Shin fenaritin da aka bai wa Arsenal ta dace?

Asalin hoton, Getty Images
Mutane ne ta yin tsokaci kan bugun fenaritin da aka bai wa Arsenal a wasanta da Bayer Leverkusen a gasar Zakarun Turai na Champions League da aka buga a daren ranar Laraba.
Arsenal ta yi amfani da bugun fenaritin wajen farke ƙwallo ɗaya da masu masukin baƙin suka zura mata.
Noni Madueke ne ya faɗi a cikin da'ira bayan haɗa jiki da Malik Tillman.
Duk da cewa an duba har da na'ura, lafari ya tabbatar cewa tabbas bugun fenariti ne, duk da ƙorafin da ƴan wasan Bayer suka riƙa yi.
Dama tun bayan da ya shiga fili, Madueke ya riƙa jan ƴan wasan Bayer a guje cikin filin.
"A nawa ganin, Madueke ya faɗi ne a hankali, amma tabbas an haɗa jiki, saboda haka na'ura na da ƙwaƙƙwarar hujjar cewa akwai fenariti," in ji Matt Upson, tsohon ɗan wasan baya na Arsenal.

Asalin hoton, Getty Images



