.

Mabiya ɗarikar katolika a Najeriya ma ba a bar su a baya ba, inda su ma suka shiga jimami na rashin babban jagoransu a duniya.

Bishop Mathew Hassan Kukkah, shugaban ɗarikar katolika na shiyyar Sokoto, ya shaida wa BBC cewa duniya ta yi babban rashi ba mabiya ɗarikar kaɗai ba.

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

'Fafaroma ya nuna wa mutane hasken ubangiji'

Shugaban cocin Katolika na Sokoto Bishop Mathew Hassan Kukkah
Bayanan hoto, Shugaban cocin Katolika na Sokoto Bishop Mathew Hassan Kukkah

Bishop Kukah ya ce Fafaroma Francis ya kasance mutum da baya nuna bambanci, ya ɗauki kowaye a matsayin ɗaya.

"Bai nuna bambanci ga Musulmi da Kirista da Hindu da kuma ƴan addinin Buddha ba," a cewar Kukah.

Ya ce babban darasi da za a ɗauka a rayuwar Fafaroma shi ne cewa Allah ne ya halicci kowa kuma kada su yarda addini ya raba su.

"Duniya tana cikin bakin ciki da rashin Fafaroma Francis.

Bishop Kukah ya ƙara da cewa marigayin ya nuna shi mutum ne mai son gaskiya.

"Francis ya nuna wa duniya wata fuska ta addinin Kirsita.

"Duk inda aka samu rashin jituwa a yankunan duniya ya fito ya faɗi gaskiyar cewa yaƙi ba abu ne mai kyau ba, musamman a yaƙin Ukraine da kuma na Gaza," in ji shi.

Shugaban ɗarikar Katolikan na shiyyar Sokoto ya ce abin da za a koya wajen Fafaroma shi ne ya nuna cewa kada mutum ya ce addininsa zai yi nasara ba tare da nuna halaye masu kyau ba.

Ya ce Fafaroma Francis ya zauna da mutane lafiya a tsawon rayuwarsa, musamman mabiya sauran addinai.

''Babban darasi da za mu koya daga rayuwar Francis musamman a Najeriya shi ne mu guji zalunci da yaudara da kuma bin gaskiya da zaman lafiya da kowa," in ji Bishop Mathew Kukah.

'Mun yi babban rashi na Fafaroma'

Shugaban babban cocin Najeriya da ke Abuja Archbishop Ignatius Kaigama
Bayanan hoto, Shugaban cocin Katolika na Abuja da ke Abuja Archbishop Ignatius Kaigama

Shi ma, babban limamin ɗarikar Katolika na Abuja, Archbishop Ignatius Kaigama ya bayyana marigayi Fafaroma Francis a matsayin mutum mai son zaman lafiya - wanda ya rungumi kowa ciki har da Musulmi da mabiya addinin Buddha da kuma sauran addinai.

Ya ce duk da bai samu ziyartar Najeriya ba kamar yadda ya yi alkawali, amma ana matukar sonsa a ƙasar wadda ke da mabiya darikar fiye da miliyan 30.

"Duniya baki-ɗaya na cikin bakin cikin rashin Fafaroma Francis. Muna alhinin rashin sa.

"Fafaroma ya kasance uba ne ga ƴan katolika, uba ne ga sauran Kiristoci na duniya har ma ga Musulmai saboda yadda yake mutunta su. Babu inda zai je bai neme su ba," in ji Archbishop Kaigama.

Ya ƙara da cewa suna fatan Fafaroman da zai gaji Francis ya kasance mai tsarki da kuma wanda zai rungumi kowa da kowa.