Mene ne hukuncin sahur ga wanda zai yi azumi?

.

Ma’anar sahur ita ce cin abinci a ƙarshen dare ga wanda ya yi niyyar yin azumi, lokacin shi ne gabanin fitowar alfijir.

Sahur abu ne da addinin Musulunci ya ba da umarnin a yi, sai dai umarnin ba ya nufin wajibci, wato tamkar wanda zai iya samar da hukunci a kan wanda bai yi ba.

A'a, umarnin an yi shi ne ta fuskar ‘mustahabbi’ wato an so duk wanda zai yi azumi ya yi hakan, amma rashin yin, babu laifi a ciki.

Mene ne alfanun da ke cikin sahur? Me kuma addini ya ce a kan sahur?

Waɗannan na cikin tambayoyin da muka yi wa Malam Abu Jabir Abdullah Musa (Penabdul).

Malam ya ce maganar yin sahur ta tabbata, a cikin wani hadisi da Jabir ɗan Abdallah ya ruwaito Annabi na cewa “duk wanda yake so ya yi azumi, to ya yi sahur da wani abin,”.

Wannan na nuni da cewa lokacin sahur, ba sai mutum ya cika ciki da abinci ba, ko yaya ne kuka ci kamar yadda aka umarta.

Mutane sun sha bamban, wani idan ya yi sahur da abinci, cikinsa yakan lalace.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Irin wannan, in ji Mallam Abu Jabir, ai ba za ka matsa musu sai sun yi sahur, sun cika cikinsu ba

A cewarsa, komai ƙanƙantar abin da suka ci a cikin cikinsu lokacin sahur, za a kalle shi a matsayin sahur.

Wasu kuma idan ba su ci sun ƙoshi ba, to ji za su yi tamkar ba su yi sahur ba, ko kuma za su wuni a galabaice.

Ya ce ko a ɓangaren masana lafiya haka lamarin yake, waɗanda suka fi buƙatar sahur, su ne waɗanda ake so dole su yi hakan, waɗanda ba sa buƙata, ko ruwa da tsagin dabino suka ci za a kalle hakan a matsayin sahur.

“Ya tabbata a hadisi cewa Annabi ya wuce da azumi bai yi sahur ba, sai dai wasu malaman na kallon haka tamkar wata keɓaɓɓiyar baiwa ce tasa shi kaɗai, domin idan aka ce kowa ya yi hakan wani ba zai iya azumin ba."

Hadisi ya tabbata cikin Bukhari da Muslim, Annabi Muhammad yana cewa “Ku yi sahur saboda a cikin sahur akwai albarka,” in ji Malam Abdullah.

To wannan albarkar ai babu wanda zai so ya yi rashin ta, a cewarsa, kuma ya tabbata cewa lokacin sahur, lokaci ne na karɓar addu’a, mutum yana kammalawa zai iya ɗaga hannu ya yi addu’a wadda ake sa ran karɓaɓɓiya ce.

Babu laifi ga waɗanda suka ci abinci misalin ƙarfe ɗaya ko biyun dare, kuma sai suka ji ba su da buƙatar sake cin abinci a lokacin sahur, to ga waɗannan babu komai idan sun wuce da azumi, kamar yadda malamin ya yi bayani.

Ya ƙara da cewa hujjar da ta sa aka ce mutum ya ci wani abu lokacin sahur, ita ce Musulunci na ƙoƙarin kare lafiya da dukiyoyin mutane ne, babu yadda za a yi ya sanya wa mutum abin da zai zamar masa mushaƙƙa.