Yadda Vinicius ya fuskanci nuna wariyar launin fata sau 20 a shekara 8 a Madrid
- Marubuci, Guillem Balague
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport columnist
- Lokacin karatu: Minti 4
Mai sharhi kan harkokin wasanni ɗan Spain Guillem Balague ya halarci wasan cike-gurbi tsakanin Real Madrid da Benfica a filin wasa na Estadio da Luz a birnin Lisbon a ranar Talata da ta gabata, inda aka tsayar da wasan na kusan minti 10 bayan Vinicious ya yi zargin an masa kalaman nuna wariya.
Wannan ne karo na 20 da Vinicius ya yi zargin an masa kalaman nuna wariyar launin fata a cikin shekara 8 da ya yi a ƙungiyar Real Madrid.
Balague ya yi sharhi kan me ya sa ɗanwasan mai shekara 25 yake yawan fuskantar matsalar.
Vinicious ya zura ƙwallo a ragar Benfica mai kyau, amma amma maimakon zura ƙwallon ta haifar da farin ciki, sai lamarin ya koma suka da zargin kalaman wariya.
Zuwa yanzu dai Vinicius ya fuskanci kalaman nuna wariya sau 20 a zamansa a ƙungiyar Real Madrid.
Wannan karon ɗanwasan ya zargi ɗan asalin ƙasar Argentina Gianluca Prestiani da yi masa kamalam nuna wariyar launin fata.
Sai dai Prestianni ya musanta zargin, sannan Vinicious ya samu goyon bayan fitattun ƴanƙwallo, ciki har da Kylian Mbappe, wanda ya ce ya ji kalmar nuna wariya sau biyar.
Bayan wasan, kocin Benfica Jose Mourinho ya zargi ɗanwasan da janyo wa kansa, musamman kan irin murnar da ya yi bayan zura ƙwallon.
Ya kuma ce ba zai yiwu ƙungiyar Benfica ta zama ƙungiyar nuna wariyar launin fata ba, domin a cewarsa, fitaccen ɗanwasan ƙungiyar a tarihinta, Euseubio ma baƙin fata ne.
A duk lokacin da Vinicious ya fuskanci masu kallo, ana masa kallon girman kai da nuna isa.
Amma kuma ana fassara hakan a matsayin nuna rashin amincewa da nuna wariya da yake fuskanta.
Frantz Fanon ya bayyana a wani littafi da ya rubuta a shekarar 1952 mai suna, Black Skin, White Masks cewa: "dole baƙaƙen mutane su yi ƙoƙari ninki biyu na ƙoƙarin fararen mutane domin su samu karɓuwa."
Wataƙila wannan ne Vinicious ke kallo ya sa yake yawan fushi da ƙara ƙaimi domin nuna ƙwanji, wanda wasu ke ganin yana wuce ƙima.

Asalin hoton, Getty Images and Eurasia Sport Images
Lokutan da aka nuna wa Vinicius wariya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Vini Jnr dai ya zama sha gwagwarmaya sha fama a Spain, inda har a kotu ya bayyana domin bayar da bahasi, sannan an sha dakatar da masu kallo da dama saboda shi.
A watan Oktoban 2021 a wasan Classico a filin wasa na Camp Nou, wani ɗan kallo ya yi masa kalaman wariya bayan an cire shi a wasan. Sai dai ƴansanda ba su samu nasarar gano mutumin ba.
Sannan a watan Maris na 2022, magoya bayan ƙungiyar Mallorca ne suka masa ihun biri, sannan suka ce ya "dauƙi ayaba."
Hukumomin ƙwallo sun nuna ɓacin rai, amma ba a ɗauki wani mataki ba.
A wani shirin wasanni mai suna El Chiringuito a Spain, shugaban ƙungiyar wakilan ƴan wasa na Spain Pedro Bravo, ya yi kira ga Vini da ya "daina yin abu kamar biri," sannan ya riƙa girmama abokan karawarsa.
Daga baya ya janye kalamansa, sannan ya nemi afuwa tare da cewa kwatance kawai ya yi, amma ba a ɗauki wani mataki ba.
A watan Satumban 2022, magoya bayan Atletico Madrid sun masa waƙar nuna wariya, amma ba a ɗauki wani mataki ba.
A watan Janairun 2023, an ga hoton wata ƴar tsana an sagale ta sanye da rigar Vini. An kama mutunen da suka aikata laifin, sannan aka tura su gidan yari, kafin daga baya aka mayar da hukuncin ya zama biyan kuɗin tara.
Lokacin da abin da ya ɗauki sabon salo shi ne a wasan Valencia a watan Mayun 2023, inda Vini ya fuskanci sashen masu kallo da suke masa kalaman ɓatanci.
Daga baya kuma aka nuna masa jan kati bayan ya yi musayar yawu da golan Valencia Giorgi Mamardashvili da ɗanwasan ƙungiyar Hugo Duro.
A watan Yunin 2024, an kulle mutum huɗu bisa samunsu da laifin nuna masa wariya, inda aka yanke musu hukuncin ɗaurin wata takwas da kuma hana su kallon wasa na shekara biyu.
Wasu lokutan ma ana nuna masa kalaman wariya ko da ba ya cikin filin wasan, domin a filin wasa na Mestalla, ana wasa ne tsakanin Atletico Madrid da Inter, amma Real Madrid ta kai ƙorafin an ci zarafinsa.
Sannan a wani wasan bayan kwana biyar, a filin wasan Osasuna an riƙa masa waƙar, "Vinicius sai ya mutu."
A ranar 29 ga Satumban 2024, an kama mutum huɗu da zargin nuna kalaman wariya a kafofin sadarwa ta hanyar ɓoye suna domin cin zarafin ɗan wasan a wasan Madrid da Atletico.
Na baya-bayan nan shi ne watan Fabrairu, a wasan kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Rey tsakanin Real Madrid da Real Sociedad, alƙalin wasa Jose Maria Martinez ya tsayar da wasa saboda nuna wariya.
A lokacin an nuna wa wani ɗanwasan daban ne wariya, amma da na'urar ɗaukar hoto ta zagaya, sai aka ga hango wani yana kwatanta Vini da biri.
A watan jiya, a wasan farko da Alvaro Arbeloa ya jagoranci Madrid, wasu magoya bayan sun nuna wa Jini Jnr wariya, inda hukumar La Liga ta nuna masa goyon baya.
Sai kuma wannan wanda ya faru a birnin Lisbon.
A game da abin da ya sa yake yawan mayar da martani kan masu nuna masa wariyar, ya bayar da amsa a watan Yunin 2024 bayan wasan Real Madrid da Valencia, inda ya ce, "mutane suna ce in daina kula su, wasu na cewa babu abin da zan iya," in ji shi.
"Amma kamar yadda nake yawan faɗa, ina alfahari da cewa waɗanda aka fara yanke wa hukunci a Spain saboda nuna wariya, ni ne na yi sanadi. Wannan nasara ce ta baƙaƙen fata baki ɗaya," in ji shi kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X.













