Hotunan halin da ake ciki a Birnin Gaza yayin da Isra'ila ta tsananta hare-hare

A young girl lies on a stretcher as she is pulled away from a destroyed building but emergency workers. She grips the side of the stretcher and looks disconsolate.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila ta tsananta ruwan wuta a kan birnin Gaza yayin da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa an ƙaddamar da "gagarumin samame" a Zirin. Ministan tsaro na Isra'ila, Israel Katz ya wallafa a shafinsa na X cewa "Gaza na ci da wuta"
Lokacin karatu: Minti 4
Smoke billows as Israeli airstrikes destroy the al-Ghafri tower in Gaza City. The building can be seen collapsing as giant clouds of dust and smoke envelop the surrounding neighbourhood. The minarets of a mosque can be seen to the right of the image.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Hayaƙi ya turnuƙe yayin da Isra'ila ta kai hari ta sama kan dogon ginin al-Ghafri a Birnin Gaza. Netanyahu ya ce Birnin Gaza ne wuri na ƙarshe da Hamas ke da ƙarfi kuma a yanzu Isra'ila ta ci alwashin karɓe iko da shi, sai dai wannan ƙuduri nata ya janyo Allah-wadai daga ƙasashen duniya
A long queue of traffic is at a standstill on a coastal road in Gaza, as people mill about on foot around the vehicles. The seashore can be seen to the left of the picture and tower blocks in the far distance.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan ne lokaci mafi tsanani da Isra'ila ke tarwatsa al'ummar Gaza tun bayan sabbin hare-haren da ta tsananta a kan birnin daga watan da ya gabata
Man fleeing with his children on foot. He carries a sleeping child in a car chair slung across his shoulders, and has a carpet tied around his back

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Dubban iyalai ne ke ƙoƙarin komawa kudancin Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da ruwan wuta
Smoke rises from a tower block and flames can be seen from a large explosion in the upper storeys. Tents and other buildings can be seen in the foreground.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, An kai hare-hare ta sama kan dogayen gine-gine da dama a ƴan kwanakin nan bayan sojojin Isra'ila sun umarci al'umma su fice
An Israeli military vehicle drives past a border fence amid a cloud of sand and dust

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren da Isra'ilar ta ƙaddamar kan Birnin Gaza na zuwa ne yayin da sakataren harkokin waje na Amurka Marco Rubio ya tattauna da Firaiminista Netanyahu. Wata hukumar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata ta bayyana cewa bincikenta ya tabbatar cewa Isra'ila ta yi kisan ƙare-dangi kan Falasɗinawa a Gaza - abin da Isra'ila ta musanta
A girl wearing what appear to be colourful blue pyjamas with red and white spots walks across rubble barefoot as displaced Palestinians salvage items from the ruins of the al-Ghafri tower after it was destroyed by Israeli strikes.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Rudunar tsaron Isra'ila (IDF) ta yi ƙiyasin cewa Falasdinawa kimanin 350,000 sun fice ya zuwa yanzu, duk da cewa akwai dubban ɗaruruwa da ake da yaƙinin cewa har yanzu suna a wurin
Smoke billows folllowing an explosion and the ruins of dozens of buldings can be seen in all directions

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ruwan wuta na zuwa ne bayan dogon lokaci na barazanar kai gagarumin samame ta ƙasa zuwa cikin birnin - Hukumomin Falasɗinawa sun ce yawan waɗanda suka mutu na ƙara yawa
Palestinians move toward central Gaza using vehicles, horse carts, and travelling on foot. Vehicles can be seen at night with belongings piled high on their roof racks and heavily loaded trucks

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, "Rundunar sojin Isra'ila ta ayyana babban titin al-Rashid a matsayin hanya ɗaya tilo da aka amince wa fararen hula da ke son ficewa daga birnin su yi amfani da ita. Mazauna sun bayyana yadda ake samun mummunan cunkoso, da dogayen layukan ababen hawa da kuma jinkiri, inda iyalai da dama suka maƙale a bakin hanya yayin da ake ci gaba da ruwan wuta ta sama," in ji wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abualouf
Map of Israel and Gaza showin newly designated 'humanitarian area' in yellow and an IDF designated 'dangerous combat zone'
Bayanan hoto, Rundunar sojin Isra'ila ta umarci dukkanin mutanen da ke Gaza "su fice nan take" zuwa wani wurin da aka amince da shi a matsayin "wurin jin-ƙai" da ke kudu