Wane ne ya rubuta littafin Injila mai tsarki?

Asalin hoton, Getty Images
A wajen mabiya Katolika akwai littafi mai tsarki 73. A wajen 'yan furotestan akwai 66. 'Yan cocin gurguzu (Orthodoc Church) kuma na ganin akwai 78.
Ana magana ne kan litattafan da aka fi sayarwa a tarihin ɗan'adam baki ɗaya, wato littafin Injila mai tsarki - ko kuma Bible a Turance - wanda gamayyar rubuce-rubuce ne da aka fassara zuwa kusan harsuna 3,000, sannan aka sayar da kusan kwafi biliyan 3.9 a faɗin duniya.
Amma abin tambayar a nan shi ne, wane ne ya rubuta waɗannan litattafan? Ganin cewa tsofaffin abubuwa ne, wasu ma sun girmi lokacin da aka fara wallafa littafi, da wuya a iya gano ainahin wanda ya rubuta su.
Abin da za a iya farawa da shi shi ne duba ma'aunin da za a yi amfani da shi na tantancewa; a ƙa'idojin da suka shafi addini ko kuma na kimiyya da ɓangaren koyo da koyarwa.
"Batu ne mai sarƙaƙiya saboda akwai ruwayoyi biyu. Akwai wanda aka fi amincewa da shi kuma har yanzu shi ne kan gaba, saboda muna da mazahabar da ta fi alaƙa da Kiristanci kuma da mutanen da ke koyonta kawai saboda suna son zama masu wa'azin Kirista a yankunansu. Wannan ita ce ruwaya ta gargajiya," kamar yadda mai nazarin addinin Kirista kuma masanin tarihi Farfesa Gerson Leite de Moraes na Jami'ar Mackenzie Presbyterian ya yi bayani.
A cewarsa, nazarin addini ya danganta ne kacokam kan yadda masu wa'azi ke buƙatar su "tabbatar cewa litattfan nan da gaske Allah ne ya saukar da su ta hannun Yesu".
Ya ƙara da cewa: "A gefe guda kuma, ƙwararru a fannin koyarwa ba su fiya damuwa da wannan ba, inda suka fi mayar da hankali kan nazartar rubuce-rubucen a mahangar tarihi."
A wannan halin, za mu iya fahimtar cewa litattafan farko na Injila da aka tattara a matsayin Pentateuch ko kuma Attaura ta Yahudawa, an fara rubuta su ne tun shekara 1,000 kafin haihuwar Yesu.
Su ne: Genesis, Exodus, Leviticus, Numbers, da Deuteronomy - litattafan da suka bayar da labarin halittar duniya har zuwa mutuwar Annabi Musa.
Rassa

Asalin hoton, Getty imges
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar wasu ruwayoyin na addini, waɗannan litattafai biyar mutum ɗaya ne ya rubuta su - wato Annabi Musa.
"Da nake karanta littafi da waƙoƙin Haroldo de Campos (1929-2003), na lura akwai maganganu biyu. Yahudawa na cewa mutumin da ya rubuta Attaurah shi ne Annabi Musa. Muna karanta ta ne kamar muna jin muryar Annabi Musa, kuma hakan na da tasiri sosai kan mabiya," in ji Farfesa José Luiz Goldfarb na Jami'ar Pontifical Catholic University da ke Sao Paulo, kuma shugaban cibiyar Yahudawa ta A Hebraica.
Sai dai kuma masu amfani da kimiyya sun yi watsi da maganar marubuci ɗaya na waɗannan litattafai.
"Bayan nazari ta mahangar addini, kenan an shafe shekara 600 ana rubuta su," a cewar Farfesa Goldfarb.
"Wannan ce matsayar da Haroldo ya ɗauka bayan nazartar Injila, da kayayyakin tarihi, da falsafa, da kuma waƙoƙi."
Ya ce nazari cikin tsanaki na litattafan za su bayar da damar rarraba su cikin rukuni ɗaya saboda irin salonsu, da ɗaiɗaikun kalmominsu waɗanda za a iya alaƙantawa da marubuta daban-daban a lokuta daban-daban.
"Abu ne mai wahala a yi magana kan marubutan saboda sun ɓace a tarihi. Binciken masana koyo da koyarwa ya nuna litattafan sun kai shekara 2,700 zuwa 3,000, ko ma sama da haka, saboda an yaɗa su ne da baki," a cewar Rabbi Uri Lam na majalisar Yahudawa ta Templo Beth-El a Sao Paulo.
A cewarsa, an shigar da litattafan a matsayin Attaurah tun daga ƙarni na huɗu kafin Yesu.
"Amma ko a nan ma akwai maganganu da yawa kuma ba zai yiwu a ce ga wanda ya fi gaskiya ba," in ji Lam.
Adabi a cikin Injila

Asalin hoton, Reuters
Wani mai bincike Moraes na ganin ganin cewa an rubuta litattafan bayan kafa ƙasar Isra'ila hakan ya bayar da ma'ana, sama da a ce an rubuta su a lokutan labaran da aka ruwaito a cikinsu - kamar lokacin da Yahudawa suka gudu daga Masar a ƙarƙashin jagorancin Annabi Musa.
"Ku duba yadda mabiyansa suka dinga gararamba a daji suna neman tsira. Abin da za su fi nema a lokacin shi ne hanyar da za su tsira da rayukansu, ba wai rubuta littafi ba. Abin da za su fi mayar da hankali shi ne tattara dakarun da za su ƙwato garinsu...Babu wanda zai damu da rubuta littafi," a cewarsa.
Akwai yiwuwar hakan ya faru ne kawai bayan kafa wata al'umma, a cewarsa.
Amma duk da haka wasu labarai ne daga ɓangarorin adabi daban-daban waɗanda marubuta daban-daban suka rubuta, aka haɗa su wuri guda.
Wani mai binciken litattafan addini, Thiago Maerki, Jami'ar Tarayya ta Sao Paulo na ganin ya kamata a dinga amfani da hanyoyin nazari na zamani domin gano wani abu game da tsofaffin litattafai.
Sabon Alƙawari (New Testament)
Za kuma a iya saka mahangar adabi cikin nazarin Gospels, litattafai huɗu da suka bayar da labarin Yesu kuma ake alaƙantawa da Matheu, da Matthew, da Mark, da Luke, da John ne.
Wani mai bincike kan tarihn Kiristanci a jami'ar Pontifical Gregorian University da ke birnin Roma na Italiya, Mirticeli Medeiros, ya ce tabbas waɗannan mutum huɗun ne suka rubuta litattafan.
"Game da rubutun Gospel, wannan babu saɓani a kai a binciken da baya-bayan nan. Musamman idan aka tuna cewa biyu daga cikin marubutan Matthew da John sahabban Yesu ne. Sauran biyun, Mark da Luke, sun harhada labaran ne daga wajen sauran sahabban," kamar yadda ya bayyana.
Sai dai Maerki ya fahimci bambancin salo da ke tsakanin waɗannan litattafai huɗu.
"Ana ganin Mark marubuci ne da ke da salon kai-tsaye, mai sauƙi. Salon John kuma na da wuyar sha'ani, kalamai masu harshen damo da kuma misalai da yawa. Shi kuma Luke yana da salo mai ɗan sauƙi amma cike da ilimi," in ji shi.
Game da Tsohon Alƙawari, akwai tambayoyi da yawa sama da amsarsu a fagen rubutunsa.
Akwai tabbaci cewa duka litattafan an fara samar da su ne kusan shekara 30 zuwa 40 bayan mutuwar Yesu. Moraes ya ce "abin da aka fi tunani shi ne waɗannan sunaye al'adu ne suka tabbatar da su".
"Babu sunan marubuta ko kanu a Tsohon Alƙawari (Old Testament)," a cewar mai binciken.
Wasiƙu
Idan ana maganar Sabon Alƙawari ne, dole ne sai an ambaci gudumawar Paul, sahabin Yesu da ya rubuta wa garuruwan Kiristoci da yawa wasiƙa.
"Kamar yadda sunansa ya nuna, Paul ne ya rubuta wasiƙun nan da kuma mabiyansa. Wasiƙa zuwa ga Timothy, ana tunanin sai bayan Paul rasuwar Paul aka rubuta ta, dalili da ya sa kenan masu nazari ke cewa sunanta Deutero-Pauline," kamar yadda Medeiros ya yi bayani.
"Amma kuma akwai cecekuce kan wasiƙun da ake alaƙanta wa Peter, waɗanda alamu ke nuna cewa ba shi ne ya rubuta su ba. Da ta Paul zuwa ga Yahudawa, wadda da alama ɗaya daga cikin mabiyansa ya ƙarasa ta."
An yi imanin cewa Paul ne mutum na farko da ya fara rubuta wani abu kan Yesu daga shekaru 57 ko 58.
"Abin tambaya a nan shi ne ko yana sane cewa yana rubuta litafi mai tsarki ne. Ƙila ba lallai haka abin yake ba a wurinsa," a cewar Moraes.











