Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku muhimman labarai da rahotanni daga ko'ina a faɗin duniya na ranar 24 ga watan Disamban 2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Harin ƙunar baƙin wake a massalaci ya yi ajalin mutum bakwai a Maiduguri

    Zulum

    Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an ji ƙarar abin fashewa a wani masallaci a birnin Maiduguri na jihar Borno, wanda zuwa yanzu ya yi ajalin aƙalla mutum 7, sannan wasu da dama suka jikkata.

    Kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai wannan harin, wanda ake kyautata zaton na ƙunar baƙin wake ne.

    Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun fara da jin ƙara mai ƙarfin gaske, daga nan kuma sai baƙin hayaƙi ya turnuƙe masallacin da ke kasuwar Gamborou a jihar a lokacin sallar Magariba.

    Malam Abuna Yusuf na cikin jagororin masallacin, ya shaida wa AFP cewa mutum takwas ne suka rasu.

    Jihar Borno da kewaye na fama da hare-haren masu tada ƙayar baya na Boko Haram, inda suke kai hare-hare a makarantu da wuraren ibada da kasuwanni, duk da yake a 'yan shekarun nan an samu kwanciyar hankali a jihar.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce mutum bakwai ne suka rasu.

  2. Gwamnan Sokoto ya buƙaci Kiristoci su dage da addu'a domin samun zaman lafiya

    Sokoto

    Asalin hoton, Office of the Press Secretary, Government House Sokoto

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi kira ga kiristoci da su dage da addu'o'i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da sauran sassan Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin saƙon gwamnan na bikin kirsimeti zuwa kiristoci, wanda mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar.

    "Duk da tarihin jihar Sokoto na zaman lafiya, amma tana fama da matsalolin tsaro musamman na harkokin ƴanbindiga a gabashin jihar. Mun ɗauki matakai masu muhimmanci domin magance matsalar ta hanyar da ɗaukar jami'an tsaron jiha, da kuma ƙarfafa jami'an tsaron tarayya domin samun ƙarfin gwiwar magance matsalar."

    Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samar da sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Ilela, sannan ya ce ya ƙara alawus ɗin da ake biyan jami'an tsaron da suke aiki a wuraren da ake fuskantar matsalar tsaro.

    Gwamnan ya yi kira ga kiristocin jihar da su yi amfani da bikin kirsimetin domin gudanar da addu'o'i ga jihar domin ta samu zaman lafiya mai ɗorewa.

    Ya kuma yaba da zaman lafiya da ake samu tsakanin ƙabilun da ke zaune a jihar, inda ya ƙara da cewa ana samun cigaba ne kawai idan akwai zaman lafiya.

  3. Mutum 13 sun jikkata bayan harin da Rasha ta kai Kharkiv

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta ci gaba da kai hari Ukraine, inda wani harin ya faɗa cibiyar wutar lantarki da ke kusa da birnin Kharkiv.

    Mutum guda ya rasa ran shi wasu 13 sun jikkata, ya yin da aka dakatar da fannin sufurin ƙasar.

    Sojojin Ukraine sun ce sun kai hari wata masana'anta da ke yankin Tula a Rasha, inda ake haɗa ababen fashewa da samar da jirage marassa matuka da ke kai hari teku, sun kuma kai wani harin a yankin Crimea da Rashar ta mamaye.

    Ministan tsaron Rasha ya yi ikirarin sun karɓe iko Zarichne da ke gabashin yankin Zaporizhzhia na Ukraine.

  4. An kama mutum 50 da ake zargi da laifukan intanet a Ghana

    ...

    Hukumomi a kasar Ghana sun sanar da kama mutum 50 da ake zargi da laifukan intanet.

    Ministan sadarwa Sam Goerge, ya ce ana kyautata zaton maza 46 da mata 3 da aka kama 'yan Najeriya ne.

    Tuni dai aka fara gudanar da bincike kansu.

    Kamen ya biyo bayan samamen da jami'an yaki da laifukan intanet suka kai da tsakar dare a yankin Dawhenya, da hadin gwiwar 'yansandan yankin.

    Laifukan sun haɗa da zamba, da zuba jari na jabu, da kasuwancin zinare na ƙarya da sauransu.

    Wannan na kuma zuwa ne ƴan kwanaki bayan da hukumar kula da ayyukan yin zamba ta intanet ta Ghana ta kama wasu ƴan Najeriya su 32 da ake zargi da aikata laifuka a tsakiyar ƙasar.

  5. Ƴan majalisar dokokin jihar Kano biyu sun rasu

    Kano

    Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa

    Bayanan hoto, Marigayi Aminu Saad Ungoggo

    Ƴan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu sun rasu a kusan lokaci ɗaya sakamakon rashin lafiya.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta.

    Ƴan majalisar da suka rasu su ne Sarki Aliyu Daneji, mai wakiltar Kano Municipal, wanda ya rasu kimanin awa ɗaya bayan rasuwar abokin aikinsa Aminu Saad Ungoggo wai wakiltar mazaɓar Ungoggo.

    Sarki Aliyu Daneji

    Asalin hoton, Ibrahim Adam

    Bayanan hoto, Marigayi Sarki Aliyu Daneji
  6. Fiye da mutum 100 aka kashe a cikin makonni biyu a Sudan - MDD

    Sama da mutane ɗari ne aka kashe a cikin makonni biyu da suka gabata a hare-hare da jiragen yaƙi marasa matuƙa a yankin Kordofan na Sudan.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kaɗu da ƙaruwar amfani da jirage marasa matuƙa da yadda duka sojojin Sudan da kuma dakarun RSF ke yi.

    Wakilin BBC ya ce ɗaruruwan 'yan Sudan ne suka tserewa yankin Kordofan, da tserewa munanan hare-haren da ake kai wa yankin.

    Da yake jawabi gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Mataimakin Sakatare-Janar kan harkokin siyasa - Khaled Khari - ya ce faɗa ya yi ƙamari a Kordofan, wanda a yanzu ya zama wata sabuwar mafarar tashin hankali.

    Ya yi gargaɗin cewa nasarorin da kungiyar ta RSF ta samu na kama karin wasu yankunan na jefa rayukkan fararen hula da ma'aikatan agaji da masu aikin wanzar da zaman lafiya cikin haɗari.

  7. Cambodia da Thailand sun soma tattaunawa don sasanta rikicinsu

    ...

    Cambodia da Thailand sun fara tattaunawa ta kwanaki hudu da nufin sasanta rikicin kan iyaka da ya sake ɓarkewa a farkon wannan wata.

    Suna ganawa ne a lardin Chanthaburi na kasar Thailand, duk da bukatar Cambodia ta yin zaman a wani wurin tsaka tsaki.

    A ranar bakwai ga watan Disamba ne dai aka sake samun ɓarkewar tashin hankali bayan rugujewar wata yarjejeniya da ministan harkokin wajen Thailand ya ce an yi gaggawar shiga wadda Amurka ta tsara.

    Ɓangarorin biyu sun ba da rahoton kai wa juna hari a yau Laraba, amma bayanai daga kowane ɓangare sun nuna cewa dukkansu suna da ƙwarin gwiwa kan sakamakon sabuwar tattaunawar da za a kammala a ranar Asabar.

  8. EFCC ta bankaɗo kadarori 41 na naira biliyan 212 da ke alaƙa da Malami

    Malami

    Asalin hoton, Malami/Facebook

    Hukumar EFCC ta ce ta gano wasu kadarori guda 41 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 212 da ta ce tana zargi mallakin tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ne.

    Jaridar TheCable mai zaman kanta a Najeriya ta ruwaito labarin, inda ta ce daga cikin kadarorin akwai otel-otel da gidajen zama da fulotai da makarantu, sannan ta ce ta gano su ne a Abuja a Kano da jiharsa ta Kebbi.

    Jaridar ta ce hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta gano kadarorin da aka ƙiyasta sun kai na naira biliyan 162,195,950,000 a jihar Kebbi, sai na naira biliyan 16,011,800,000 da Kano, da kuma na naira biliya 34,685,000,000 a Abuja.

    Gwamnatin Najeriya dai na tuhumar tsohon ministan da tuhume-tuhume guda 16 da suka danganci zamba cikin aminci a ake zargin tsohon ministan da ɗansa Abdulaziz Malami.

  9. Jihar New South Wales ta Australia ta amince da mallakar bindiga bayan hari kan Yahudawa

    Firimiya sanye da baƙar kwat yana nuni da yatsa a lokacin zaman makoki

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firimiyan jihar New South Wales, ya yi alkawarin kara samar da sauye sauye bayan da gwamnatinsa ta amince da wasu sabbin dokoki kan mallakar bindiga.

    Firimiyan jihar New South Wales, ya yi alkawarin kara samar da sauye sauye bayan da gwamnatinsa ta amince da wasu sabbin dokoki kan mallakar bindiga.

    Chiris Minns, ya ce gwamatin ta dauki matakin ne bayan harin da aka kai wa Yahudawa a wani wurin biki a gabar tekun Bondi, inda har mutum 15 suka rasa ransu.

    Karkashin sabuwar dokar mutum zai iya mallakar bindiga har guda hudu, manoma kuma za su iya mallakar sama da bindiga goma.

    Sannan an kara wa yansanda karfin ikon hana zanga-zanga.

    Gwamnatin jihar ta ce wannan sabbin dokoki na mallakar bindiga su ne mafi tsauri da aka taba yi a Australia inda aka takaitawa mutane bindigogin za su iya mallaka.

    Tuni dai masu suka ce zasu kalubalanci matakin hana zanga zanga.

  10. Ayyuka huɗu da rundunar tsaro ta mutum 2000 za ta yi a Kano

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun assasa rundunar tsaron askarawan jihar ne na sa-kai domin taimakawa jami'an tsaron tarayya na sojoji da ƴansanda domin tabbatar da tsaron al'umma.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da sababbin dakarun askarawa 2,000 da gwamnatin jihar ta horas, tare da ba su kayan aiki da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

  11. Amurka za ta hana wasu ƴan ƙasashen Turai bisa kan sa wa Amurkawa ido a intanet

    Trump sanye da baƙar kwat yana nuni da yatsa alamun gargaɗi.

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce za ta hana visa ga wasu 'yan kasashen Turai biyar, inda take zargin su da jagotantar wani aiki na sa ido ga ayyukan wasu Amurkawa a intanet.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya bayyana ayyukan mutanen a matsayin wani mummunan aiki na sanya ido.

    Mutane sun hada da wani kwamishina na hukumar tarayyar Turai, Thierry Breton, wanda ya taimaka wajen tsara sharudan kafofin sada zumunta.

    An yi amfani sabbin sharudan a farkon watannan inda har aka ci tarar kamfanin X na Elon Musk.

  12. Ƴansanda biyu sun samu rauni bayan harin bam a mota a Rasha

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukuntan Rasha sun ce 'yan sanda biyu sun samu rauni bayan rahotanni fashewar abubuwan da aka samu a kudancin Moscow.

    Wata sanarwa da mahukuntan suka fitar kan fashewar abubuwan sun ce an fara bincike akan lamarin.

    Wasu kafafan yada labaran ƙasar sun ce bam ne ya tashi a cikin wata mota lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani babban janar din Rashan a ranar Litinin din da ta wuce.

    Hakan ya sa Rasha ta ƙara tsananta hare-harenta a yankin Odesa da ke kudancin Ukraine, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a wasu sassa tare da barazana ga muhimman ababen more rayuwa na harkar jiragen ruwa.

    Mataimakin Firaministan Ukraine, Oleksiy Kuleba, ya ce Moscow na kai hare-haren ne “cikin tsari,” yana mai gargaɗin cewa a makon da ya gabata cewa hankalin yaƙin “na iya karkata zuwa Odesa.”

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce hare-haren da ake kaiwa akai-akai na nufin toshe damar Ukraine ta amfani da hanyoyin safarar kayayyaki ta teku.

    A farkon watan Disamba, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar katse wa Ukraine hanyarta ta zuwa teku a matsayin martani ga hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da aka kai wa tankokin man Rasha a Tekun baharul aswad.

    A daren Litinin ne hare-hare suka auku kan kayayyakin tashar jiragen ruwa a Odesa, inda suka lalata wani jirgin farar hula, kamar yadda gwamnan yankin ya bayyana.

  13. INEC ta yi watsi da Tanimu Turaki a matsayin shugaban PDP

    ..

    Asalin hoton, PDP/X

    Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta ce ba za ta amince da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam'iyyar PDP ba inda ta ce ta yi hakan ne bisa amfani da shari'o'i da ke kotu.

    Wannan dai na ɗauke ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 22 ga watan Disamba da sakataren hukumar, Dakta Rose Oriaran-Anthony ya sakawa hannu wadda jaridar Punch ta samu.

    INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan wasiƙu da ta samu daga lauyoyin jam'iyyar PDP cewa ta gyaran bayanan jam'iyyar da ke rumbun bayananta dangane da sunayen shugagannin jam'iyyun na ƙasa da aka zaɓa a babban taron jam'iyyar a jihar Oyo a watan Nuwamban da ya gabata.

    To sai dai hukumar ta Inec ta ce ta yi duba da nazari kan buƙatun lauyoyin bisa dogaro da "abin da yake na gaskiya, da dokoki da kuma hukunce-hukuncen kotuna dangane da batun", da suka hana hukumar sa ido ko kuma amince wa da sakamakon abin da ya fito daga taron na ranar 15 ga watan Nuwamban 2025.

  14. Nicholas Maduro na Venezuela ya ce ya samu goyon bayan kwamitin tsaro na MDD

    Nicholas Maduro yana jawabi sanye da jar hula hana sallah sannan ya dunƙule hannayensa guda biyu da ke nuna alamun ƙarfin gwiwa.

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya ce gwamnatinsa ta samu goyon baya daga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya akan rikicin da suke da Amurka.

    Mr Maduro, ya bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa da kwamitin ya kira domin tattaunawa akan tankokin man Venezuela da Amurka ta kwace.

    Mr Maduro ke nan ke cewa idan kuka kalli wannan fashin teku, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta yi alawadai da shi inda har muka samu goyon baya daga kwamitin.

    Rasha da China sun zargi Amurka aikata cin zali da kuma rura wutar rikicin.

    Amurka dai na zargin Mr Maduro da jagorantar kungiyoyin mutanen da ke safarar kwayoyi.

  15. Jami'an rundunar NSCDC sun yi ɓatan dabo bayan harin ƴan bindiga a Neja

    ..

    Asalin hoton, NSCDC

    Wasu jami'an rundunar tsaro ta NSCDC sun ɓata bayan wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai wa wani ofishin jami'an rundunar a ƙauyen Ibrahim Leleh da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan bindigar masu yawa da suka shiga ƙauyen sun buɗe wuta kan duk wnai jami'n tsaron da suka yi arab da shi da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Talata, al'amarin da ya tilasta wa jami'an NSCDC sun shiga daji domin tsira da rai.

    Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ƴan bindigar sun ƙwace ƙauyen bayan ƙwace makaman jami'an rundunar.

    Kakakin rundunar ta NSCDC a jihar Naija, Abubakar Rabi'u ya tabbatar wa da jaridar afkuwar al'amarin

  16. Trump yana cikin zulumi bayan zargin amfani da jirgin Epstein

    Trump sanye da baƙar kwat da jan lakatayi yana jawabi

    Asalin hoton, Getty Images

    An sake kira ga gwamnatin shugaba Trump akan ta hanzarta sakin tsoffin bayanai da ke da alaka da mutumin nan da aka samu da laifukan lalata da kananan yara, Jeffrey Epstein.

    Bayanan da aka wallafa na sakonnin email a baya-bayan nan sun yi zargin cewa Donald Trump ya yi tafiye-tafiye a jirgin Epstein.

    Wani ɗan jam'iyyar Democrats ya ce bayanan sun bayar da mamaki sosai saboda sun sa shugaban duk bai ji dadin abin da ya faru ba.

    Mr Trump dai ya sha musanta aikata ba daidai ba a game da badakalar Epstein. Sashen shari'a na ƙasar ya ce zai ci gaba da samar da bayanan da ake buƙata a game da batun Epstein.

  17. Mata a Iran na neman a saki wata ƴar fafutuka da aka yanke wa hukuncin kisa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hoton wasu mata da ke nuna shauƙi da ƙauna ga jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokacin bikin sabuwar shekarar 1404 ta ƙasar.

    Ɗaruruwan fitattun mata, ciki har da tsofaffin shugabannin ƙasa da firaiministoci da waɗanda suka samu kyautar Nobel ta zaman lafiya, sun fitar da takardar koke ga gwamnati ta saki wata mai fafutuka, a yayin da ake fargabar za a iya zartar da hukuncin kisa a kanta.

    Wasikar ta ce a watan Oktoba aka yanke wa Zahra Tabari mai shekara 67 hukuncin kisa, karkashin abin da suka kira wani 'zaman kotu na je-ka-na-yi-ka da aka yi cikin minti goma'.

    Zuwa yanzu ba a tabbatar da hakan ba a hukumance.

    Sun ce ana zargin Ms Tabari da laifin riƙe wata takarda da ke kira da karfafawa farar hula gwiwa su nuna turjiya kan matsin da mata ke fuskanta a Kasar Iran.

    Ana kuma zargin ta da zama ƴar kungiyar PMOI da gwamnati ta haramta a ƙasar.

    Ƙasar Iran dai da ke bin turbar shari'ar Musulunci na fuskantar ƙalubale daga wasu tsirarun ƴan ƙasar masu kodai rajin sauyi ko kuma alaƙa da ƙasashen yamma da ke adawa da Iran.

    Masu fashin baƙi na ganin cewa Iran tana da ƙwarewa wajen daƙile barazanar da ta ninka irin wannan.

    An ga yadda ƙasar ta Jamhuriyar Musulunci ta daƙile zangza-zangar zaɓuka da ta hamayya da lulluɓi da na tsadar rayuwa da dai sauran su.

  18. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Laraba wadda Hausawa ke yi wa kirari da Tabawa ranar samu.

    Muna fatan Allah ya sa ranar ta amsa sunanta na ranar samu ga dukkannin mai rai.

    Yau ma mun dawo kamar kullum da labarai da rahotanni da sharhi kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance da wannan shafi na kai tsaye na sashen Hausa na BBC. Ka da ku manta za ku iya leƙawa sauran shafukan namu na sada zumunta domin samun ƙarin labarai da rahotanni da ma hirarraki.

    Mun gode.